Web Analytics Made Easy - Statcounter

My life partner 1 complete Hausa Novel

锘縖6/9, 11:00 AM] Teemarh: _…卮乇賷賰 丨賷丕鬲賷…_*
_{MY LIFE PARTNER}_

*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
銆帮笍銆帮笍銆帮笍銆帮笍銆帮笍銆帮笍銆帮笍銆帮笍銆帮笍銆帮笍
_We are here to Educate, Motivate and Entertain our Readers_
銆帮笍銆帮笍銆帮笍銆帮笍銆帮笍銆帮笍銆帮笍銆帮笍銆帮笍銆帮笍

*BY FATIMA* _{Real~Teemarh}_

_1~2_
*Thanks to Almighty Allah for giving me the ability and chance to start the book SHARIK HAYATI {My life partner}, Special greetings to the whole members of ZAMANI WRITERS ASS. Ina maku fatan alkhairi da kuma gamawa lafiya, My Ilham, Fatima (Baby), My Zee Auwab and Luvly KK can’t luv u less sisters. Members of my groups are not excluded too, ina sanku sosai wallah 馃グ Finally my fans, Ina maku gaisuwa irinta addini aduk inda kuke, billah nima ina yinku over and over 鉂o笍*

A firgice ta mike tana kallan agogan dake manne a bangon dakin, ta zare manyan
idanuwanta waje ta ce”What!!! Past 8″. Quickly ta janye duvet din dake jikinta ta shige bathroom hankalinta a tashe, bayan 6 minutes ta fito daure da towel ta nufi gaban mirror, comb ta dauka ta fara combing gashinta, nan da nan ta gama ta dauka ribbon tayi packing smooth hair dinta waje daya, daga nan ta fara robbing body lotion shap-shap. Cikin few minutes ta gama ta nufi press dinta ta dauko doguwar riga baki ta saka kafin ta dauko veil dinsa ta yafa ta jawo side bag dinta dake jikin bag hanger sannan ta fice a dakin, daidai shoe rack ta tsaya ta dauka flat shoe sannan ta kama hanyar stairs cikin sauri ta fara saukowa. Ba kowa a falon sai TV dake kunne sai karan standing fan, hakan yasa ta wuce kitchen da gudu tana fadin “Ummi! Ummi!” Kafin ta karasa shiga kitchen din Ummi ta fito rike da warmer, kana kallanta kaga mahaifiyar yarinyar saboda tsantsar kama da suke. Ummi ta mata wani irin kallo ta ce”Are u ok? What’s the essence of running” ta ce” Ummi ina da appointment a clinic yau fa” ta karashe maganar in a hurry, Ummi ta dalla mata harara ta ce”Wa kika gayawa to?”, a hankali ta dan gyara veil dinta ta ce”I’m sorry Ummi, jiya da doctor hisham ya kirani kin riga kin rife kofa, and i didn’t woke up early today”. Ummi ta ajiye warmer din hannunta akan dinning ta ce”Kije Mustapha ya kaiki, i think i don’t have to go,”. Silently ta ce “To saina dawo” daga haka ta fice a kitchen din ta nufi kofar fita.
Babban gidane na gani na fada, yana dauke da shuke shuken flowers all over, part guda biyu ne daya na kallan daya sai kuma BQ daga gefe sannan parking lot a tsakiyan apartments din wanda ke dauke da motoci 6. Da sauri ta karasa jikin motar tana kallan Mustapha ta ce”Na makara fa Musty, kuma cewa yayi he’s leaving the country today” ta karashe maganar tana shiga back seat, Mustapha ya rife kofar ya zagayo cikin hanzari ya shiga driver seat ya kunna motar yana fadin “Yanzu zamu isa Hajiya Karama, aini inasan shiga asibitin nan kodan ina ganin turawa, ance nasu nema asibitin ko?”. Murmushi tayi me kyau ta ce”Sure, amma ai mutanenmu na nan suna aiki a caan” Mustapha ya washe baki ya ce”wa yake ta bakar fata Hajiya karama, ai turawan sunfi dadin gani, kaii Allah yayi halitta, farare kal kal dasu kamar ka bigesu jini ya fito, nifa ban ta6a ganin turawa ido da ido ba a garin kano sai a asibitin nan” ta ce”To menene abin san gani a jikin bature Mustapha, sai wani zuzutawa kake” cikin sauri ya ce”Ai wallahi Hajiya karama bature abin a ganshi ne, aini dana zauna kallan bakar mace gara a kaini gaban tsohuwar baturiya naita kallanta ina maimaitawa”, dariya sosai tayi kafin ta ce”Wato dai Mustapha bakasan ganinmu kenan, kace baturiya zaka nemo” zaro ido yayi ya ce”Na isa ince banasan ganinki, ai wallahi dana fara ganinki na zata bakyajin hausa sai larabci” dariya ta fashe dashi tana girgiza kai, duk drivers din da suke yi a gidansu tafi san Mustapha saboda idan yana mata hira yana sata nishadi, ko bata da lafiya inya shigo gaisheta sai yasan yadda yayi ya sata murmushi. Yana parking ta fito a motar tana kallansa ta ce”To zan shiga Mustapha, ga turawa nan aita kallansu, idan na fito ka fadamin wacce ka za6a” bata jira amsarsa ba ta wuce ciki saboda sauri da take.Kamar me counting steps ta shiga clinic din very gentle, office din dake gefenta by d left ta nufa ta fara knocking a hankali, ta ciki aka bata izinin shiga sannan ta bude kofar a hankali ta shiga, Doctor hisham kawai take kalla tana murmushi ta karasa ciki ta ce”Morning Dr” ya mayar mata da murmushi ya ce”Morning Fatima, how are u?” A hankali ta ce “I’m fine Dr, i though u are leaving now”. Dr hisham ya kalli wristwatch din hannunsa ya ce”I have 1 hour left, have a seat” ya karashe magana yana nuna mata kan sofa, juyawa tayi a hankali zata zauna ta ce”But Dr pls i don’t want injection this time around i need just dru… ” shiru tayi tana kallan Mutumin dake zaune kan sofa yana danna waya, saam bata kula da mutum a wajen ba, and his face look very familia, ta dan hade gira in a very low voice ta ce”Morning” ba tare daya dago ba ya ce”Same” daga haka yaci gaba da danna wayarsa, ta juyo tana kallan Dr dake rubutu ta ce”Can i have them now?” Ya ce”Yes wait a minutes, how is Abba?” Ta zauna kan hannun kujeran ta ce”He’s fine”. Very gentle mutumin gefenta ya tashi ya ya karasa wajen Dr Hisham ya mika masa hannu ya ce”Dr I’m going, thanks for all” Dr yayi murmushi ya ce”Alright friend Allah ya sauwake” zame hannunsa yayi cikin na Dr ya mayar cikin pocket dinsa ya ce”Ameen” daga haka ya nufi kofar fita a office din. Doctor Hisham ya mika mata takardar daya rubuta mata magunguna ya ce”Gashi, idan kika siya a pharmacy zasu miki explaining just like they used to” ta kar6a takardan ta ce”Thank u, and when are u coming back from cairo?” Ya ce”I’m spending just 5 days, idan akwai matsala u can meet Dr Aryan zai maki komai” ta ce “To nagode”, daga haka ta fita a office din ta wuce pharmacy.
Still mutumin nan yana tsaye a wajen, ta samu gefensa ta tsaya tana kallan fuskarsa daya hadeta ko walwala babu unlike ranar daya taimaketa. Kallan magungunan da aka masa packaging kawai take, sak irin nata wanda take sha, kenan shima irin ciwanta gareshi? Abinda ta fada cikin ranta kenan. Mika nata takardar tayi bayan an sallameshi ya bar wajen, cikin few minutes itama aka mata packaging nata ta biya kudin sannan ta bar pharmacy din cikin gaggawa saboda bataso mutumin ya mata nisa. Tana shan kwana ta ganshi a zaune ya limshe idanuwansa kamar me bacci, ta karasa a hankali ta tsaya a kansa ta ce”Assalamu alaikum” ya bude manyan idanuwansa cikin cool and sweet voice ya ce”Wa’alaikum salaam” ta danyi murmushi dan batai tinanin zai amsa ta ba, wasa ta farayi da ring din hannunta ta sunkuyar da kanta kasa sannan ta ce”Thank u once again for helping me the other time, lokacin dana farka Salma tace min ka tafi, sai yau Allah ya hadamu, thank u so much” kallanta kawai yake yana sauraronta since she started talking, ya sauke kansa kasa ya ce”Ba komai, ki dinga kula” ta ce “Insha Allah” daga haka ta juya zata tafi ya ce”Your name” ba tare data juyo ba ta ce “Fatima Rafi’ah” ya mike tsaye yana kallanta ya ce”I’m Yusuf Muhammad” sai a lokacin ta juyo ta ce”Nice to meet u, thanks much” daga haka taci gaba da tafiya tanajin ta sauke wani babban nauyi na masa godiya da tayi.Ta bayanta taji ya ce “Rafi’ah” ta tsaya caak sai kuma ta juyo tana kallansa, da alama binta yake a baya, ya karaso wajenta yana folding hannayensa ya ce”Can u pls pretend as my girlfriend?”
Zaro ido tayi tana kallansa ta ce”What!” Ya gyada mata kai looking into her eyes ya ce”Yes, pls do help” cikin sarkakkiyar murya ta bude hannayenta tana kallansa ta ce”But why?” Hannayensa duka ya saka a pocket dinsa ya ce”I will explain ltr, just go back and have a seat there”. Kallansa kawai Rafi’ah take with some expression, bayan 2 minutes ta dauke idanta a kansa, dai dai nan phone dinsa ta fara ringing, ya zaro wayar a aljihu ya dauka yana kallan Rafi’ah da kanta ke kasa ya ce”Hello Aunt… Ehh na daukota”, from the other side Aunt dinsa ta ce”Zata bimu gida kenan kaga sai mu gaisa da kyau” kansa ya dan shafa ya ce”No no, i told u she can’t follow us, just wanted her to great you and then she will live” ajiyar zuciya ta sauke kafin ta ce”Ohk to ku karaso mu gaisa” ya ce”Alright Aunt”.
Kallan Rafi’ah yayi ya sauke phone dinsa a kunnensa ya ce”Let’s go” ta dago tana kallansa sai kuma ta girgiza kai ta ce”Noo, i can’t pretend, how will i even start? Driver na jirana kuma” ya ce “Just few minu…” Kafin ya karasa magana ta juya ta fara tafiya, binta ya dingayi da kallo yana tinanin what’s the next thing to do, gashi ya fadawa Aunt dinsa sun iso asibitin. ta danyi tafiya me nisa kafin ta juyo ta kalleshi taga ya koma yana tafiya a hankali, duk sai taji bata kyauta ba, gashi ranar da ciwanta ya tashi he’s the first daya taimaka mata a wajen ba tare daya santa ba, why won’t her help him too? A hankali kuma ta ce”But i can’t pretend, ta ina ma zan fara?” shiru tayi tana tinani, bayan few minutes ta nufeshi da niyyar ta yarda zata taimake sa shima, a inda ta sameshi dazu a nan wajen ta sameshi yana zaune just like before ya kama kansa, cikin sanyin murya ta ce”Na amince” ya dago yana kallanta ya ce”Are u sure?” Ta gyada masa kai, tashi yayi ya nufi wajen parking ta bishi a baya, sai buya take kar Mustapha dake caan gefe ya hangota, front seat Yusuf ya bude mata ya ce”Bismillah” ta shiga ta zauna sannan ya rife ya zagaya mazaunin driver ya sawa motar key suka bar harabar wajen.
Wata hanya yabi a cikin asibitin inda ya bullo dasu wani sashe daban an rubuta pediatrics clinic & ward, parking yayi ya juyo yana kallanta ya ce”Office dinta yana ciki, zamu shiga” ita dai sai kallansa take cike da mamaki, to menene dalilinsa na karyar budurwa, lokaci daya kuma zuciyarta ya tsinke, tofa kar watarana suzo da Umminta matar ta ganta ta nuna ta santa, wata zuciyar kuma tace bafa komai kije kawai. “Rafi’ah” jin ya kira sunanta yasa ta dawo daga tinanin da take, fitowa tayi shima ya fito sannan yayi gaba ta bishi a baya, tinda take zuwa asibitin bata ta6a shiga wajen ba, yayi kyau sosai, ga doctors turawa da bakake sunata zirya cikin clinic din, suna dai dai office dinta idansa ya sauka akan magungunanta dake hannunta, yasa hannu y kar6a ta tsaya kallansa ya ce”Idan mun fito zan baki” daga haka ya cusa ledan cikin aljihunsa ya murda handle din yana kallanta ya ce”Come in”. Da sallama ya shiga tana biye dashi a baya, ya danyi murmushi yana kallan Aunt din tasa ya ce”Yau dai na cika alkawari ko?” Fara’a sosai matar take tana kallan Rafi’ah da kanta ke kasa ta ce”Masha Allah, u made it brother, wallahi na zata zakamin just like the other time” tasowa matar tayi daga mazauninta ta rungume Rafi’ah da zuciyarta ke bugawa, ta kama hannunta tana murmushi ta ce”Sannu da zuwa Kanwata pls have a seat” ta zauna tana kallan matar da take ta farin cikin, kallo daya zaka mata ka gane she is so happy at that time. Yusuf ya kalli Rafi’ah dake zaune kan kujerar office din ya ce”Sweetheart meet our first born, she’s Anty Khadija by name” murmushin karfin hali tayi ta ce”Ina yini Anty” Anty Khadija ta kamo hannunta ta ce”Lafiya kalau kanwata, fatan kuna lafiya, yasu Mamanki?” Cike da nutsuwa ta ce”Suna nan lafiya kalau”. Daga haka Anty Khadija ta mike ta bude fridge din dake office din ta dauko mata drink da glass cup ta ajiye mata a gabanta ta ce”I hope watarana zakije har gida ki gaisheni” murmushi Rafi’ah tayi ta langwa6ar da kanta kawai, Yusuf dake danna wayarsa ya dago yana kallan Aunt din nasa, sai dai baice komai ba, Anty Khadija ta kamo hannunta ta ce “Ur name sister” silenty ta ce”I’m Fatima but ana kirana Rafi’ah” Murmushi me kyau Anty Khadija ta sakar mata kafin ta ce”Wonderful, u are bearing our Mum’s name” kara saukar da kanta tayi tana ta wasa da ring din hannunta, Anty Khadija ta mike ta ce”Bari na kira a kawo maki abinci” Yusuf ya dago da sauri ya ce”A’a Aunty yanzu zata tafi fa” harara Anty ta maka masa ta ce”Bafa Yusuf nace za’a kawowa ba” ya mike yana kallan Rafi’ah ya ce “Let’s go” Anty Khadija ta bude baki tana kallansa ta ce”Are u ok Yusuf, ko ruwa ka barta tasha mana” har zaiyi magana wayar Rafi’ah ya fara ringing, ta kurawa screen din ido tana kallo ganin sunan Umminta yayi appearing, nan da nan kirjinta ya hau bugawa da karfi, karfa ta kira Doctor yace mata ya sallameta tin dazu.
“Who’s that Fatima?” Muryar Anty Khadija da taji ne yasa ta mike tana kallanta ta ce”Is my Mum, i think i have to go Aunt, thanks for d care and i appreciate” Anty Khadija ta sauke ajiyar zuciya ta ce”Ohk, Allah ya tsare, ki gaida mutanen gida” daga haka ta kalli Yusuf dake shafa tulin gashin kansa ta ce”Burinka ya cika” ya danyi murmushi ya ce”Watarana zata zo maki gida Aunt” daga haka ya nufi kofa Rafi’ah ta bishi a baya tana kara yiwa Aunty Khadija sallama, binsu tayi a baya ta rakasu har mota sannan ta dawo ciki daga nan yaja suka bar wajen. Suna komawa inda ya dauketa tayi saurin bude kofar zata nufi nasu motar ya riko hannunta ya ce”Your drugs”…
[6/9, 11:00 AM] Teemarh: *_…卮乇賷賰 丨賷丕鬲賷…_*
_{MY LIFE PARTNER}_

