Web Analytics Made Easy - Statcounter

Allah ne sheda book 1 complete hausa novel

Allah ne sheda book 1 complete hausa novel.

Ayyah taslima kinga ajiye aikin nan kije xan karasa girkin nan kinji kinga kinyi latti xuwa school, to anty dakin bari na karasa miki kawai na kusafa.
a’a kije driver yashirya ke yake jira ki fito kawai, jeki kanwata Zan karasa; ki maida hankali ayi karatu saikin dawo.
to antyna nagode saina dawo’to kanwata.
dasauri tashirya cikin school uniform dinta ta dauki baskect dinta ta fice, harga Allah tana kaunar anty tauhida saboda yadda take sonta kai kace’ wata kanwarta ce alhalin kuwa babu dangin uwa bare na uba, hasalima taslima yar aikinta ce’zakuyi mamaki idan nace’muku yar aikinta ce, takewa wannan gatan harta sakata makaranta domin a lokacin da aka dauko Mata taslima a matsayin yar aiki dama tun a kauyensu ita tana karatu hakan yasa tauhida(anty) ta mayarda ita ta kuma jawota a jiki kamar wata kanwarta wacce suka fito gida daya, komai yimata takeyi, shi yasa suka shaku matuka.
around 1:30pm tashigo gidan ta kwalla Kira “antyna! antyna!!
shirun dataji yasa ta nufi bedroom din tauhida a kwance take’ tana xubarda kwallar data Saba,
shiru tayi’a lokacin data sameta a wannan yanayin zama tayi a gefenta tareda dafa kafadarta tace ‘antyna’.
dasauri tauhida ta dago tana share kwalla tace’taslima yaushe kika dawo,banji dawo war ki bane.

Allah ne sheda book 1 complete hausa novel

anty dama bazakiji dawowa ta nasani tunda kina nan kina abunda kika Saba,ban San har zuwa yaushe ne zaki daina tunani da kukan nan ba,Allah yasani bana son ganinki cikin wannan yanayin ko kadan domin hankalina yana matukar tashi,
Allah sarki kanwata kiyi hakuri, kinfi kowa sanin Abunda yake damuna banida burin daya wuce naganni da dana! ko diyata a duniya sai dai kuma Allah bai bani ba, shekata6 kenan da aure taslima Dana samu cikin saiya zube baya zama munyi maganin asibitin munyi na Islamic din but kin daiga shiru taslima Ina tsoron Karna mutu banga,iri na ba a duniya nasan idan na mutu taslima kowa zai manta dani ne, a duniya tunda kinsan banida iyaye na,mamana da babana duk sun rasu dama ni kadai suka Haifa a duniya sai kuma suka rasu,hakan yasa na tashi a hannun wan mahaifina wato baban tauhed mijina Wanda shida matarsa suka rike ni tamkar yarsu yaransu kuwa babu wani banbanci a tsakanin mu,tin Ina karamata tauhed yake hidima dani,harna girma inda hakan yazama soyayya aka hadamu aure nida shi, so da kauna da kula babu Wanda bana samu a gurin tauhid daga baya yanayin aikinsa ne yasa baya xama a gida kinsan cewar soja ne,kuma babba Ana tura shi kasashe yayo watanni inda yake Nuna min damuwar sa akan barina dayake yi ni kuwa na nuna masa babu matsala na kuma Kara masa kwarin gwiwa akan aikin nasa,shi yasa yake alfahari dani,

rashin haihuwata ni yafi tayarma da hankali domin shi yake rarrashina, akan hakan Ina son haihuwa matuka a haka muka cigaba da addu’a akoda yaushe muna Neman zabin ubangiji a family ma duk su suke kwantar Minda hankali, haka nacigaba da rayuwa idan yayi tafiya sai kannensa suxo su tayani xama domin su ukku iyayensu suka Haifa shine babba tauhed sai saudat da muhsina, yanayin karatun su yasa na nemi a samo min yar aiki shine aka kawo min ke,naji dadin zama dake saboda kirkin ki tarbiyar ki,nutsuwa kamala da sauran su,shi yasa nake jinki kamar jinina kuma kece kika zamo mai share min hawaye a duk lokacin da suka xubo, kece madadin tauhed…….

hausanovels.org

💕💞💕💞💕💞💕💞💕ðŸ

Allah ne sheda book 1 complete hausa novel

wannan shafin kune members of Sirrinki Alkhairin ki group and Matan aure group godiya da sadaukarwa a gareku.

