Kalaman bada hakuri a soyayya
Kalaman bada hakuri a soyayya:
Duk da cewa rayuwar masoya tana kasancewa abar koyi a koda yaushe musamman ma a bangaren zaman lafiya, da kulawa da juna, da kyautatawa juna da kuma kaunar juna. Amma duk da haka wata rana ana iya sabawa kamar yadda aka ce tsakanin harshe da hakori ma ana sabawa. A nan kuma mun kawo muku yadda ake furta kalaman bada hakuri a soyayya idan sabani ya samu.
Waye ya kamata ya bada hakuri a soyayya?
A yayin da sabani ya shiga tsakanin masoya, akwai bukatar bada hakuri domin kawo karshen fushi da juna, wanda kuma hakan na da sigar da ya kamata a yi amfani da ita wajen furtawa. Amma kuma waye ya kamata ya bayar da hakurin ne a yayin da bukatar hakan ta taso?
Idan an sabani ya shiga a Soyayya, ba cewa za a yi duka a taru a baiwa juna hakuri ba, a’a wanda aka yiwa abinda ya jawo batawar ya fi dacewa a baiwa hakuri. Misali idan ke ki ka yi masa laifi har ya yi fushi, to sai ki bashi hakuri tare da yi masa alkawarin za ki gyara kuma hakan ba za ta sake faruwa ba.
Idan kuma kai ne ka yi mata abinda ya bata mata rai har ya jawo batawar ku, sai kaima ka bata hakuri tare da yi mata alkawarin hakan ba zata sake faruwa ba.
Amma abu mafi kyau idan mutum ya yi wani abu da ya jawo batawa tsakanin sa da abokin soyayyar sa, to idan ya bayar da hakurin komai ya wuce yana da kyau ya kiyaye maimaita irin wannan kuskuren a nan gaba.
Kalaman bada hakuri ga masoya
Na maza: Haba shalelena, hakika nasan abinda ya faru ko a kaina ne dole raina ya ɓaci har na nuna fushi na a fili, amma kuma tunda har ki ka ga nima na shiga damuwa a bisa hakan ai kinsan ba da niyya na yi miki hakan ba. Amma dai ina neman afuwar ki tare da yimiki alkawarin hakan ba za ta sake faruwa ba.
Masoyiya ta ki sani cewa babban burina shi ne na ganki a cikin farin ciki, saboda kinsan bazan yi abinda zai bata miki rai daganan ba. Pls my love ki yi hakuri kinji🙏
Na mata: Horney nasan abinda ya faru dole ranka ya baci, amma wlh ni kaina ba da niyyar bata maka rai na yi ba. Amma dan Allah ka yi hakuri hakan ba zata sake faruwa ba, nasan kana da hakuri sosai shi yasa na yi maka alkawarin hakan ba zata sake faruwa ba, domin sam bana don bacin rai da samuwar ka Horney.
Sai ki kalleshi cikin shagwaba ki ce “Yaya har yanzu banga ka fara ba kodai so kake zuciyata ta buga ne saboda tsabar nadamar abinda na aikata bisa kuskure ne?
Insha Allahu za ki ga ya sauko sai kuma ku cigaba da hirarku ta soyayya kamar yadda aka saba.
Yawwa ai nasan idnai ta hakura yanzu ta yi murmushi, sai ka kalleta ku hada ido ka yi mata murmushi tattausa mai karya zuciya. Insha Allahu zata huce nan take.