*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
銆帮笍銆帮笍銆帮笍銆帮笍銆帮笍銆帮笍銆帮笍銆帮笍銆帮笍銆帮笍
_We are here to Educate, Motivate and Entertain our Readers_
銆帮笍銆帮笍銆帮笍銆帮笍銆帮笍銆帮笍銆帮笍銆帮笍銆帮笍銆帮笍

*BY FATIMA* _{Real~Teemarh}_

_3~4_

A hankali ta juyo ta kar6a ledan drugs din ta ce “Thank you” daga haka ta juya ta nufi inda motarsu yake. Mustapha na ganinta ya tashi da sauri ya bude mata back seat yana ta murmushi ya ce “Kinsan turawa nawa na gani sun wuce daga fitar ki?” Rafi’ah ta danyi murmushi ta ce “To idan munje gida zan gayawa Ummi sai kuyi magana” ya sakar mata murmushi yana shafa keyarsa ya ce “Haba haba ai maganar bai kai aje gun Hajiya ba, ni ina ni ina wadannan turawan” Dariya ta danyi taci gaba da danna wayarta shi kuma yaja motar suka fita a clinic din. Suna isa gida Mustapha yayi parking ya fito ya bude mata door ya ce “A huta gajiya” ta ce “Nagode” daga haka ta nufi entrance din gidan, a hankali ta murda handle din kofar ta shiga, sai da zuciyarta ya buga ganin kallan da Ummi ta mata, ta saurin sunkuyar da kanta ta ce “Kiyi hkr, i just saw ur missed call now” Ummi ta dauke idanta a kanta ta maida kan TV ta ce “Take ur breakfast now, after all kizo” akan sofa ta ajiye ledan drugs dinta sannan ta nufi kan dinning ta dauka plate da serving spoon sannan ta bude warmer. Few minutes ta gama cakalar abincin data diba sannan ta dauka glass cup ta bude dispenser ta diba ruwa kafin ta koma parlor ta zauna, ledan drugs dinta ta jawo ta balla wanda take sha as usual sannan ta mike zata bar parlor. “Rafi’ah” sunanta da Ummi ta kira ne yasa ta tsaya, ta juyo da sauri ta ce “Ohh Ummi na manta kince idan na gama” daga haka ta koma gefen mahaifiyartata ta zauna, Ummi ta sauke ajiyar zuciya ta ce “Yanzun nan na gaya maki abu har kin manta Rafi’ah? Me yake daminki ne two days? Or are u sick this days?” Girgiza mata kai kawai tayi, Ummi ta ce “To Allah ya shiryeki, can u remind how many days baki kira Anty Halima kin gaisheta ba?” Turo baki ta danyi kafin ta ce “Ummi ce maki tayi bana kiranta?” Ummi ta mata dakuwa ta ce “Ko karya ta miki? I don’t know what’s wrong with u this days, gaba daya kinyi turning upside down” Rafi’ah ta sunkuyar da kanta ta ce “Wallahi is her fault Ummi, haka kawai sai tai ta min wata magana da bana so” Ummi ta dalla mata harara ta ce “Do as u wish, ko yayyankaki take banga dalilin rashin kiranta ba, duk duniya ina da wacce ta fita ne, ‘yar uwata daya tak a duniya kiyi kusan sati baki kira kinji lafiyarta ba, idan baki kirata ba who will u call?” Shiru tayi ta dinga jujjuya ring din hannunta bata ce komai ba, Ummi ta mike ta ce “Abbanku ma yace baki kira kin gaishe shi ba” Murmushi tayi jin an anbaci Abbanta ta ce “Ai Ummi na fita very early today, da bazan manta ba” Ummi ta ta6e baki ta tattara plate din kan dinning ta wuce kitchen.
Phone dinta dake kan TV stand ta dauka tayi dialing number Abbanta, bugu biyu ya dauka hade da sallama bayan ta amsa ya ce “Good morning Mummy nah” ta dan langwa6ar da kanta ta ce “Morning Abba, how is work?” Ya ce “All fine Mamana, u missed school today why?” cike da shagwaba ta ce “Abba naje clinic yau fa kuma ni kadai na” Abba ya sauke ajiyar zuciya ya ce “This is not safe at all, ya za’ai ta barki ki fita ke kadai?” Shiru kawai Rafi’ah tayi tana jujjuya ring din hannunta, Abba ya ce “How many days baki kira Hajiya kun gaisa ba? She called me day before yesterday and yesterday too still complaining, meya hanaki kiranta ki gaisheta? cewa tayi ma ni nake hanaki zumunci da ita” ta turo baki ta ce “Abba dazu fa Ummi ma saida tamin fada, kuma kona kira Mummy sai tai tamin maganar aure as small as i am” Murmushi Abba yayi kafin ya ce “And that not the reason da zaisa kiyi sati daya baki kirata ba Mamana, remember she the only one of your mother’s sister” a hankali ta ce “To” Abba ya ce “Not just To alone, idan baki kirata ba wallahi Abba zai manta da Mamansa yayi mata fada” ta danyi murmushi ta ce “Insha Allah Abba, when are u coming back Abba, muna ta missing dinka nida Abdul” cike da rarrashi Abba ya ce “Worry not Mamana, zan dawo ending week din nan insha Allah” ta ce “Allah ya kawo ka lafiya Abba” ya ce ” Ameen, try and be taking ur drugs kinji ko” ta ce “Yanzu ma nasha Abba” ya ce “Good, we will talk ltr in the evening i have a lot to cover” ta ce “Allah ya tsare” ya ce”Ameen Mamana” daga haka yayi hanging call din. Kwanciya tayi akan sofa kafin ta bude lock din wayarta ta kira number Mummy, yana fara ringing ta dauka, Rafi’ah tayi kasa da murya ta ce “Assalamu alaikum” ba tare da Mummy ta amsa sallamarta ba ta ce “Ai dama ubanki kadai zaice ki kirani kiyi” Rafi’ah da mood dinta ya canza ta ta6e baki ta ce “Bafa ki amsa sallamar ba Mummy kuma ba Abba yace na kira…” kafin ta rufe bakinta Mummy ta ce “Keep that ur small mouth shut, inba iskanci irin naki ba kwana nawa baki kirani ba? Ko danni ba Zainab bace?” Rafi’ah ta bubbuga kafarta a kasa ta ce “To kiyi hakuri, ni wallahi zancen auren da kikeminne banaso shiyasa bana san kiranki” Mummy taja dogon tsaki ta ce “Aida dangin ubanki ne da yanzu kin ishesu da kira, kowa da dangin uwarsa yake fara alfahari amma banda ke saboda wauta ta miki yawa, inba hauka ba me suke muku wanda kuke jin dadin sa?” A hankali Rafi’ah ta ce “To kiyi hakuri, i know i hurt but that’s not my intention, how will i not call u Mummy, bayan kinyi 1 month bakya kasar, wallahi ina missing dinki sosai” Ajiyar zuciya Mummy ta sauke kafin ta ce “Fine, ita kuma mahaifiyarki zan kirata tana tina muku cewa ni yayarta ce, ni kadai take dashi a duniyarnan tinda ba uwa ba uba” Dariya tayi a hankali ta ce “Ai munsani Mum, tana kuma gaya mana, ni maganar aure ne banaso kina min wallahi” Mummy ta ce “Bari dai na dawo kasar kafin komai, aure ko bakyaso sai kinyi shi tinda ba zama zamuyi tayi dake ba” Rafi’ah ta yatsine fuska ta ce “Ai Abba is not in support, SS2 fa kawai nake Mummy, why not idan na gama degree” Mummy ta ce “Allah ya kiyaye, kina gama secondary school zakiyi aure, shiyasa nake tina miki ki tsaida miji, shi kuma Abban naki idan bazai aurar dake ba sai ya bani ke tinda shi gani yake kamar labari kawai nake, indai ina raye sai dai ki karasa karatunki a gidan miji” Rafi’ah ta dan ta6e baki a hankali ta ce “Ai iyayena ma ba yarda zasuyi ba” Cike da masifa Mummy ta ce “Yimin bori dan ban haifa ba, da ace ina da ‘ya’ya mai zaisa na saka miki ido Rafi’ah, ai a rashin babu ne” jin mood dinta ya canza yasa Rafi’ah yin dariya sannan ta ce “Just joking fa Mummy, kiyi hakuri” Mummy ta ce “Sai anjima zan kira idan na koma gida” bata jira cewar Rafi’ah ba tayi hanging call din.
Wajajen karfe 3 na rana Rafi’ah ta tashi daga nauyayyen baccin da yayi gaba da ita, ta mike a hankali ta shiga toilet tayi brush sannan ta doro alwala ta fito, hijabi har kasa ta saka sannan ta hau kan sallaya. Bayan ta idar tayi addu’a sannan ta cire hijab din ta dauka phone dinta dake kan gado ta fice a dakin. Tafiya take cikin quick light step har ta karasa saukowa daga stairs din, ta karasa cikin falon tana kallan Ummi dake marking papers din gabanta, saam bata kula da luvly brother dinta dake zaune akan dinning ba, bayan ta zauna gefen Ummi ya taso a hankali ya cire scarf din kanta, tayi tsaki ta juya tana kallansa ta ce”Ka dawo kenan ko?” daga haka ta kwace hulanta ta saka, tana juyawa ya kara cire mata yana dariya, kamar zatai kuka ta ce “Ummi wallahi zan zane Abdul, kiga abinda yakemin” Ko kallansu Ummi batai ba bare tayi magana, Abduljalal ya zauna gefenta ya dora hannunsa a shoulder dinta ya ce “How are u Anty nah, yau a school anata tambayan ki nace kinje follow-up Clinic” a hankali ta ce “Ohk”. Bayan Ummi ta gama marking dinta ta dago tana kallan Rafi’ah da gaba daya tayi collapsing jikin Abdul tana kallo, Ummi ta dalla mata harara ta ce “Tashi ki zauna” mikewa tayi da sauri tana turo baki ta ce “To Ummi kice ya tashi na kwanta, mu 3 akan sofa daya” Ummi ta ce “Ke ki koma caan mana” ta make kafada ta ce “Ni kusanki zan kwanta” tana rife bakinta Abdul ya tashi ya nufi dakinsa yana murmushi ya ce “Na kar6i girman”. Daga haka ta koma ta kwanta tayi pillow da cinyar Umminta, bayan few minutes Ummi ta ce “What did u told Abba in the morning?” Tashi Rafi’ah tayi tana kallanta ta ce “I haven’t told him anythi…” Kallan da Ummi ke mata yasa tayi shiru ta sunkuyar da kanta, Ummi ta ce “This should be the last zamuyi abu baya nan ki kirashi ki gaya masa, sau nawa ina kaiki Clinic muna kar6an magani?” Tayi shiru still kanta na kallan kasa, Ummi ta ce”Talk now, how many times? Ya kirani dazu yana ta fada na barki kin fita ke kadai, ba Mustapha nace ya kaiki ba? shekara 17 ace bazaki iya zuwa ki kar6a common drugs ba, i still don’t like yadda Abba yake treating dinki wallahi, nayi magana harna gaji, wallahi Abdul ya fiki iya abubuwa, ya dawo kamar shine gaba dake, when will u change Rafi’ah fisabililliah?” Sai lokacin hawayen idanta ya sakko, wallahi har zuciyarta ba wai ta fadawa Abba dan yayi fada bane. Bayan hannunta tasa ta share hawayen idanta sannan ta dago ta kalleta ta ce “I’m sorry, and insha Allah i won’t repeat such thing again” Ummi ta ce “Better, kin kira Anty Haliman ne?” Ta kara turo baki ta ce “Na kirata dazu, nifa wallahi kice mata ta dainamin zancen aure inba hakaba zan daina kiranta duka duka kowa ma ya huta” Ummi ta ce “To menene damuwanki da zancen aurenta? Wallahi koda wasa kar naji kin daina kiranta, banda shashanci irin naki auran za’a miki yanzu? Ki bita kawai a hankali” Rafi’ah ta share guntun hawayenta ta ce “Kuma harda cewa wai nafisan dangin Abba da ita, ni meye ruwana dasu banda gaisuwa daya zama dole” Ummi ta ce “Ki daina min hawaye dama, koma me zata fada u have to listen, ita kadai nake dashi duk duniya, bayan ni baku da wata uwar data wuce Anty Halima” a hankali ta ce “I know Ummi but ni banason yadda Mummy take abu sometimes, komai sai tayi magana haba” Ummi ta ta6e baki ta ce “And i asked u to cook kikaje kika nemi gado kika hau bacci ko?” ta yatsine fuska ta ce “Zanyi yanzu” Ummi ta ce “It’s impossible in jira sai kin gama baccinki na jaraba kafin kiyi abinci, na gama rice kije ki rakasa stew din and if u like pls let it burn” daga haka Ummi ta mike ta dauka scripts dinta ta haura upstairs.
Kitchen ta wuce ta gauraya stew din sannan ta fito ta wuce upstairs zuwa dakinta, Hijabs dinta guda 3 ta dauko duk color daya sannan ta sakko, Abdul ta samu yana zaune yana cin banana, ta karasa kusanshi ta ce “Abdul pls help me and wash my Hijabs, kaga gobe zanje school kuma Thursday akwai hadda” ya juyo yana kallanta ya ce “Let me finish watching this match, i will wash ltr” ta shagwa6e fuska ta ce “Haba Abdul, kawai kaje ka zuba ruwa a washing machine kasa liquid detergent shine sai anjima that’s all it’s fah” ya ce “Anty banfa ce bazan wanke maki ba, wai ma meyasa ba kisa an kai laundry ba” ta zaro ido ta ce “Da Mustapha sai yayi sati bai kar6o kayanba ni inada Islamiyya jiranshi zanyi, just tell me idan baza kai ba” tashi yayi ya kar6i hijabs din yana kallanta ya ce “Is that all?” Ta bashi light hug ta ce “Thank u dan kanina me kama da Mummy” daga haka ta fashe da dariya, yaja tsaki ya ce “Ni bana kama da ita, kiba ne kawai kamar ita” bin bayanshi tayi har backyard tana ta dariya ta ce “Allah kuna kama” ya ce “That’s what people said, amma ai ni bana fada irinna Mummy, jiya fa dana kirata we spent more than 1 hour muna waya, duk kuma complain takemin a kanki” a wani balcony dake wajen ta zauna ta ce “Na kirata ai yau, ta daiyi fada kam, ni dama idan ta gama Umranta ta dawo Nigeria ta wuce Bauchi mu huta” Abdul yayi dariya ya ce “Gidansu anan kice su wuce Bauchi” ta ta6e baki ta ce “To gidanta kam sai bayan wata wata zan ringa zua”. Haka sukaita hiran Mummy har kayan ya gama turning ya tsaya, ta kalli Abdul ta ce “Dan Allah kayi spinning Abdul” ya ce “Komai zan maki ne wai” ta ce “Pls, kaga Salma Umar kaninta har nails dinta yake yanke mata idan yayi tsayi, kaga nima yayi tsayi zaka yankemin ko Abdul dina” Murmushi sosai yayi ya tashi ya fara kwashe hijabs din, duk duniya bayan Abbansu da Umminsu ba wanda ya keso sai luvly sister dinshi, he hate seeing her crying, he hate seeing her unhappy, duk wani abu a duniyar nan da zaiyi turning dinta upside down baya sonsa, wani lokaci ji yake inama lalurar da Allah ya dora mata ya dawo kansa. Ji yayi kawai ta tashi a firgice, ya juyo yana kallanta ta ce “What’s that Aunty?” Kamar zatai kuka tana kallansa ta ce “Oh my God, it’s burnt, it’s brunt i know, Allah na manta dashi ne” daga haka ta zura da gudu tayi hanyar kitchen Abdul ya bita da kallo yana kyalkyala dariya.