Allah ne sheda! by xee’abu safana

Allah ne sheda book 1 complete hausa novel

hakane anty dukda haka kisa hakuri a ranki kinji komai lokaci ne, kuma haihuwa nufin Allah ne kiyi hakuri kinji antyna!
to taslima nagode kinji Allah yai miki Albarka kije watsa ruwa kiyi sallah saiki zo muci abinci,
yawwa antyna ta uncle dina ko kefa harnaji dadi’murmushi kawai tai batace komai ba,
kwance take tana waya da tauhed yace’namesake (domin haka suke kiran junansu tace’ Na”am namesake Dina,

kinga wallahi nayi kewar ki Ina so inzo inganki gaskiya ni,
dariya tayi domin cikin shaqwaba yayi maganar tace’ soja mazan aiki karka tada hankalin ka Ina lapiya kuma Ina kular maka da kaina sosai da sosai, bana so kadamu kanka harkaje ka fara ramewa,
smilen yayi tareda shafa lallausan sajen sa yace’Allah sarki iyalina Allah yabrmu tare’amin mijina nakaina,

a haka suka cigaba da wayarsu taslima dake zaune, bayan tauhida ta kashe wayar tayi’dariya tare da fadin Kai Ana shan love a gurin nan anty wallahi kina son uncle dayawa shima kuma yana sonki, kuna burge ni wallahi,

Allah ko kanwata to kema zancigaba da miki addu’a Allah yabaki miji nagari kamar ki domin mata tagari ita tafi dacewa da miji nagari, shi isanya nakewa uncle dinki addu’a ko bayan ba raina Allah yabashi Mata tagari wacce zata kula dashi fiyeda ni,
haba anty ai dake zai kare rayuwar sa, insha Allah.

ohni! wai kuna bani mamaki kunsan fa rayuwar nan batada tabbas ba madawwa miya bace’ tadan wani lokaci ne,
dukda haka dai anty’to shikenan ina fatan kinshirya kayanki Dan kinsan gobe ne,kikace zakije kauye gurin umma, haba anty aikin san yadda nake dokin ganin ummana yau ai bazanyi baccin kirki ba, kinsani ummana Allah sarki,
au wato taki ce ke kadai ma ko?

au sorry ummanmu!
washe gari tunda safe taslima da driver suka dauki hanyar kauyen nasu da akwai nisa hakan yasa sai karfe3 na yamma suka shiga kauyen sukayi parking a kofar gida da gudu tashiga gidan tana kwalawa ummar ta tah Kira,
ummar datake duke tana hada itace a murhu tace’ wah nakeji kamar taslima, kafinta karasa taji an rungemeta dukkan su farin ciki suke kara ra, a fuskokin su,

daki suka nufa driver kuwa shigowa yayi da kayan bayan sungaisa da umma yasha ruwa yace’xai wuce.

Inna kuwa tanajin xuwan taslima ta dauko tabarma ta shinfida a tsakar gida tanata habaici da maganganu anje karuwanci andawo shine za’a shige daka a bawa uwa Dan abunda aka samo Ana karyar aiki akaje to aidai maji magani,
tundaga umma har task in a babu Wanda ya kulata, taslima ta fito da 20k dinda anty tauhida ta bada akawo wa umman da kuma tsaraba da kayan abinci da sutura, sosai umma ke godiya tana sawa tauhida albarka sannan takara yiwa taslima nasiha ta rike mutuncin ta tabama marar da kunya,

satin ta daya amma jitayi kamar tana kurkuku saboda axabar bakaken maganganu da mugun fata irin nasu baba da inna Dan haka 1week tayi tadawo kano,tacigaba da karatun ta DA kuma aikinta,,,,,,

hausanovels.org

💞💕💞💕💞💕💞
Allah ne shaida!

