Web Analytics Made Easy - Statcounter

Kalaman soyayya masu tsuma zuciya

Kalaman soyayya masu tsuma zuciya

Suleiman Yunusaya ce

An turomun wani rubutun da larabci me cike da hikmah da ababen lura ga masu tunani, sai nayi ƙwaɗayin fassarashi zuwa hausa dan kowa ya amfana da temakon Allah.
Rubutun de ya ƙunshi hirane da wani yaro yayi da mahaifinsa, ta yadda ya fara tambayar da cewa;—

ya ‘abi ‘iilaa ‘ayn ‘ant dhahb?

Ya Babana! Ina zaka je?

ya waladay ‘antahit rihlatay ‘iilaa huna sawf ‘asafir .

BABAN: Yarona! Na gama tafiyata daga nan, yanzu zanyi tafiya ne.

ya ‘abi ‘iilaa ‘ayn?

YARON: Zuwa ina kuma Babana?

ya waldy safri bieayd, min dar albatil ‘iilaa dar alhaqi.

BABAN: Yarona! Tafiyata (na yanzu) da nisa (domin zan tashine) daga ɓatacciyar gida (gidar ƙarya) zuwa gidar gaskiya.

ya ‘abi hal sayatul hdha alsfr?

YARON: Shin zaka daɗene a tafiyar naka Babana?

ya waladay nem sayatual ‘iilaa ‘ana yaritha allah al’ard waman ealayha.

Kalaman soyayya masu tsuma zuciya

BABAN: Yarona! Lallai tafiyar zata dauki tsawon lokaci har sai da Allah ya sa kasa da dukkan abin da ke cikin ta suka gaji..

ya ‘abaa hal maeak zad lasfark?

YARON: To shin Babana kanada guziri (n tafiya) kuwa?
ya waladay nem maei walakun safari baeid jdaan wala ‘aelam hal zadi sawf yablighuni ‘am la, fa’arsil ‘ant li alzaadd.

BABAN: Ehhh Yarona! Inada guzuri amma tafiyar nawa da nisa bansanko guzurin ze kaini ba kokuma baze kaini ba 😢 (amma to bayan na tafi) kai (yarona) ka turomun (ƙarin) guzuri.

kayf ‘ursilah lak wa’ant ealaa sufran?

YARON: Ya za’ayi na turomaka da guzuri bayan kayi tafiya? (Ai baze yuwu ba tunda baka kusa kuma babu ɗan aike).

ya waladay alduea’a, ‘adeu li allah ‘an yaghfir li wayarhamni wyef eaniyan, fahdhana zadian, ‘iina qataeat alduea’ li fasawf yanqatie zadi.

BABAN: Yarona! abun nufi a nan shi ne, ka kasance mai yimin addu’a kana mai rokamin Ubangiji ya jikaina ya kuma rahamsheni. Wannan shi ne iya abinda da zaka ci gaba da aika min har zuwa ranar da za ka gaji ka daina, to daga nan guzuri na ya kare.

hal sa’arak ya ‘abi maratan ‘ukhraa

YARON: To shin Baba zan ganka kuma wani lokacin?

nem satarani eindama tantahi rihlatuk ‘ant aydaan.

BABAN: Ehh! Zaka ganni idan kaima ka ƙare tafiyarka (ka bar duniya).

Kalaman soyayya masu tsuma zuciya

‘uwsini ya ‘abi qabl rahilik.

YARON: To Baba kamun wasiyya kafin ka tafi.

ya waladi la taghurink aldunya wazinatuha,
wa’anzur ‘iilaa min jme aldunya bi’akmaliha walam yakhudh minha ghyr alkufini, wala tushrik biallah ahdaan, wa’asmie kalam allah (alqara’an alkarima), watakalam mae allah (alsalat almaktubata), wa’awdae eind allah (alusuduqata), waeamil allah (al’akhlaq alfadilata), wakun mae allah daymaan wabdaan .

BABAN: Yarona! Kar duniya ta ruɗeka da adonta, ka duba ka gani mana, wanda ya tara duniyar fa babu abunda ita take bashi daga ƙarshe sai likafani, karka yarda ka haɗa Allah da wani wurin bauta (shirka), ka riƙa jin maganar Allah (Alƙur’ani), ka riƙa yin magana da Allah (Salloli biyar), ka riƙa yin ajiya wirin Allah (Sadaka), kayiwa Allah aiki (da ɗabi’u kyawawa maɗaukaka), ka kasance tare da Allah ako wani lokaci.
Allah Ya Gafarta Musu.

______munirat Abdussalam ta fita daga musulunci

Kalaman soyayya masu tsuma zuciya
ABABENDA NA AMFANA DASU.

1. Labarin yamun kama da wani hadisin Annabi (S.A.W) da yake cewa;-
Ka Kasance A Duniya Kamar Matafiyi.
Dan haka ya wajaba ga matafiyi ya dora daga inda ya tsaya don yada zango.
To haka muke a duniya.

2. Labarin ya tunamun da hadisin Annabi (S.A.W) da yake cewa:-
Daga lokacin da bil adama ya kwanta dama hakika abubuwansa na nan duniya sukan dakata baki daya, sai su rage wasu guda uku kacal kamar haka
A: Sadakatul jariya
B: ilimin Da ya koyar kafin ya faku
C: Barin tsatso mai kyau, ma’ana saihan yaya
Kaga ƙissar daga farko har ƙarshe hadisin yake nuna mana kokuma muce mafi yawa daga cikin shashin hadisin.

3. Ya tunamun da hadisin Annabi da yake cewa:-
Me Sallah Fa Yana Ganawa Ne Da Ubangijinsa….

4. Ya nunamun cewa lallai fa Qur’ani fa maganar Allah Ne babu makawa.

5. Ƙissar ya tunamun maganar Malluman mu da suke cewa:-
Idan Kanaso Allah Yayi Magana Dakai To Ka Karanta Qur’ani (Maganar Allah Ne Zuwa Gareka), Amma Idan So Kake Kawa Allah Magana To Kayi Alwala Kawai Ka Hau Sallah (domin me sallah ganawa yake da Ubangijinsa).
_____

Kalaman soyayya masu tsuma zuciya

Abin Tambaya:-
1. Shin kana ba yaronka damar yin hira dakai kamar haka? Kode alaƙarka dashi kullun zare ido ne da daka masa tsawa?

2. Shin kaba yaronka tarbiyya da ze iya waiwayarka ya maka addu’ah bayan mutuwa? Kode zunzurutun duniyar ka tara masa babu tarbiyya?

3. Shin ka taɓa tunanin kai matafiyine a duniya har kayi guzurin tafiya? Kode kullun budget na shekaru ashirin nan gaba da lissafin shekaru talatin kake bugawa?
___

Allah Yasa mu dace, Ya gafarta mana zunuban mu, Yasa aljannah ce makomar mu, da iyayen mu da Malluman da abokan mu da sauran musulmai baki daya.

Ameen Thumma Ameen.

Back to top button

You Want Latest Updates?

X