*Attention pls 馃檹馃徎*

*This is to inform u that i may not be able to be updating everyday, I’m still in school so sai ranar da kuka ganni kawai, but i promise u that i will try my best to be entertaining u insha Allah, so expect no date of posting, u can see me any day/time. Sannan littafin bana kudi bane na wanda ke da ra’ayin karanwa ne 馃グ*

*The page is dedicated to Fadila Madaki* 馃槏
[6/9, 11:00 AM] Teemarh: *_…卮乇賷賰 丨賷丕鬲賷…_*
_{MY LIFE PARTNER}_

*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
銆帮笍銆帮笍銆帮笍銆帮笍銆帮笍銆帮笍銆帮笍銆帮笍銆帮笍銆帮笍
_We are here to Educate, Motivate and Entertain our Readers_
銆帮笍銆帮笍銆帮笍銆帮笍銆帮笍銆帮笍銆帮笍銆帮笍銆帮笍銆帮笍

*BY FATIMA* _{Real~Teemarh}_

_5~6_

Anty Khadija ce zaune a babban parlon su da glass cup a hannunta tana shan exotic, lokaci~lokaci ta kan daga kanta ta kalli series din da ake a TV, bayan ta shanye na cikin cup din ta dago kanta tana kallan mahaifiyarta dake zaune a gefenta ta ce “Umma bafa kice komai ba?” Cike da damuwa matar da aka kira da Umma ta juyo tana kallanta, Anty Khadija ta ce “Dole ne fa Umma mu tashi tsaye, wallahi tallahi Yusuf ya kawomin budurwarsa har office dina, i’m still in a state of shock Umma, wai Yusuf da budurwa, lallai kam this is impossible wallahi” Umma ta ajiye remote din dake hannuna ta juyo tana kallan Anty Khadija, sai lokacin ta samu damar motsi, ta kirkiro murmushin takaici ta ce “Ba sai yayi auren ba idan shi yake da iko, indai ina raye rayuwar Yusuf ba zata ta6a kyau ba wallahi, sai dai ya kare rayuwarsa a haka, idan yaso ciwan zuciyar ya kashe shi” daga haka ta mike ta fara haurawa stairs, Anty Khadija taci gaba da chewing gum dinta ta ce “Atoh, indai ba’a dau mataki ba kam komai zai lalace” daga haka ta dora kafarta daya akan daya taci gaba da shan exotic dinta.
kasa dago kanta tayi tana ta wasa da fingers dinta, sai bayan Ummi ta gama mata fada ta ce “Pls don’t let me angry again, wallahi zan manta da baki da lafiya na miki duk abinda naga dama” a hankali ta ce “Kiyi hakuri” Ummi ta ce “Ki wuce ki gyara kan dinning” tabi ta gefe a hankali ta wuce zuwa parlor ba tare data bari sun hada ido da Ummi ba. Karfe 8 bayan an idar da sallan isha Yusuf ya shigo parlor, milk shadda ce a jikinsa ta sha aiki, tayi masifar amsar jikinsa kamar dama saboda shi akayi ta, kallo daya Umma ta masa ta dauke kanta, ba yabo ba fallasa ya dan saki fuska ya ce “Sannu da gida Umma” a hankali ta ce “Sannu” Anty Khadija ta ce “Doctor sai yanzu?” ya ce “Wallahi Anty, nayi meeting ne shiyasa na dawo late” ya karashe maganar yana cire lab coat din jikinsa ya nufi dakinsa, Anty Khadija ta bishi da harara kasa kasa ta ce “Wicked man” Umma ta ce “Not only wicked” Anty Khadija ta ta6e baki looking into her mother’s eyes ta ce “Ni wallahi Umma a duniya idan akwai wanda na tsana ya biyo bayan Yusuf, duk da nunawa nake ina san shi ina kaunarshi amma bakiga da yadda nasa ya kawomin budurwarta saba” Umma ta harari kofar dakinsa ta ce “Yanzu haka ma wajenta yaje zaice wani meeting yayi, indai ina raye kaida farinciki kunyi sallama, aure kuwa sai dai yaga anayi” Anty Khadija ta ce “Sai fa kinyi da gaske kin kara cusa masa tsanar rayuwar aure, ni dama i just wanted to know ko yana da budurwa yasa na matsa masa, kuma na ganta, fara sool, gata yarinya da ita” Umma ta ce “Ina nan dake shida kansa zaice baya santa wallahi, banda shi ba ma yaji da ciwan dake daminsa zai jajibowa kansa soyayya, ai insha Allahu wannan yarinya itace ajalinsa” Anty Khadija tayi murmushi ta ce “Allah yasa, kinga idan ya mutu ai wancen tsohon zai daina mana maganarsa kowa ma ya huta” Umma ta ce “A juri zuwa rafi dai” kiran daya shigo wayarta ne yasa tayi shiru ta dauka wayar ta kara a kunne, bayan ta gama answering call din ta ce “Wai yaushe Jiddah zata dawo ne Umma?” ta ce “Duk sanda kika dawo da ita, dama bake kikace ta tafi a gidan ba” Anty Khadija ta ce “I’m thinking about something, why not muyi amfani da Jiddah ta hanyar rushe soyayyar Yusuf da waccen yarinyar” Umma tayi murmushi ta ce “Haka ma yayi” daga haka Anty Khadija ta mike ta nufi upstairs tana dialing phone number din Jiddah.