Allah ne sheda book 1 complete hausa novel

xee’abu safana mrs’Bamalli

this is your page safiyya lamba Ina godiya da nuna kulawa da kaunar littatafai na jinjina yar mutanen sakwatawa,

¶¶¶¶¶

cikin kula tauhida ta dubeta tace’taslima alfarma naxo nema a gurinki?

alfarma kuma ni anty,ai babu abunda zaki nema a gurina ki rasa shi, meh kike so anty!

aikine mai wahalar gaske taslima, aikine kuma na sirri sonake yazama sirri tsakanin na dake,sai Wanda xaiyi aikin?

anty meh kike so ne haka?

kuka tasaki ta rike hannun taslima tace’ kanwata yanxu haka Ina dauke da wani cikin a karo na6 kenan doctor ya tabbatar minda cewar cikin nan shima zubewa zaiyi kamar sauran saboda inada matsala kuguna(marata) bazata iya daukar Dan mutum ba mafita daya ce!
mene ne mafitar aunty?

dole saidai acire kwayoyin halitta na asaka a cikin wata indai anaso su rayu! taslima ki taimake ni, Ina rokon ki, ki amince a cire kwayoyin halitta na asama ki kirainar min su,ki haifarmin ki bani, taslima kinsan burina bai wuce Inga jini na ba, kuma inaji a jikina bawani dadewa zanyi a duniya ba,

Allah ne sheda book 1 complete hausa novel

jin maganar antyn tayi kamar saukar aradu ina bazai yiwuba, inzama bazawarar karfi da yaji alhalin bantaba yin aure ba,kuma idan mutane suka ganni da Cikin meh zance musu, mezan cewa ummana? baba da Inna suyi mana dariya a kunyata ni a idon duniya domin duk Wanda zancewa ba cikina, bane bazai yarda ba,ko a gaban ummana naje banida wata sheda,duk Wanda xancewa banyi zina ba kuma banyi aure ba,bazai yadda ba tunda dai ciki ba’a shansa a ruwa ko a shaka a iska kowa cewa zaiyi waye shaidata, to ni kuma ai nasan ALLAH NE SHAIDA sai kuma ita antyn, gaskiya bazan yarda ba,wannan ai ganganci ne da rayuwa da kuma farin cikina, take so inyi, tawani bangaren kuwa Ina tausayawa Mata matuka Ina kuma tuna alkairinta a gareni sosai,,,,
taslima kinyi shiru’ kallonta nayi nace’AUNTYYYYYY!!!!
Murmushi Antyn tayi tace’taslima? Fadamin abunda ke ranki,
A kasalance tace”anty na amince, da sauri tauhida ta rungumeta tana fadin nagode kanwata ki shirya gobe muje mucewa ummanki zamuyi tafiya zamu Dade, sannan kuma namiki alkawarin babu Wanda zaisan maganar nan dagani sai ke sai ALLAH to anty! Ta fadi ita dai kam duk jikinta a maceh yake tana tsoron al’amarin,

Allah ne sheda book 1 complete hausa novel

Washe gari suka shirya suka dauki hanyar kauyensu ita kam duk batada walwala domin abun yana bata tsoro,a haka sukaje Umma taji dadin ganin su barinma dataga harda tauhida,
Tauhida da kanta tayiwa ummar bayani fatan alkairi tai musu suka kwana daya suka dawo gida, ranar da za’ayi aikin sosai tauhida ta kwantarwa taslima da hankali inda taji tadan samu relief, a ranar doctor yai musu aikin, aka cire kwayoyin halittar daga jikin tauhida aka sakawa taslima, 1week sukai a hospital sika dawo gida a lokacin kuma su taslima suka fara zana jarabawar waec,
Ita kanta tana mamakin yadda Antyn ta tah take kulada ita Dan yanxu ko ruwan wanka ita take hada mata, Dan haka ta fara sakin jiki da al’amarin dukda sabon yanayi datake taji a jikinta, a haka ciki ya fara mikawa kuma sungama exam da haka tacigaba da zama domin yanxu boyeta anty takeyi a kullum tana fadin taslima’ ki saki jikin ki, kinji babu Wanda zaisan wannan sirrin dagani saike sai Allah ko mijina bazai saniba har sai zuwa bayan kin haihu zan sanar masa gaskiya kinji,

To but anty inda Allah yasa ni kuma nasamu miji nayi aure yagane baisame ni a budurwa bafa mezance masa,anty kinsan duk macen data haihu to sai tazama disvargin.
Hakane amma ke aina xaba miki miji kicire wannan shima a ranki kinji nayi miki miji nagari, yanxu ki kwanta ki huta bari inshiga kitchen mezan girka miki?
Ummmmm! Dan daga Kai tayi Rana’ nazari tace’ tuwon dawa miyar kuka tsanwa shar kar’asamata manja! Kuma bana son asaka tarugu ko kayan miya, so nake asaka sansamin yaji a miyar,
Dariya anty tayi’ tace to angama,