Ranar Friday da yamma Rafi’a na zaune a dakinta tana tilawa Abdul ya shigo rike da phone dinsa ya na “Mummy want to talk to u” ta kar6a wayar ta kara a kunne hade da sallama, Mummy ta ce “I don’t really know the essence of ur phone Fatima, why is it always off? Haka saurayinkin yake kiranki yaji ko yaushe a kashe” Abdul ya sheke da dariya harda kwanciya, turo baki kawai tayi kafin ta ce “Ni Islamiyya zan tafi ai mun gaisa” Mummy ta ce “Kika kashemin waya wallahi sai ranki ya 6aci, daga tambaya zaki taramin mutane wani wai islamiyya, Allah yasa Madina zaki taho” Qur’an din ta ajiye gefen bed side drawer ta mike tsaye, Mummy ta ce “To dama next week zan dawo, nace bari na fada da wuri dan ranar dana sauka dake zan wuce gidana” kallan wayar kawai Rafi’ah take with confusion ta ce “I will just go and see u Mummy, Abba ya hanani barin gida” Mummy taja tsaki ta ce “Sai na gani ai, na ta6a jin yadda ake hana diya taje wajen yayar uwarta, shekara nawa ina naci ya bani ke baiban ba na hakura, sai dan kwana uku zuwa hudun da zakimin zai hana, da anyi magana yace ba lafiya kike dashi ba, ai yanzu kam we have to drop a very big thank to God, Zainab tacemin bai fiye tashi ba yanzu ko?” daga mata kai tayi kamar tana gabanta sannnan ta mikawa Abdul wayarsa ta ce “To Allah ya kawoki lpy” Mummy ta ce “Alright sai anjima” daga haka tayi hanging wayar.
Dai dai lokacin Ummi ta bude kofar dakin, ta dinga kallan Rafi’ah dako uniform din boko bata cire ba, gashi har ana shirin islamiyya, Ummi ta ce “Why haven’t u remove ur uniform Fatima?” A hankali ta ce”I slept off bayan na dawo, yanzu zanyi shirin islamiyya” Ummi ta ce”Hope u are not sick?” Girgiza mata kai tayi ta ce “Noo, stress ya sani bacci Ummi” ta ce “Ohk, Abba yana hanya fa” tayi wani tsalle hade da kara ta ce “Are u serious Ummi?” Ta daga mata kai ta ce “Sure, ya kiraki bai sameki ba” gaba daya she can’t hide her happiness, ta rungume Ummi cike da shagwa6a ta ce “Almost 2 months fa banga Abba ba Ummi, amma dai muma 2 months zai mana ko?” Ummi ta zameta a jikinta ta ce “I don’t know” Rafi’ah ta zauna gefen gado ta ce “Is he alone?” Ummi ta dalla mata harara ta ce “U can call him and ask” turo baki tayi ta tashi ta fara cire uniform dinta ta ce “Ai nasan waccen matar saita biyoshi” Ummi dai bata kula taba ta kalli Abdul dake kwance kan gadon Rafi’ah ta ce “Kai ba zaka je islamiyyan bane?” Ya mike yana kallanta ya ce “Zanje Ummi” ta ce “Oya do fast is after 4 now” daga haka ta fice a dakin yabi bayanta shima. Har Abdul ya shiya ya dinga jiran Rafi’ah a mota bata fito ba, ya kalli Mustapha dake kallan film din india a wayarsa ya ce “Let me check on her” daga haka ya koma cikin gida, a parlor ya samu Ummi tana tasa turaren wuta, ta juyo tana kallansa ta ce “Baku tafi bane, karfe 4 da rabi fa” ya tsaya yana kallanta ya ce “Anty isn’t out fa Ummi” ta ajiye kwaskon hannunta ta nufi stairs ta ce “The only thing Rafi’ah can do fast is to sleep, in dai bacci ne tana kwanciya bata kara minti daya” tana bude kofar dakinta ta sameta a gaban mirror tana ta fama da trouser dinta ta kasa daure tazuge, dama mostly Ummi ke daura mata ko Abdul, itama ta koya amma yau gaba daya ta rasa kan abin ta masa kulli yafi hudu, dago kanta tayi tana kallan Ummi kamar zatai kuka ta ce “Help me pls Ummi, i can’t do it, tin dazu yaki zama, my neck is even aching” Ummi taja tsaki ta karasa gabanta ta durkusa tana gyara mata ta ce “Keep shut now before i give u a dirty slap, when was the last time na koya maki daura abin nan” kamar zata fashe da kuka ta ce “Ummi ni kasawa nayi, I’m just trying my best but na kasa daurawa” mikewa Ummi tayi bayan ta gama daura mata ta ce “Wear your hijab and come out now” ta dauka zulelen hijab dinta har kasa ta saka sannan ta lankaya side bag dinta da qur’an ke ciki ta biyo bayan Ummi, bayan sun sauko ta bata light hug ta ce “Pls Ummi kiyi ma Abba hug dina kafin na dawo na mishi wani” Ummi ta dalla mata harara ta wuce kitchen, murmushi tayi ta fita a parlo’n ta wuce parking lot, bayan ta shiga motar Abdul ma ya shiga, Mustapha ya juyo yana kallanta ya ce “Wani film din india nake kalla Hajiya Rafi’ah, yarinyar yadda kikasan ke, komai naki take, ita fa har takalmin makaranta mahaifiyarta take saka mata” dalla masa harara Rafi’ah tayi ta shiga turo baki, hakan yasa yayi shiru yaci gaba da tukinsa, dan yasan yau babu me ta6a Rafi’ah tinda Abba yake hanya, in kwa aka ta6a ta har abinda aka mata tin tafiyarsa saita juye masa, shima Abdul shiru yayi ganin irin 6ata ran da tayi, bayan few minutes ta ce”Ai duk kaika fada mishi” Abdul ya zaro ido ya ce “I’m not the one sis, have u forgotten he said… ” toshe kunnuwanta biyu tayi, cikin tsawa ta ce “I don’t want to hear anything pls” shiru yayi ya juya kansa gefe, yasan by this time kam sunyi late kuma ana duka, shi kuwa tinda ta masa shouting bazai kar6a mata duka ba yau.
Mustapha na parking suka fita yaja mota ya barsu a wajen, Abdul ya nufi gate din ya tura, zaro ido tayi ganin students a compound ana ta dukan lattee, Abdul ya danyi murmushi ya shige ciki tabi bayansa, duk gaba daya ta gama tsorata sai numfashi take saukewa daki daki, ga idanuwanta da suka fito alaman tsoro, bayan an yiwa kowa Abdul ya mika hannunsa aka masa guda hudu ya wuce, Rafi’ah da duk ta rude ta ce “Pls don’t leave me Abdul, pls help me kaji dan Allah” ko ya juyo ya kalleta ya shige ciki abinsa, Malamin ya daure fuska yana kallanta ya ce “Kawo hannunki” ta ce “Ai Abbana yazo ya fadawa Malam Ahmad kar ana dukana, bani da lafiya wallahi” wani kallan rashin mutunci ya mata ya ce “Ai kowa ma ba lafiya ce dashi ba, ki kawo hannunki na dakeki ki wuce aji an fara kar6an hadda” ta dukunkune one side ta ce “Pls let me go, i promise not to come late again, dan Allah kamin hakuri” Tinkarota malamin yayi ta fasa kara jikinta ya hau rawa, har idanta ya cika da kwalla ta dago tana kallansa ta ce “For God sake na roke ka”. Muryar wani malami sukaji yana cewa “Wannan ai mahaifinta yazo tin shigarsu islamiyya ya sami headmaster, ai ba’a dukanta Malam Umar” ko kallansa Malam Umar baiyi ba ya ce “Su sauran ‘ya’yan da aka daka ba mutane bane, dan meyasa zaku ware ta ace baza a ta6a taba, ni ba ruwana da ubanta koshi waye dukanta zanyi wallahi” Malam Sadeeq ya ce “Ba batun ‘yar wani bace Malam, indan haka za’a bi ai rabi da quarter ba dukansu za’ai ba, ina maka bayani ne akan akwai dalilin da yasa ba’a dukanta” ganin ko kallansa baiyi ba yasa ya wuce ya barsu a wajen, sai lokacin hawayen idanta suka gangaro kasa, ya daka mata tsawa ya ce “Bani hannunki kona miki a jiki ki wuce” girgiza masa kai ta hau yi ta saita kofar gate ta fita a dari da sittin.
Cikin saurin ya taka birki yana fadin innalillahi, itama gaba daya ta tsoruta jira kawai take taji an kade ta, jin shiru yasa ta bude hijabinta a hankali tana kallan gabanta, sai kuma ta sunkuyar da kai ta kasa magana, Yusuf ya fito a motar sanye da lab court, daga gani yanzu ya tashi a clinic, ya dinga kallan Rafi’ah da kanta ke kasa ya ce “U again” ta dago da sauri jin muryarsa, suna hada ido ta saukar da kanta kasa, ya matso kusa da ita ya ce “U haven’t forgot the other incident right?” Ta girgiza kai a hankali ta ce”It isn’t my fault that time, shine yazo ya bigeni without me knowing and baiyi horn ba” ya danyi murmushi yana kallanta ya ce “Yau fa?” ya karashe magana yana shafa beard dinsa, ta kara sunkuyar da kai ta ce “I’m sorry it wasn’t intentional, and dukana za’ai” Yusuf ya dan zaro ido ya ce “Who?” Ta ce “Malam Umar” ya kalli gate din islmiyyar sannan ya kalleta ya ce “Why?” Kamar zata fashe da kuka ta ce “Is because i’m late” ya ce “And why did u came late?” Sai lokacin ta dago kanta tana kallansa ta ce “Na kasa daura tazugen wandona shin… ” zaro ido tayi da sauri taja baya, sai a lokacin ta lura saam bai dace ta fada masa haka ba, ya danne dariyar dake cinsa ya ce “Then what?” Ta fara kame kame ta ce “Noo i slept off…. Yes i slept and… And i woke up very late..Very late i swear”
[6/9, 11:00 AM] Teemarh: *_…卮乇賷賰 丨賷丕鬲賷…_*
_{MY LIFE PARTNER}_

*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
銆帮笍銆帮笍銆帮笍銆帮笍銆帮笍銆帮笍銆帮笍銆帮笍銆帮笍銆帮笍
_We are here to Educate, Motivate and Entertain our Readers_
銆帮笍銆帮笍銆帮笍銆帮笍銆帮笍銆帮笍銆帮笍銆帮笍銆帮笍銆帮笍

*BY FATIMA* _{Real~Teemarh}_

_7~8_

Folding hannayensa yayi yana kallan idanta ya ce “This is not strictly true” ta saukar da kanta kasa a hankali ta ce “It’s true” murmushi me kyau yayi ya dan matsa gefe kafin ya ce “To ki shiga ciki” ta noke kafada ta ce “No, i’m going back home” ya ce “Why?” Ta ce “Yace zai dukeni to” ya danyi murmushi yana shafa tulin gashin dake kansa ya ce “To muje na kar6a maki” ta dan zaro ido ta ce “Are u serious?” Ya ce”Sure let’s go” ta saki wani daddaden murmushi tabi bayansa suka shiga gate din. Ba kowa a compound din sai sound din karatun student, ya juyo yana kallanta ya ce “where is ur class?” Ta nuna masa upstairs da hannunta ta ce”A sama ne” bin staircase din yayi da kallo kafin ya fara takawa tabi bayansa. Suna hawa ta nuna masa class dinsu, ya shiga da sallama ya mikawa malamin hannu, ita dai Rafi’ah na tsaye bakin door tana kallansu, bayan sun gama magana Yusuf yayi masa godiya sannan ya fito, a dai~dai bakin kofa ya tsaya yana kallan Rafi’ah ya ce “U can go in, and kicewa Umma a dinga saka maki robber a wando ba tazuge ba” tayi saurin rife fuskarta da hijab dinta, ya danyi murmushi a hankali ya ce “Bye bye” daga haka ya nufi stairs ya fara sakkowa, Yana fitowa ya shiga motarsa yasa mata key ya wuce.
Minti 10 ya kaishi gida, yayi horn gate man ya bude sannan ya shiga yayi parking, fitowa yayi ya bude back seat ya dauko laptop dinsa da lab coat sannan ya nufi entrance din gidan, da sallama ya shiga parlon fuskarsa hade da murmushi as usual, Jiddah ta taso da sauri ta kar6i laptop din hannunsa tana farfara ido ta ce “You are welcome Ya Yusuf” shi dai kallanta kawai yake da mamaki, ta turo baki ta ce “Ya Yusuf ba magana kuma” sauke idansa yayi a kanta ya ce “Thank u, when did u came back?” Fuskarta dauke da murmushi ta ce “In the morning” Ya ce “U are welcome” daga haka ya wuce dakinsa tabi bayansa, kan bed ya nuna mata ta ajiye masa laptop din sannan ta juyo tana kallansa ta ce “Yaya” ya ce “I’m all ears?” Ta ce “What will u eat” juya kansa yayi gefe baice komai ba, ta dinga kallansa kafin ta ce “Or are u not hungry?” Sai lokacin ya sauke ajiyar zuciya ya ce “I just need a cup of tea” ta ce “Alright, bana hada maka” daga haka ta nufi kofar fita ya bita da kallo.
Jiddah na hada tea tana ta murmushi Anty Khadija ta shigo kitchen din, strictly ta dinga kallanta kafin ta ce “Wa kike hadawa tea da la’asar din nan” Jiddah ta juyo tana murmushi ta ce “Anty Khadija Ya Yusuf ne ya dawo, and he want to take a cup of tea” Anty Khadija taja dogon tsaki ta karasa gabanta ta dauka cup din tea din ta zubar cikin sink kafin ta kama kunkuminta tana kallan Jiddah eyes into eyes ta ce “Ubanwa yasa ki hada masa tea?” Sauke kanta tayi kasa ta ce “Anty Khadija naga yanzu ya dawo a Clinic kuma yana bukatar kulawa tin safe… ” bige bakinta Anty Khadija tayi ta ce “Keep quite before i give u a dirty slap, kawai daga ganin sarkin power sai miya tayi zaki, an gaya miki kulawa dashi kika zo yi” Murguda mata baki Jiddah tayi kafin ta ce “To ke ina ruwanki dani, nifa gaskiya bazaki takuramin ba wallahi, ki fita a harkata kawai, idan ba haka ba duk abinda na miki ke kika sani” daga haka tayi wucewarta fuuuuuu ta barta tsaye a wajen. Mamaki sosai ya kama Anty Khadija ganin abinda Jiddah ta mata, har yaushe bakinta ya bude da zata na fada mata maganganu irin haka, ta sauke ajiyar zuciya kafin ta fita a kitchen din tayi hanyar stairs.

Alhaji Muhammad Sageer shine mahaifin Yusuf, babban dan kasuwane sannan yana da tarin dukiya, Alhaji Muhammad mutum ne mai san mutane da taimakon talakawa, matarsa kwaya daya tak me suna Aisha, shekararsu 5 da aure sannan ta haifi Yusuf, tin daga lokacin ya dauki san duniya ya daurawa Yusuf, idan kanaso kaga 6acin ransa to ka ta6a masa only son dinsa a rannan ne zakaga 6acin ransa kaca~Kaca. Watarana suka dauki hanyar Kaduna dan zuwa ziyarar ‘yan uwa da abokan arziki, a hanyarsu ta dawowa sukai hatsari Allah ya kar6i ransa da matarsa, a lokacin Yusuf nada shekara 15. Tin daga ranar kanwar mahaifin Yusuf ta kar6eshi, zama na rashin dadi Yusuf yake a hannunta, daga haka har ta kafe ta tsare duk wani gadon Yusuf ya dawo hannunta, gashi ba komai take masa ba, kai kace ba da dukiyarsa take shanawa ba, itama mijinta ya mutu sai ‘yarta kwaya daya Khadija, tin daga lokacin bata kara aure ba, itace waccen kasa gobe wannan, ta sayi gidaje da dama bayan na gadon Yusuf, daga haka ta tsunduma cikin kasuwanci, kan kace kwabo kudi sai kara haka6a yake, sai dai Yusuf ba abinda ya karu da kudin duk da kudinsa ne, karatun likitanma da yayi a Dubai mijin kanwar mahaifiyarsa ce ya biya masa, bayan ya tafi itama Umma ta biyawa Anty Khadija tayi karatunta a kasar Cyprus, kusan a tare suka dawo, suka kuma fara aiki a tare sai dai kowa inda yake aiki da ban ne.
Jiddah ‘ya ce agun kanin mahaifin Khadija, shekararta 20 kacal a duniya, gidansu yana nan kusan su Anty Khadija, tinda Yusuf ya nuna yana santa Anty Khadija ta koreta wai sai ta koma gidansu saboda ba gidan ubanta bane, watan ta kusan 5 bata gidan, sai yanzu ta kirata ta bata hakuri saboda dawowanta zai mata amfani wajen 6ata soyayyar Yusuf da Rafi’ah a yadda ta dauka soyayya suke.

*馃槂 sorry ina busy wallah, ziyara nake kota ina, but i promise akwai update gobe insha Allah.*

_08103810398_
[6/9, 11:00 AM] Teemarh: *_…卮乇賷賰 丨賷丕鬲賷…_*
_{MY LIFE PARTNER}_

*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
銆帮笍銆帮笍銆帮笍銆帮笍銆帮笍銆帮笍銆帮笍銆帮笍銆帮笍銆帮笍
_We are here to Educate, Motivate and Entertain our Readers_
銆帮笍銆帮笍銆帮笍銆帮笍銆帮笍銆帮笍銆帮笍銆帮笍銆帮笍銆帮笍

*BY FATIMA* _{Real~Teemarh}_

_9~10_

Anty Khadija na gama hawa upstairs ta wuce dakin Umma, nan ta samu Jiddah ta gama fada mata duk abinda ya faru, cike da masifa Anty Khadija ta ce “Ubanwa kika murgidawa baki?” Jiddah ta 6ata rai tana kallan Umma ta ce “Kingani ko Umma, ni kenan kullum sai taita takuramin, what’s her business with me?” Anty Khadija ta nuna ta da yatsa ta ce “Sai in kakkaryaki wallahi na zubar da abin banza” Tsawa Umma ta daka musu ta ce “Enough is enough” duk shiru sukai sai numfashi da kowaccen su ke saukewa in a bad mood, Umma ta ce “Ku dai wallahi anyi asararru, banda asara ta muki yawa menene abin fada a wannan lamarin, don’t u know u are blood, to be sincere duk wacce ta kara min fada a gidan nan wallahi i will surely deal with her, And let me remind u this, da ubanki da uban Jiddah uwa daya uba daya suke, your father is immediate after jidda’s father, amma baki da abokiyar fada sai ita” a kusan tare duk suka ce “Kiyi hkr” ta zauna taci gaba da danna wayarta, fita Jiddah tayi a dakin kafin Anty Khadija ta sauke ajiyar zuciya ta ce “Umma Yusuf fa take hadawa tea, kuma ni tsorona kar ta sake sakashi a ranta dan wallahi ba auransa xatai ba” Umma ta dago tana kallanta a bid shock ta ce “Allah ma ya kiyaye Jiddah ta hada jini da Yusuf, Allah na tuba me zatai da me ciwan zuciya lokaci daya ya mutu ya barta da kuruciyarta” Anty Khadija ta ce “Umma wallahi gani nake yana santa har yanzu, kuma itama akwai yiwuwar tana sanshi, nifa kawai na kirata ne ta dawo ta shiga tsakaninsu da waccen bafulatanar yarinyar, daga nan ta kama gabanta” Umma ta dinga kallanta kafin ta ce “Babu inda Jiddah zataje Khadija, tana nan tare damu, ko wancen lokacin da kika koreta i was somehow busy yasa banyi magana ba, saboda haka yadda kike zaune a gidan nan Jiddah ma na nan” cike da fishi Anty Khadija ta ce “To gaskiya kija mata kunne ta daina wuce gona da iri, idan ba haka ba… ” katseta Umma tayi ta hanyar cewa “Ai da wata caan daban ta auri Yusuf gara Jiddah ta aureshi ta dinga juya shi akan ya samu kwanciyar hankali, an gaya miki duk duniya inada makiyi irin Yusuf ne? Ko a lahira bana tinanin zan gafartawa uwarsa, nida dan uwana ta mallakeshi ta hanamu muyi zumunci har Allah ya kar6i rayuwarsa, gashi data tashi haihuwa saita haifo me kamarta, Yusuf dai babu abinda ya bari a jikin Aisha shiyasa dana ganshi nake tuno ta a rayuwa” Anty Khadija ta ta6e baki ta ce “Muje zua dai” daga haka ta juya itama ta fita a dakin.
Jiddah na zaune a parlor Yusuf ya fito a dakinsa cikin jallabiya ash, tayi matukar kar6ensa sai kamshi yake zubawa, ta dago tana kallansa ta ce “Ya Yusuf sorry for keeping u waiting, nazo zan hada maka naga babu milk” a hankali ya zura hannayensa biyu a pocket dinsa kafin ya ce “It’s ohk” daga haka ya fita a parlorn. Karfe shida saura su Rafi’ah suka dawo gida, ko gama parking Mustapha baiba ta fito da gudu ta nufi cikin gida, Ummi ce a zaune akan kujera tana operating laptop sai Abba dake cin abinci akan dinning, ganin yadda ta shigo da gudu yasa Ummi ta daka mata tsawa ta ce “Are u stupid, why won’t u walk like a human being” Abba dake kallan Rafi’ah ya ajiye spoon din hannunsa ya ce”Why all this shout Madam, komai ne sai anyi fada” shiru Ummi tayi taci gaba da abinda take, Rafi’ah ta karasa cikin quick steps ta rungume Abba, shafa bayanta ya hau yi yana murmushi ya ce “How are u daughter” tayi shiru bata ce komai ba saima kara narkewa da tayi a jikinsa, ya ce “Kinyi karatu sosai?” Nan ma shiru bata ce komai ba, dago kanta yayi a kirjinshi yaga hawaye sha6e~sha6e a fuskarta, ya shiga share mata cikin rarrashi ya ce “Why all these tears Fatima?” a hankali ta ce “I missed u alot Abbana” daga haka ta kara rungumeshi, murmushi Abba yayi ya bata light kiss akanta ya ce “It’s ohk, ba gashi Abba ya dawo ba?” Ta daga masa kai itama tana murmushi, handkacheif ya ciro a pocket dinsa ya share mata idanta kafin ya kama hannunta suka zauna, dai dai lokacin Abdul ya shigo da jakar Rafi’ah data bari a mota, ya rungume Abba ya ce “U are welcome” Abba ya shafa gashin kansa ya ce “Thank u son, how is everything?” Cike da fara’a ya ce “All is fine Abba” ya mike yana kallan Ummi ya ce “We are back” ta ce “Sannu” daga haka ya haura stairs.
Rafi’ah na jikin Abba har aka kira sallan magrib, ya dan shafa kanta ya ce “I’m going to mosque sweetheart” mikewa tayi a jikinshi ta ce “Alright Abba, a dawo lafiya” kan dinning ya nuna mata ya ce “Ga caan tsaraban ki” tayi murmushi me kyau ta ce “Nagode Abba” daga haka ta nufi wajen ta dauka ledan Apple da chocolates different types, up stairs ta nufa da ledan a hannunta, Abdul dake tsaye yana balle links dinsa ya ce “Abba ya wuce mosque ko?” Ta ce “No, he’s waiting for u” daga haka ta shige dakinta ta ajiye ledan a kan dressing mirror ta shiga cire uniform dinta. Sleeping dress ta saka iya knees dinta me siririn hannu, ta kara combing kanta sannan tayi packing dinsa da peach ribbon, sai tayi mungun kyau kamar baby doll, instead tayi alwala tayi sallah sai ta zauna ta dauka chocolate ta bude tana sha, har wani limshe ido take tsabar dadi, tana cikin sha aka bude kofar dakin, ta dan zaro ido tana kallan Ummi dake kallanta surprisingly enough, ajiye chocolate din tayi ta mike ta ce “I want to pray now” mari Ummi ta kai mata tayi saurin kaucewa ta shige toilet, Ummi da ranta ya gama 6aci ta ce “I will catch u” daga haka ta tattara ledan Apple dana chocolate ta fita dasu zuwa dakinta. Few minutes tayi taking a toilet sannan ta fito ta saka babban hijab ta tada sallah, bayan ta idar ta cire hijab din ta hau kan gado ta kwanta ranta duk babu dadi ganin babu abubuwanta a inda ta ajiye. Sai da su Abdul sukai sallan Isha sannan suka shigo gida, Abdul ya wuce kan dinning dan yin dinner Abba kuma ya zauna gefen Ummi, murmushi Abba yayi ya ce “Hajiya ba’a gajiya da aiki ne?” Ummi ta rife laptop din gabanta ta ce “Next week fa holiday zai kare, shiyasa na fara research a kan course outline, u know we have only 7 weeks to cover” Abba yayi nodding happily ya ce “Hakane Ummu Rafi’ah, fatan student basa samiki ciwan kai” murmushi tayi ta ce “Not at all, ko lectures muke the hall was so quite, so u don’t have to worry kasan fa lecturing was my hobby since” Abba yayi dariya ya ce “I’m the first person to witness that, nida ake barmin Mamana a wajen nannies a tafi aiki” dariya Ummi tayi ta ce “To ba gashi yanzu ya wuce ba?” Looking smiley ya ce “Hakane”.
Bayan few minutes ta juyo tana kallansa ta ce”Yallaboi i have a lots to talks with u” Abba ya ce “Go ahead, yau kam ai a gidan ki nake” Ummi ta dan juya kai ta ce “I though zaka tafi wajen matarka ne” Abba yayi murmushi ya ce Haba first wife, don’t judge me wrong mana, matar dana dawo da ita kuma naje wajenta? Kema ai kinsan always ranar da muka dawo nan nake kwana biyu kafin na shiga caan, last time ma bata da lafiya ne that’s why na kwana” Ummi ta ce “Alright” ya ce “I’m all ears” ta danyi ajiyar zuciya kafin ta ce “Akan Rafi’ah ne dama” Abba ya dan zaro ido thinking something bad happens to her ya ce “Meya faru, ina kikace ciwan ya dade bai tashi ba sosai?” Ummi ta ce “A’a she’s getting better now, but pls yallaboi ka zauna kayi mata fada, saam Rafi’ah bata da nutsuwa musamman this two days, na bata girki ta kona, running any how, babu ruwanta ko a gaban waye, walking without scarf, in dai gaya maka yanzu Abdul yafi ta nutsuwa, zaka rantse kace shine gaba da ita” Abba ya numfasa ya ce “That’s doesn’t mean ki dinga mata tsawa kina firgita ta, and don’t judge me wrong, nasan u are the number one witness da zaki fara bada labarin ciwan yarinyar nan, u know she’s suffering from heart attack, little thing or such zai iya kawo mata attack, ba wai bazan iya mata fada bane, i can do it, but a little, a yanzu babu abinda take bukata irin kwanciyar hankali da kulawa, just pray for her, i don’t want to loose her” a hankali Ummi ta ce “But… ” katseta yayi ta hanyar cewa “But what? Dan Allah mu bar maganar nan a nan Madam” Ummi ta ce “Allah ya shirya mana, ya bata lpy” Abba ya ce “Ameen” kallan Abdul yayi dake game a laptop ya ce “Call ur sis for me” Abdul ya mike ya nufi stairs, kwance ya sameta akan gado tayi shiru, ya zauna gefenta yana shafa cute face dinta ya ce “Anty Abba is calling u” tashi tayi a hankali ta ce “To” tabi bayansa har suka sakko kasa, gefen Abba ta zauna ta dan turo baki ta ce “Gani Abba” ya jawota jikinshi ya bata side hug ya ce “What’s wrong with u Mamana” kallan Ummi tayi dake zaune sannan ta sunkuyar da kanta ta ce “My chocolate” tana dago idanta suka hada ido da Ummi, tayi saurin boye fuskarta a kirjin Abba, ya shafa smooth hair dinta ya ce “Zata baki idan ta tashi, gobe da safe kuma kuje ku yiwa Antyn ku sannu da dawowa” Rafi’ah ta kara turo baki btace komai ba, Abba ya ce “I’m i not talking to Rafi’ah” sai lokacin ta dan kalleshi ta ce “To” Abba ya kalli Ummi ya ce “Nikam meyasa ba’a yiwa Mamana kitso? ga gashi har baya amma ba kitso” Ummi ta ta6e baki ta ce “Ba so take ba” Abba ya kalleta ya ce “Why Mamana?” Ta ce “Abba me zafi fa akemin” ya kalli Ummi ya ce “Next time dama kar a mata me zafi” Ummi dai bata ce komai ba taci gaba da arranging papers din da tai marking.
Karfe 10 Abba yace kowa yaje ya kwanta, Rafi’ah ta rungumeshi ta ce “Bye bye Abba” ya shafa fuskarta ya ce”Good night Mummy” ta rungume Ummi ma ta ce “Night sweetheart” Ummi ta shafa bayanta ta ce “Night, and don’t forget to say ur du’ah” ta ce “Insha Allah” harta tafi sai kuma ta dawo ta ce “Dan Allah Ummi na dauka chocolate daya” Ummi ta ce “No, da safe zan baki” ta juya ta fara haurawa stairs bayan ta musu bye bye, dakin Abdul ta shiga ta sameshi yana kallo a system, itama zama tayi gefensa ta fara kallan itama.