Allah ne sheda book 1 complete hausa novel

Kullum abunda take so take ci a gidannan Dan haka batada matsala saita tunanin haihuwa!
A haka har cikinta yakai wata 6 ciki fa yafara tsufa domin yafito sosai, har gida doctor yake zuwa yana dubata, ya kuma tabbatar musu yan’biyu ne namiji da mace’ Allah sarki anty harda kukan dadi tayi yanxu a duniya babu abunda tafi so kamar cikin nan, Dan haka kullum cikin addu’ar Allah yasauki taslima lapiya take,

Around 10pm na dare kwance take tana wayada tauhid tace’namesake kasan mene ne?
Gyara kwanciyar sa yayi tareda shafa sajensa yace’ a.a namecy saikin fadi,

Namesake Allah inada ciki,

Zabura yayi yace’sure, habibaty are you serious?
Am serious inada ciki harna tsawon wata shida6,
What you said 6month?
Yes 6months amma fa baya jikina wllh,
Shiru yayi yana nazarin maganar ta tah banda yasanta lapiyarta lau, da ace wani ne yai maganar da yace’ lallai bayada hankali,shi baigane wannan bahaguwar maganar ba wai tanada ciki na6 months amma a jikin wani kajifa wani sabon salon hauka kuma,

Allah ne sheda book 1 complete hausa novel

Shirun dataji yayi yasa’tace wallahi mijina da gaske nake kashirya ka kusa zama uba,
Jiyayi ta Kara rikita masa kwakwalwa yace’ ke tauhida karfa kibari son haihuwa ya haukata ki yakike min wani zance haka,
Dariya tayi tace’shikenan saika dawo zanmaka bayani duk yadda lamarin yake, kuma kashirya idan kadawo zanmaka aure Allah kuwa,
Oh! Shoooooooot! Ya fada yana dafe kansa yace’karki rikita min kwalwa da shirmen ki na yau kinji ki kwanta saida safe ki kulada kanki i love you ya fadi tareda manno Mata wani dogon kiss ya kashe wayarsa.
Dariya abun yabata ta tashi tashige bathroom ta dauro alwala ta tada nafila.

Allah ne sheda book 1 complete hausa novel

Shafin kune wannan @GOLDEN’S WRITES ASDOCIATION@ godiya mai tarin yawa Allah yakara hada kanmu,

Shi kuwa tauhid yana kashe wayar tsoki yayi tareda fadin xai nemi Dama a gurin aikin subarshi yaje’ Nigeria yakai tauhida a duba masa kwakwalwarta da haka yayi baccin sa,

Tauhida kuwa bayan tayi nafila alqur’ani tadauko tacigaba da karantawa kallon agogo tayi taga har daya da rabi na dare tati 1:30am Dan haka ta rufe tareda yin dogayen addu’o’i taje gefen taslima dake kan gado kwance Dan yanxu daki daya suke kwana, shafa cikin tayi taji sai motsi yake murmushi tati’ tareda mannawa cikin kiss ta kwanta bacci yadauketa,

Kiran sallar asubh ne yatayar da taslima bayan tayi sallah harta gama ta juya taga yadda tabar tauhida a haka tasameta murmushi tayi’ tace’ waih! Yau wacce Rana antyna da lattin sallah, aikuwa Bari inmiki wayau yauni Zan hada mana breakfast Dan haka, ta nufi kitchen around 8am ta gama ta nufo dakin again thanks a bata tashiba, Dan haka ta nufota tana antyna! Antyna!! Kitashi kiyi sallah, shirun dataji yasa ta tabata tace’anty!anty!! Jitayi babu alamar numfashi a rikice ta daga hannunta tasaki taga yafadi yaraf! Kallonta tayi taga idanunta ya kalli sama kuma farine kawai da wata Kara tasaki da guru ta nufi waje a garden inda maigadi da driver suke sai ganinta sukai da gudu ga katon ciki, da mamaki suke kallonta ciki kuma, karasawo tai tana fadin kutaimake ni antyna!!!
Tanata nuna cikin gidan binta sukai har dakin baba maigadi ne yaduba tareda dogon salallami yace’ hajiya ta rasu!
Wani ihu taslima tasaki tareda sulalewa kasa a someh! Wannan yayi dai’dai da shigowar doctor dake dubata,