*SHARIK HAYATI*

_08103810398_ [6/9, 11:00 AM] Teemarh: *_…卮乇賷賰 丨賷丕鬲賷…_*
_{MY LIFE PARTNER}_

*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
銆帮笍銆帮笍銆帮笍銆帮笍銆帮笍銆帮笍銆帮笍銆帮笍銆帮笍銆帮笍
_We are here to Educate, Motivate and Entertain our Readers_
銆帮笍銆帮笍銆帮笍銆帮笍銆帮笍銆帮笍銆帮笍銆帮笍銆帮笍銆帮笍

*BY FATIMA* _{Real~Teemarh}_

_11~12_

The next day bayan an gama breakfast sunyi shirin Islamiyya Abba yace suje su gaisar da Antyn su, Rafi’ah tayi kicin~kicin da rai tayi kamar bata ji ba, ganin Abba ya tashi ya haura upstairs yasa Abdul ya kalleta ya ce “Anty muje mana, sai mu tafi kar muyi latti” farfara idanuwanta tayi ta kara rungume side bag dinta ta ce “I’m not going, idan zakaje sai kai kaje” Abdul ya mike ya ce “Do u want Abba to makes u angry?” Kin kulashi tayi ta fara wasa da ring din dake hannunta, ganin haka yasa ya dauki bag dinsa ya fita a parlorn. Bayan few minutes Ummi ta fito a kitchen rike da flask a hannunta ta dura akan dinning, kallan Rafi’ah tayi ta ce “Have u eaten?” Ta daga mata kai, Ummi ta ce “What of your drugs?” Ta ce “Yess i took all” daga haka Ummi ta juya ta koma kitchen, horn din mota da taji ne yasa ta mike ta dauka 500 da Abba ya bata sannan ta fita waje.
Yusuf ne zaune a office dinsa yana kallan test din da aka masa, ya limshe idanuwansa yana girgiza kai ya ce “Innalillahi” bude kofar Office din akayi Dr. Aliyu ya shigo da sallama, shima duk jikinsa yayi sanyi ya karasa kusa da Yusuf ya dafa shoulder dinsa, bayan minti 5 ya sauke ajiyar zuciya yana kallan Yusuf ya ce “How comes Dr.? meyasa duk test din da ake maimakon yayi normal sai yayi gaba, Yusuf kafi kowa sanin hatsarin ciwan zuciya fa, i don’t mean to explain such” share dan guntun hawayensa Yusuf yayi yana kallan Aliyu ya ce “I don’t know Doctor, I don’t really know what’s wrong with me” he said in a husky voice, Aliyu ya limshe idanuwansa kafin ya budesu ya ce “Yusuf”, dago kansa yayi a hankali , Aliyu ya ce “U know, kasan kanada ciwan zuciya Yusuf, but why are u playing with your life, so kake ka mutu ko menene hakan?” Kasa saukar da kansa Yusuf yayi cikin sarkarkiyar murya ya ce “My… Pa..re..nt., i’m a loving child Aliyu, how can i forgot my parents? Forgot my happiness? The only once who makes me smile all d time? yau iyayena sun cika shekara 7 da rasuwa, why will i not recall and pray for them Aliyu, so kake na manta dasu? Kasan it’s not easy and it’s impossible” daga haka yasa hannayensa biyu yayi wiping tears dinsa, shiru Dr Aliyu yayi for some minutes kafin ya zauna a chair din dake gefensa ya ce “I know u must remember them Yusuf, they need prayer than any orther thing apart, kayi ta musu addu’a insha Allah suna cikin rahama, amma dan girman Allah ka rage yawan tinani Yusuf, kafi kowa sanin condition dinka, lafiyar ka tafi komai a yanzu” murmushi Yusuf yayi a hankali ya kama hannun Aliyu ya ce “Thank u so much, I’m very proud to have a friend like u” Aliyu ya mayar masa da murmushi ya ce “Ba komai, amma dan Allah a kiyaye” Yusuf ya mike yana cusa test din cikin pocket dinsa ya ce “Insha Allah, ina musu addu’a a kullum Aliyu, but idan shekara ya zagayo i really feels it deep down me, especially when the exact date comes” Aliyu ya ce “Allah ya musu rahama” Yusuf ya ce “Ameen” daga haka ya mika masa hannu ya ce “Till tomorrow” Aliyu ya ce “Alright, Allah ya kaimu”. Suna fita yasa key ya rufe office dinsa sannan yayi wa sauran Doctors din sallama ya fita.
Slowly ya dinga tafiya cikin motarsa harya iso unguwar Rimi gidan kanwar Amminsa, dai dai kofar wani babban gida yayi parking sannan ya fito rike da phone dinsa ya shiga gidan, gate man kawai ya gani a compound yana watering flowers, bayan sun gaisa ya nufi entrance din gidan, yana murda handle din kofar yaji a bude ne, hakan yasa ya shiga hade da sallama yana murmushi. Da gudu wata cute little girl ta nufoshi, ya dagata sama ya ce “Oyoyo little” ta kankameshi ta ce “You are welcome Yaya” yaja hancinta yana sauketa ya ce “Ina Mami?” Ta ce “She’s in her room, Yaya what and what did u brought for me?” ya dan zaro ido kafin ya ce “Nothing, but zan kai Ammina shopping insha Allah” Khairiyya ta washe baki ta ce “Allah Yaya” ya ce “Sure” zama yayi akan sofa yana kallan TV ya ce “Call Mami for me” ta ce “Ohk” daga haka ta nufi upstairs da gudu.
_{Anty Aisha kanwar Maman Yusuf ce wacce suke uwa daya uba daya, su kadai iyayensu suka haifa, itama a nan kano take da zama a unguwar rimi, mijinta baban lawyer ne, shi ya kai Yusuf abroad yayi karatu har ya gama, yaransu guda uku, Sameer shine babba wanda a kalla yana da shekaru 26 sai kuma Faruk me shekara 20 sai kuma autarta me sunan maman Yusuf wato *FATIMA* shekarar ta 10 kacal a duniya}_
A tare suka sakko downstairs, Khairiyya ta zauna gefen Yusuf ta ce “Yauwa Yaya ka fada ma Mami, ina da gaske kace zaka kaini shopping?” ya bata side hug ya ce “Ai dolena Ammina guda, ba shopping ba ko Kano kikace mu zagaya yau sai inda karfina ya kare” Mami dake murmushi tana kallansu ta ce “Ko idan man motarka ya kare ba?” Ya danyi murmushi yana kallanta ya ce “Ina yini Mami?” Ta ce “Lafiya kalau Yusuf ya clinic?” Ya ce “Alhamdulilah, kwana biyu banzo ba Mami aiki ya min yawa” tana murmushi ta ce “Ba komai Yusuf, Allah dai ya taimaka” ya ce “Ameen, su Sameer basa nan” Mami ta ce “Sameer ya tafi Abuja jiya, Farouk kuma ya shiga gari” ya ce “Ohk” Mami daketa kallansa tin dazun ta ce “Amma ya jikinka Yusuf? Are u getting better ko dai har yanzu gaka nan dai?” ya juyo yana kallanta ya ce “Da sauki Mami sosai” ta ce “To Allah ya kara maka lafiya, yau kuma sai gaka da wuri, ni ai da na zata zuwan yamma zaka mana” Ya gyarawa Khairiyya scarf dinta kafin ya ce “Yau Saturday ai Mami, ward rounds kawai nayi, but week days to 5 nake tashi” Mami ta ce “Masha Allah, ya batun aure fa Yusuf?” murmushi kawai yayi yana kallanta, ta ce “Ko so kake mu aura maka koma wacece? Shekarunka fa 32 yanzu” ya shafa afro din dake kansa ya ce “Mami soon insha Allah” ta ce “U are always saying soon, when is that soon Yusuf?” Ya sauke kansa kasa ya ce “Kuyi ta addu’a” ta ce “Kullum yinta muke ai, ga abinci akan dinning idan zaka ci” ya mike yana kallan Khairiyya ya ce “Muje muci tare, Mami Daddy baya nan ne?” Ta ce “Bai dawo ba, we are expecting him on Wednesday by God grace” ya ce “Allah ya dawo dashi lafiya, when will u visit me Zarah?” Ya karashe magana yana kallan Khairiyya dake zuba musu mango juice cikin glass cup, ta dago tana kallansa ta ce “Idan an bamu mid~term break zanzo Yaya” ya ce “Ohk, what was ur last position?” Ta ce “2nd, kuma Yaya Sameer yace zai siyamin tablet but har yau shiru” Yusuf yayi murmushi ya ce “May b kin masa laifi ne?” Ta ce “Noo, i just wake him up the other day, wai ashe he’s having headache, shine yaji haushina” ya ce “To kinga? Ke kika jawa kanki ai”.
Bayan sun gama cin abinci ta kama hannunsa ta ce “Yaya mu tafi ko?” ya ce “Not yet Amminah, we still have much time, sai da la’asar zamu fita” daga haka ya bata side hug suka zauna suna kallan TV.
Karfe 12 da rabi Mustapha ya dauko su Rafi’ah a islamiyya, suna shigowa gida ta ajiye side bag dinta tana kallan Ummi ta ce “I’m so tired Umminah” Ummi ta ce “Go take a shower, i think u will feel better” ta mike a hankali ta ce “Abba fa?” Ummi ta ce “Yana apartment din Antyn ku” turo baki tayi ta wuce upstairs, Tana shiga daki ta lankaye bag din sannan ta jawo towel ta shiga cire kayanta dan yin wanka, minti 10 ta dauka a toilet kafin ta fito, ta zauna gaban mirror ta fara combing kanta sannan ta shafa lotion ta mike ta saka kaya, riga da skirt na atampa tasa, dinkin ya zauna mata das das, ta daura dankwalinta sannan ta sauko downstairs, direct kan dinning ta nufa ta fara cin abinci, after all ta dawo gefen Ummi tana taya ta recording marks.
karfe 2 da rabi Abba ya shigo parlon da sallama, Rafi’ah ta dago kanta tana amsa sallamarsa ta ce “You’re welcome Abba” ya ce “Zo nan Rafi’ah” ta dan zaro ido tana kallansa, dan duk sanda ya kirata haka tasan akwai babban laifin data aikata, ta karaso gefensa a hankali ta ce “Gani” ya ce “Sit down” ta zauna kanta a kasa, sai lokacin Ummi ta dago kanta ta kallesu, Abba ya ajiye wayarsa ya ce “What did i told u in the morning before u left for Islamiyya?” Taso tayi pretending like she didn’t recall amma ganin reaction din Abban nata yasa ta ce “Kace naje na gaishe da Anty” ya ce “And why didn’t u go?” Ta kara sauke kanta kasa tana wasa da azurfan hannunta, ya ce “I’m i not talking to u” a hankali ta ce “Nothing” ya ce “Saboda ban isa na sakaki ba ko kuma bata kai kije ki gaisheta ba” girgiza masa kai ta hauyi a hankali, ya ce “To tashi kije ki gaisheta, and never let this kind of foolishness happens again, i can’t tolerate, idan kin dawo kizo kuma ki dauka veil dinki zaki rakata shopping” kamar zatai kuka ta mike a hankali ta fita a parlor, kamar me counting steps dinta take tafiya harta isa apartment din, ta murda handle din sannan ta shiga parlorn da sallama, ko amsa sallamarta batai ba ballantana ta amsa gaisuwar data mata, Rafi’ah ta juya ta fice a parlorn, haushi duk ya cikata, tana shiga parlornsu Abba ya ce “Kije kuma ki rakata shopping now” ta kara turo baki ta wuce upstairs tana bubbuga kafa, tana shiga dakinta ta fashe da kuka ta jawo wayarta tayi dialing phone din Mummy, bugu biyu ta dauka tana “Yau an tinoni kenan?” Jin kamar kuka yasa ta ce “Subhanallah, are u crying Rafi’ah?” Cikin kuka ta ce “Koba Anty Amina bace” Mummy ta ce “Menene kuma ya faru? Tazo ne?” Hawayenta ta share kafin ta ce “Jiya sunzo da Abba, kinga yanzu ya gama min fada wai banje na gaisheta ba, danaje kuma na gaisheta tana kallona taki amsawa, wai kuma Abba yace saina rakata shopping, gaskiya ni i can’t, i so much dislike her Mummy, kinga fa ita bata zo ta gaishe da Umminmu ba amma Abba yake tilastamu mugaisheta” Anty Halima ta sauke ajiyar zuciya ta ce “Wipe your tears, ina dalili zaki dinga kuka akan kishiyar uwarki, ki barta caan da mungun halinta, tinda Abbanki ne yayi magana ki rakata, amma idan ta miki ki mata kema, ban yarda ki raga mata ba wallahi, duk wannan asarancin na Zainab ne, ita dan fadan nan ma na mata bata iya ba, wallahi ban yarda kiyo halinta ba, ina dalili keda gidan ubanki a dinga takura miki” Rafi’ah ta turo baki ta ce “Ni banma san dalilin da zaisa na raka taba” Mummy ta ce “Makirci ne irinna mata, ki dai kula da duk wani takunta, aniyarta ta bita caan, kuma koda wasa karki daukar mata kaya ai ke ba ‘yar aikinta bace, idan na dawo ma kika koma gidana kikai auranki ina zata ganki” Rafi’ah tayi saurin hanging call din ta tashi ta fito a dakin, da Ummi taci karo zata shiga dakinta, ta 6ata rai ta ce “Ummi kinji wai sai in rakata shopping” Ummi ta ce “And so? Wani abu ne zai ragu ajikinki ko me? wallahi da nasan bakije kin gaisheta ba da sai ranki ya 6aci a gidan nan, ina zaman zamana kin jawomin magana yana fadin ninake kyaleki, saime idan kin gaisheta” ta ce “Ummi to ita gaisheki take?” Ummi ta daka mata tsawa ta ce “Kindly disappear here, wallahi zan 6ata maki rai Rafi’ah” barin wajen tayi hawaye na zuba mata. Bayan ta sauko ta wuce Abba dake zaune a parlor ta fita compound din gidan, ta karasa parking lot ta jingina da mota ta wani hade rai. Kusan ten minutes tana tsaye kafin ta fito walking slowly tana ta chewing gum, an sha kwalliya kai kace gidan biki zata, Mustpha yayi saurin bude mata back seat jikinsa na rawa, bayan ta shiga ta ce masa “Ka cewa wannan yarinyar ubanta baice mata tare zamu tafi bane?” Rafi’ah ta dago kanta da sauri jin abinda tace, ta kara folding hannayenta tana tsaye jikin motar Abba, Mustapha ya karasa kusanta a hankali ya ce “Hajiya karama ke ake jira” ta dalla masa harara ta juya kai gefe, Abba ta hango ya fito da waya kare a kunnensa yana answering call, hakan yasa tayi saurin shiga motar tana ta turo baki Mustapha yaja suka wuce.
Tafiyar minti 20 sukayi kafin suka iso shopright, bayan Mustapha yayi parking suka sauka suka karasa ciki, ita dai Rafi’ah sai binta take tana dalla mata harara ta gefen ido, almost 1 hour suna zagaye amma abu guda 4 kawai ta dauka, kuma ita da kanta ta rike basket dinta, ta dan saci kallan Rafi’ah ta ta6e baki ciki ciki ta ce “Sai kin gaji da yawo yau munafuka” suna tsaye a wani waje wani dan saurayi yazo wucewa, ya danyi murmushi kafin ya ce “Excuse pls Madam” Anty Amina ta matsa tana binsa kallo ya shige, juyowa yayi ya kalli Rafi’ah sannan ya kara kallanta, hade ran da tayi yasa ya juya ya tafi abinsa dan da niyyarsa ya mata magana.
suna tsaye awajen sukaji ance “Fatima” Rafi’ah tayi saurin juyowa tana murmushi, wara manyan idanuwanta tayi ta ce “Doctor” yana rike da hannun Khairiyya ya karasa gabanta ya ce “How are u?” Ta ce “Fine, is this your sister?” Ya danyi murmushi yana kallan Khairiyya ya ce “Yes, she is” Khairiyya dake rike da Baby doll dinta ta ce “Good Afternoon” Rafi’ah ta shafa kanta ta ce “How are u little girl? U are so cute” Yusuf ya cusa dayan hannunsa a pocket dinsa as usual ya ce “Thank u, are u leaving now?” Ta girgiza kai ta ce “Actually no, and i came with driver” ya ce “Alright, that’s good” sai lokacin idansa ya sauka akan Anty Amina dake gefen Rafi’ah tana rike da basket, tin zuwansa ta kura masa ido ko kiftawa babu, kallan Rafi’ah yayi a hankali ya ce “Are u together with her? I mean the lady besides u” Rafi’ah ta daga masa kai ta ce “Yess, my housemaid” jin haka yasa Anty Amina ta gwalalo ido tana kallan Rafi’ah ta ce “I don’t understand, who’s your housemaid here?” Ta kallai Yusuf sannan ta kalli Anty Amina ta ce “Let’s move from here pls” Yusuf ya dan matsa gefe sannan tabi bayansa itama, sororo Anty Amina tayi tana kallan Rafi’ah, daga haka ta cije baki ta saki basket fin hannunta fuuuu ta bar wajen cikin sauri. Dariya sosai Rafi’ah ta kyalkyale dashi harda kama ciki, sai yanzu abinda ta fada yayi mungun bata dariya, Tsayawa kawai Yusuf yayi yana kallanta with confusion, ta kai minti 5 tana ta kyalkyala dariya kafin ta kalli Yusuf ta ce “Anywhere thank u much” ya danyi shiru sannan ya ce “Are u sure she’s your housemaid?” Ta ce “Of course, kasan idan suka waye sai a hankali, wai yanzu fishi tamin, dama tana ta rokona kar watarana na copsa mata”, Yusuf yayi murmushi ya ce “And u did?” Sake dariya tayi ta ce “Why will i not Doctor” ya sauke ajiyar zuciya yana kallanta,
Sweet da chocolate ta kwasarwa Khairiyya ta biya kudin sannan suka fito, sai bayan sun fita ta mika mata ledan ta ce “This is yours little Baby?” Khairiyya ta kalli Yusuf sannan ta kar6a ta ce “Thank u” Rafi’ah ta kama hannunta ta ce “What’s your name?” A hankali ta ce “Fatima Khairiyya” Rafi’ah ta dan wara ido looking smiley ta ce “Woow ashe namesake dina ne” dai dai lokacin ta kalli inda sukai parking taga ba motarsu a wajen, Yusuf dake kallanta ya ce “Where are they?” Ta ce “May b they’ve gone” ya ce “Ohk, let me drop u home” tabi bayansa har suka isa inda motarsa take, back seat ya budewa Khairiyya bayan ta shiga ya budewa Rafi’ah front seat ta shiga sannan ya zagaya seat dinsa ya sawa motar key, suna hawa saman titi ya kalli Rafi’ah dake murmushi ya ce “Who’s she? I mean the woman?” Ya kara tambaya for d second time, silently ta ce “Stepmother” tana rife bakinta ta sheke da dariya tana kai kanta kan cinyoyinta, surprisingly enough Yusuf yake kallanta ya ce “Do u mean your Daddy’s wife?” Ta daga masa kai still laughing ta ce “Nima ramawa nayi, haka kawai ta fito dani just to make me angry, munkai awa muna zagaye amma wadannan abin daka gani a basket su kadai ta dauka” ta kara turo baki ta ce “Ai dani take wallahi” Yusuf couldn’t hold his laugh, yayi dariya kafin ya ce “Zaki sha fada wajen Daddy ai” ta ce “Ba fada ba? Aini ba yanzu na saba jin fada ba” yayi nodding kansa ya ce “Kin saba kenan?” Ta ce “Noo” ya sake kallanta ya ce “Since from the first day i saw u nayi noticing u are stubborn” ta danyi murmushi ta ce “And it isn’t true, ina rama abinda akamin ne kawai that’s all” ya maida hankalinsa ga tuki ya ce “Wane area kike?” Ta ce “Hotoro GRA” daga haka ta fada mishi house number din.
Anty Amina na komawa gida apartment dinta ta nufa ta kasa zaune ta kasa tsaye, ita abinda Rafi’ah ta fada bai dameta sosai ba kamar kamannin Yusuf, tabbas bazata ta6a mantawa dashi a rayuwa ba, amma da dukkan alamu bai gane taba, a hankali ta ce “Kaddai saurayin Rafi’ah ne?” Daga haka ta lalibo wayarta cikin hand bag dinta ta fara neman phone din Abba. Bugu daya ya dauka ya ce “I will call u ltr i’m busy now” daga haka yayi hanging call din, a bakin titi Rafi’ah tace Yusuf ya ajiyeta, tayi masa godiya sannan ta shafa kan Khairiyya ta ce “Bye little girl” Khairiyya ta daga mata hannu sannan ta juyo tana kallan Yusuf ta ce “My house isn’t far from here, so nagode sosai” ya danyi murmushi ya ce “Mention not” daga haka ta shiga cikin layin walking very slowly tana auno fadan da Abba zai mata, tasan duka kam is impossible tinda ba ta6a mata yayi ba. Cikin sauri Anty Khadija taja birki ganin Rafi’ah, if she could recall itace yarinyar da Yusuf ya kai mata office dinta, kafin tayi parking ta fito tuni Rafi’ah ta tura gate ta shige gida, ta dinga kallan dankareren gidan kafin taja motarta tayi gaba, motar Yusuf ta gani akan junction ya tsaya suna gaisawa da wani, lokaci daya jikinta ya bata cewar shi ya ajiye Rafi’ah yanzu, ganin yadda yake ta fara’ah suna gaisawa da mutumin ya tabbatar mata da cewa Yusuf yana cikin farinciki, abinda ta tsana ta ganshi a ciki kenan, tayi mungun tsanar ta ganshi yana murmushi, taja wani dogon tsaki sannan taja motarta ta tafi a wajen ta ce “Ba dai naga gidansu ba, muje dai zua” daga haka ta kara speed din motarta tayi hanyar gida.