Allah ne sheda book 1 complete hausa novel

Sai wajen sha biyu ta farfado inda taganta a gidansu tauhida wato gidan iyayen tauhid, juyawa tayi gefenta taga gawar tauhida tasauri ta nufi gurin aka janyeta, tanaji tana gani aka fita da gawar tauhida domin kaita masaukinta na gaskiya wani kuka tasaki tana fadin anty karki tafi kibarni anty zaki barni cikin matsalar rayuwa kece shaidata sannan kuma *ALLAH NE SHAIDA* kidawo anty!!!
A haka aka mayarda taslima wani daki daban, tacigaba da surutun ta, tana kuka haka ta wuni a dakin har dare, salloli kawai takeyi ko abinci bataci yadda taga dare haka taga safe a haka tai rayuwa harta 3days akayi addu’an sadakan3 ummi ce(mahaifiyar su tauhid)’ ta shigo fuskar nan a murtuke ke! ta fada cikin tsawa!
A firgice taslima ta juyo ta dubeta jikinta na rawa, dubanta tayi ‘tace” ke kuma a gidan ubanwa kika samo wannan katon cikin?
Hawaye suka zubo mata tace’wallahi hajiya na rantse da Allah ba cikina bane, cikin anty tauhida ne wallahi *Allah ne shaida* itama kuma shaida ce, bantaba zinaba wallahi tallahi cikinta ne,

Wani wawan mari ta tsinka mata Wanda yasaka taslima ganin wasu stars na yawo, kunji wani sabon sanfarin sarrafa iskanci kuma Dan ubanki ni zakiyiwa zancen mahaukata a to ko mahaukaci wannan maganganun bazasuyi tasiri a xuciyarsa ba bare ni, koda yake ba hurumina bane bama yimiki wannan tambayar mazah’mazah ki hada kayan ki nanda 1hr kibarmin gida dama ai kwadayi ne yake kawoku burnin aiki inbanda haka, da kuma karuwanci ai duk laifin tauhida ne ta wani jawoki a jiki, ta dauke kamar wata kanwarta to Dan haka maza ki bar gidannan kin tsureni da idanu kamar mayyah, munafuka!
Fuuuu!!! Ta fita dakin nikuwa tsoro ya kamani Dan haka da sauri na fito Ina waiwaye harna fita gidan sautin kukana harya daina fita sai hawaye dake bin fuskata, napep na tsayar na fada masa inda zai kaini, kai tsaye gidan antyna na nufa na iske maigadi shine ya bude min nashiga kayana na tattara tsaf! Da kudin albashina wanda dama bana siyan komai tarawa nakeyi hotunan da mukai da antyna nadauko da wanda ita kadai tayi na fito nacewa” mai napep din kaini tasha inda xanhau motar jigawa! To yace’dan haka suka nufi tasha inda tahau motar jigawa tana ta tunanin halinda ummanta zata shiga idan taganta da wannan ciki! Tafiya sukai doguwa kafin isarsu jigawa motar kauyen su wato”roni” tahau tun a motar ta fara kuka gabda magruba ta isa kauyen duk wanda ta hadu dashi saiya bita da ido.

Jiki a mace tashiga gida da sallama” inna ce a bakin rijiya tana jan ruwa, kallon taslima tai a banzace’ sai a lokacin takalli cikin dake jikinta wurgi tayi da gugar, tayi wata shewa sannan ta cigaba da rangada guda ba kakkaftawa kankace meh mutane sun fara lekowa domin a tunanin su haihuwa ce akayi tunda al’adar garince insun haihu, wasu harta Katanga lekowa suke suga menene?
Ahayyeh! Nanayeh! ai mudai munsan rana dubu ta barawo rana daya take! tamai kaya ai cewa ake sharri mukeyi antafi aiki birni, mukau munsan yawon dandi aka tafi a birni to aifa ga aikatau nan andawo dashi, ai lallai ankuwa yo aiki wallahi babban aiki makuwa jama’ar gari kuzo kugani.

Umma dake daki tajiyo kwakwaxon inna hakan yasata fito taga meke faruwa, ai wani jiri taji na niyar dibarta domin abunda tagani gani takeyi kamar a mafarki, taslima ce da wani katon ciki innalillahi wa’inna ilaihi raji’un abunda tadinga mai-maitawa kenan cikin tashin hankali!

Baba dake bayi yayi saurin fitowa shima ido yabita dashi,
Inna tacigaba da cewa malan gashinan kana gani ankawo mama cikin shege a gidan nan nikam wallahi bazan zauna da dan zina a gida daya ba, dole inbar musu gidan,
Dasauri yace” kije ina ai sune dabarin gida bake ba, dama meh suke mana a gidan nan ai kece mata ta’ ita kuma wannan ya nuna umma(kinsan matar kanena ce shi kuma yabi duniya yabarta da lalata tar yarsu kuma kinga abunda ta kwaso Dan haka dole ne suma su shiga duniya Dan haka tabbas nabaku kankanen lokaci kafin inje masallaci indawo ku tabbatar kunbar gidan nan)

Daki ummana tashige saboda tashin hankali kukan ma takasa saina zuci datake yi,hada kayanta tashiga yi ni kuwa Ina gefe inata rusa kuka, ko kallon inda nake batayi ba,
Tabbas da baba(mijin Inna) da mahaifina ubansu daya kowa da uwarsa iyayensu duk sun rasu hakan yasa suke zaune gidan gadon su, baba da Inna sun tsani mahaifina da ummata basa kaunarsu ko kadan har aka haifeni nima abun yashafe ni, su kuwa basu taba, haihuwa ba, rana daya aka nemi mahaifina aka rasa, ummana tashiga tashin hankali matuka tun Ina karama, tun tana saka ran ganin shi harta fidda fiyeda shekara goma kenan anso tai aure takiya tace”zata cigaba da jiran mijinta har abada tunda tasan yana sonta kuma bai saketa ba, ita ta raine ni ci da sha sutura ta kuma sakani makarantar boko da arabi, dana fara girmane baba yaso ya aurar dani taki yarda shinefa suka bawa wata mata ni ta kaini aiki birni su kuma a basu kudin, ummana tayi bakin ciki da kuka sosai daga baya tacigaba damin addu’a da nasiha,
To shinefa Allah yasa aka kaini gidan anty tauhida wacce tamin gata,ta kuma mayarda ni school harna gama har xuwa yanxu da abunnan yafaru)!

Allah ne sheda book 1 complete hausa novel

Tsaf! Umma ta hada kayanta tayo waje na biyota baya, har muka fita gidan ai fitar mu keda wuya mutanen gari suka fara yimana ruwan duwatsu anata jifar mu, yara na ihu suna tayi cikin shege!
Ai tuni muka Kara sauri sukuwa suna binmu har bakin gari wani uban dutsi da aka jefo ai sai ga idanuwa na wani dum! Naji dif! Naga duhu ya ziyarci idanuwa na wani zugi da radadi nakeji har tsakar kaina da karfi nace” wayyo Allahna Umma! Umma kina Ina umma bana gani!
Allah sarki dah da mahaifi sai Allah cikin takaici ta juyo umman tana kallonta,Wanda yayi dai’dai da lokacin da akayowa ummar jefa a kunne! Wani dum! Taji kunnuwan nata’ tana kallon bakin taslima na magana amma batajin meh take cewa!
Ita kuwa kuka tasake Saki tace” wayyo Allahna ummana na makance umma idona a bude yake umma amma bana ganin ki umma duhu nake gani umma!!!!!!!!! Bana gani kitai makeni,
Matsowa tayi umman domin harga Allah batajin abunda taslimar ke fadi”kama hannunta tayi’tareda fadin taslima” Ina ganin bakin ki na magana amma kwata! Kwata banajin meh kike fadi banajin komai a kunnuwa na, sun jefe ni a kunne idan kina jina kizo mutafi karsu sake yimana lahani!!!

Innalillahi wa’inna ilaihi raji’un ummana bakyaji na sai dai kina iya magana nashiga ukku sun kashe miki kunne kenan sun mayarda ke kurma, ni kuma sun kashemin ido sun mayarda ni makauniya wayyo Allahna!
Shirun dataji umma tayi yakara tabbatar mata da batajin ta,Wayyo Allahna nashiga ukkuna, ya *Allah Kai ne sheda* ……………..

Allah ne sheda book 1 complete hausa novel

still am in love with you my fans thank you, follow me!!!!!ΠΠΠΠΠΠΠÎ

Sai munhadu a book2 wato *ALLAH NE SHEDA 2* nagode masoya kucigaba da kasance Dani akoda yaushe taku har kullum”
ZAINAB ABUBAKAR SAFANA
xee’abu
Mrs’salihu Bamalli kaduna my luvly ustax.

GOLDEN’S WRITERS ASSOCIATION

Thank you for your shown love to me we are together fans.

Back to top button

You Want Latest Updates?

X