_SHARIK~HAYATI_

*Remember update is 2 days per week, And the page is dedicated to my luvly, sweet, mint, bread, sugar, honey 馃檮 what again? Time bom, big bom 馃槀 My ILHAM 馃А stay blessed Jiddah ta*
[6/9, 11:00 AM] Teemarh: *_…卮乇賷賰 丨賷丕鬲賷…_*
_{MY LIFE PARTNER}_

*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
銆帮笍銆帮笍銆帮笍銆帮笍銆帮笍銆帮笍銆帮笍銆帮笍銆帮笍銆帮笍
_We are here to Educate, Motivate and Entertain our Readers_
銆帮笍銆帮笍銆帮笍銆帮笍銆帮笍銆帮笍銆帮笍銆帮笍銆帮笍銆帮笍

*BY FATIMA* _{Real~Teemarh}_

_13~14_

Cikin quick light steps ta shigo compound din nasu, ta dan kalli apartment din Anty Amina sannan ta ta6e cute mouth dinta ta nufi entrance din gidan, Ummi ce kadai zaune a parlo tana kallo, Rafi’ah ta saukar da kanta ganin irin kallan da Ummi ke mata, ji tayi ta ce “Where are u from?” Wani katan abu daya tsaya mata a wuya ta hadiye kafin ta ce “Shopright” Ummi ta dinga kallanta sannan ta ce “And why did u came back alone? didn’t u know that they spent more than 20 minutes before u came in” a hankali ta ce “Naje daukan perfumes ne, so kafin na dawo na samu sun taho” Ummi ta ta6e baki ta ce “Is ok” daga Rafi’ah ta wuce upstairs da fargaban abinda zai faru idan har Abba yaji tacewa Antinsu mai aiki ce. Direct dakinta ta shiga ta kwanta akan bed tana sauke ajiyar zuciya, calmly ta danne side din da zuciyarta yake saboda heartburn data faraji, ta limshe idanuwanta to make sure it’s not taking long, ji tayi kamar an kara mata wanda takeji akan da, ta fashe da matsanaicin kuka tana kwalawa Ummi kira, juyi ta farayi tana yarfe hannu, dayan hannunta kuma yana kan heart dinta dake mata zafi kamar zata fasa kirjin ta fito. Tin tana hawaye harta dawo she’s crying loud calling Ummi and Abdul. Ummi na zaune a parlo taji kawai she’s not comfortable with her daughter’s absence, tasan the next abu da zatai to bacci ne, hakan yasa ta mike ta nufi upstairs, Immidiately tana gama hawa Rafi’ah ta saki wani irin kara hade da kiran Abba, Ummi ta bude dakin da saurin tayi kanta tana salati, dagota tayi jikinta tana kallan idanta dake limshe ta ce “Rafi’ah!” tana bude idanuwanta hawaye suka shiga gangaro mata, a hankali ta dago hannun Ummi ta dora akan chest dinta ta ce “It’s hurting me Ummi” daga ta tayi kamar baby girl ta rungumeta suka fito a dakin, suna fitowa sai ga Abba da hawowansa kenan yana waya, cikin tashin hankali ya ajiye wayar akan sofa yana furta “Subhanallah” daga haka ya kar6eta in a hurry ya fara sakkowa steps da ita, komawa daki Ummi tayi ta dauko hijab dinta sannan ta sakko. Ko kafin ta fito har Abba yasa Rafi’ah a mota, bayan Ummi ta shiga yaja motar suka fita a gidan zua Clinic din da suke zuwa. Suna isa cikin gaggawa aka turo bed aka daurata akai sannan aka wuce da ita ciki.
Dr. Saleem, Dr. Aryan da kuma wasu turawa biyu ne a kanta to make sure they give her quick assistance, Aspirin doctor Aryan ya saka mata a baki, as usual ta fara chewing a hankali harta hadiye sannan aka bata nitroglycerin ta sha, after then aka mata injection din papaverine to reduce the pain and discomfort beyond her chest to orther part of her upper body, few minutes da mata alluran ta samu tayi bacci, Dr. Aryan ya kalli sauran doctors din dake kanta ya ce “I think it’s successful” wani bature a cikinsu ya ce “By God grace” daga haka suka fita gaba dayansu suka jawo kofar to let her rest. Suna fitowa Abba ya karasa wajensu ya ce “How is she Doctor?” Doctor Aryan ya cire hand gloves din hannunsa yana kallan Abba ya ce “It was successful, insha Allah within 1 hour zata tashi” Abba ya sauke ajiyar zuciya ya ce “Thank u” daga haka ya koma inda Ummi ke zaune, daka ganta kasan tana cikin tashin hankali, Abba ya kamo hannunta yana massaging just to make her calm ya ce “Relax please, kiyi ta mata addu’a” ta goge dan hawayen dake makale a idanta ta ce “I don’t want to loose Rafi’ah Yallaboi” ta karashe maganar cike da damuwa, Abba ya ce”The best thing is du’ah Ummu Rafi’ah, u know God plan the best, it is a test from God, kuma ina fatan zamuci wannan jarabawa insha Allah” a hankali Ummi ta ce “Allah yasa”.
Anty Amina ce zaune a parlorn ta tana shan fresh yoghurt sai yayarta dake zaune a gefenta tana sauraronta, bayan ta dasa aya matar ta zaro ido hade da kundumo ashar ta ce “Baki fasawa yarinya baki ba? Ita har tana da bakin da zata kiraki da ‘yar aiki? Wallahi tallahi Amina kinyi asara, ko uwarsu ce ta fada miki haka bakya tsigale taba ballanta wannan taniniyar yarinyar” Anty Amina ta ajiye glass cup din hannunta ta ce “Nifa Anty Rahama wani abun mamaki na gani that’s why i totally forgot her speech, nifa tsohon saurayin Nusaiba na gani ya mata magana” Anty Rahama ta ce “Wacece Nusaiba?” Gyara zama Anty Amina tayi ta ce “Kawata da muka gama karatu tare, wallahi tana sanshi yana santa ingaya maki wata ‘yar uwarsa ta shiga tsakani suka rabu, ni kuma dama fa.. Tin kafin nayi aure kyau yakemin, fatana dai ba saurayinta bane, wallahi Anty Rahama bakiga kyansa ba, kamar shi yayi kans… ” tsawa Anty Rahama ta daka ta ce “Lallai Amina na yarda kin fara hauka, ina ruwanki da wani saurayi caan da mijinki” ta 6ata rai ta ce “Anty Rahama hauka kuma?” Ta ce “Hauka mana Amina, da kinsan irin tuggun da muka hada nida Umma akan Ya Muhammad ya aureki da baki fadi haka ba, ina gashi muna ‘yan wansa na jini amma akace ya nemeni yaki, haka na hakura nayi wannan tsinannen auren da babu komai a cikinsa sai wahala, me za’ai da talauci Allah na tuba” Anty Amina sai kallanta take bata ce komai ba, Hakan yasa Anty Rahama ta kamo hannunta ta ce “Ko kin manta da Ummanmu da mahaifinsa uba daya suke, to haka mukaita kai kawo kauyen Masko har Allah yasa da kansa yaje ya sami Gwaggo Allah ya jikan rai yace yana sanki da aure, ke wahalar da muka sha wallahi bazai misaltu ba, amma gaki shekara 3 har yanzu ko 6ari baki ta6a yi ba” Anty Amina ta ta6e baki ta ce “To Anty kikasan ko shine baya ai… ” katseta Anty Rahama tayi ta hanyar cewa “Kuul dama!!! da baya aihuwa ya haifi Rafi’ah da Abduljalal? Ki dai zauna dai, kina gani duk dukiyar nan su kwashe su barki da dan karamin fili” Anty Amina ta mike ta ce “To ai haihuwar ta Allah ce, duk magungunan da kike kawomin ina sha amma shiru har yanzu” Anty Rahama ta ce “Maza bani abinda zan samu in wuce na bar Umma ita kadai Ikleemah ta fice” daki Anty Amina ta shiga ba jimawa ta fito da sarkan gold ta mikawa Anty Rahama ta ce “Ga dai wannan” Anty Rahama ta washe baki ta ce “To barka, sai a siyar aci gaba da nema maki maganin haihuwa, ina dalili shekara 3 fa kenan babu labari” daga haka tayi kasa kasa da murya ta ce “Ni inaga ma wannan kishiyar taki ce tasa miki hannu, dan taga dake ake tafiya Abuja a barta a Kano” Anty Amina ta ce “Nima dai abinda nace kenan, amma koma menene yazo karshe” Anty Rahama ta nufi kofar fita ta ce “Muna nan dake zakiji labari, to nidai na tafi” Anty Amina ta daga mata hannu ta ce “To sai anjima” daga haka Anty Rahama ta fita ita kuma ta dawo ciki.
kwance take jikin Ummi tana ta faman sauke ajiyar zuciya, Ummi ta kamo hannunta tana kallan idanta ta ce “How are u daughter?” A hankali ta ce “Da sauki” Ummi ta gyara mata scarf din kanta ta ce “Allah ya baki lafiya”, bude kofar dakin akai Abba ya shigo Abdul na biye dashi, suka karasa kan gadon suna kallanta cike da tausayi, jikinta Abba ya ta6a ya ce “Mamana, ina ke maki ciwo yanzu?” Silently ta ce “My chest Abba, amma kadan kadan yake” Abba ya durkusa dai dai fukarta ya ce “Soon zai daina Mamana, zanje gida na dawo me zan kawo maki?” Ta danyi smiling sannan ta ce “Shawarma Abba” ya shafa kanta ya ce “To Insha Allah” Abdul ya kamo hannunta na hagu yana kallanta ya ce “Get well soon Anty, Allah ya baki lpy me daurewa” kallansa tayi trying hard to control herself ta ce “Thank u love” limshe idanuwanta tayi dan ita kadai tasan abinda takeji deep down, damma da aka mata alluran ya rage mata radadi da ciwo, Abba ya kalli Ummi ya ce “Lie her down and pray Madam, after then itama tayi sallah tayi addu’a sosai kinji Mamana?” Kai ta gyada masa ta ce “To” Ummi ta kwantar da ita ta ce “Allah ya kiyaye, amma Abdul kar ya dawo ya zauna kawai tinda kaima komawa zakayi ai” Abba ya ce “Me zai hana muzo tare mu koma, ai shima yanaso yaga condition dinta” Ummi ta ce “To sai kun dawo” daga haka suka fita ita kuma ta shiga toilet danyin alwala. Yusuf ne zaune a office din Dr. Aryan, bayan ya mishi bayanin abinda ya kawo shi Dr. Aryan ya ce “Allah ya sauwake” daga haka ya kira Dr. Hisham ya sanar masa yadda sukai, on the other side Doctor yace ya kar6a test din nasa sannan ya rubuta masa sabbin magani, after yayi hanging wayar ya kalli Yusuf sannan ya ce “Let me have the test” Yusuf ya mika masa test din, bayan ya duba ya ce “Allah ya sauwke, bari nayi ma wata patient injection idan na dawo saina rubuta maka drugs din, nasan by now she’s awake” Dr. Aryan ya karashe maganar yana kallan agogon dake manne a bangon office din, mikewa Yusuf yayi dan sauri yake ya wuce gida, gaba daya he looks so tired, Dr. Aryan ya ce “Can’t u wait?” Yusuf ya ce “Let me have the injection saina mata i’m also a medical doctor” daga haka ya ciro ID card dinsa ya mikawa Dr. Aryan, kar6a yayi yaga sunansa, asibitin da yake aiki da year din daya fara aiki sai field dinsa daga karshe, murmushi Dr yayi ya ce “Masha Allah, ashe ina tare da babban likita ne, nice to meet u Yusuf” daga haka ya mika masa allurar Yusuf ya fara hadawa, Dr. Aryan ya kalleshi still smiling ya ce “Me yasa amma baka za6i field din cardiologist ba {Likitan Zuciya}, kodan ciwanka ma?” Yusuf yayi murmushi ya ce “Not interested, and self medication is not allowed” Dr ya ce “Kuma hakane, Allah ya sauwake, let me get the drugs for u, room dinta shine na kan corner, probably room 4” Yusuf ya ce “Ohk” daga haka yaci gaba da hada alluran. Ummi na fitowa a toilet ta kalli Rafi’ah data juya baya sannan ta dauki sallaya tayi hanyar fita, a hankali Rafi’ah ta ce “Ummi ina zakije” tsayawa Ummi tayi ta juyo tana kallanta ta ce “I want to pray outside Rafi’ah, ina nan corridor ko kinasan wani abu?” Girgiza kanta ta hauyi ta ce “No” daga haka ta limshe idanuwanta Ummi kuma ta fita.
Yusuf na gama hada alluran ya fito a office din Dr. Aryan sannan ya nufi room din da Rafi’ah take, da sallama ya shiga room din ya karasa kan gadon, tana kwance ta juya bayanta idanta a limshe, ya karasa dab da ita ya leka fuskarta, zaro ido ya danyi yana kallanta surprisingly enough, jin kamar motsi a bayanta yasa ta bude idanuwanta ta juyo a hankali, ta zaro ido silently ta ce “who i’m i seeing?” Zama yayi a gefenta ya ce “How are u now?” Ta ce “Much better, how did u know i’m here?” Ya danyi murmushi ya ce “My heart told me u are here” ta saki murmushi me kyau ta ce”It’s impossible” ya ce “Bakisan idan zuciya na san ganin abu tana searching ta gano in yake ba?” Ta danyi dariyar daya bayyana with teeth dinta kafin ta ce “So ita ta kawo ka kenan?” Ya ce “Sure! Yaushe kika samu attack” ta fara wasa da fingers dinta ta ce “Immediately i entered my house, so i slept to rest, kawai kuma sai na farajin somehow heartburn” Yusuf dake kallanta tin tini ya ce “Allah ya kara maki lpy, are u sure u are taking ur drugs?” Ta daga masa kai ta ce “Ina sha” daga haka ya mike ya ce “I’m giving u an injection now” ta dan matso bakin gadon ta mika masa hannunta, daga hannun rigar yayi yana kallanta ya ce”Kina tsoron Allaura ne?” Ta danyi smiling ta ce “Not that much, amma fa kar kamin da zafi” yana ta dariya ya goge wajen da spirit sannan ya caka alluran, ya dinga kallan fuskarta to see her reaction, sai ma yaga batai wani raki ba, cotton wool ya saka mata a wajen sannan ya ce “Sorry, insha Allah da safe zan shigo na gaisheki” ta ce “Ohk, thank u” ya daga mata hannu ya nufi hanyar fita, kafin ya bude kofar Ummi ta bude ta shigo, ya danyi kasa da kansa with full of respect ya ce “Ina yini Umma” Ummi ta ce “Lafiya kalau” daga haka ya fita a dakin ita kuma ta shigo tana kallan Rafi’ah da har ta sake kwanciya ta ce “Magani aka baki ne?” Ta girgiza kai ta ce “Injection” Ummi ta ce “Tashi kiyi sallah sai na hada maki tea ki sha” daga haka Ummi ta daga ta suka shiga toilet.
Da sallama Abba ya shigo parlorn yana kallan Anty Amina dake zaune, ta amsa masa sallamar ranta babu dadi sannan ta ce “Inata kiran wayarka baka picking” Abba ya zauna yana kallanta ya ce “The phone isn’t with me, Rafi’ah ba lafiya anyi admitting dinta dazu, so gobe da safe kije ki duba ta” ta dan hade rai ta ce “Zanje gida fa, banje na gaishe da Umma ba, kuma dama akwai abinda tamin inaso kaja mata kunne” Abba ya dago yana kallanta ya ce “But nace maki tana asibiti ko? And goben make sure kinyi branching kin gaisheta” bata ce komai ba ta wuce kitchen ta dauko masa ruwa da cup ta ajiye a gabansa sannan ta koma daki ya bita da kallo ganin fuskarta kamar an kunna wuta. Washegari wajajen karfe goma Anty Amina tazo asibiti, duk ranta a 6ace yake dama ba dan Abba ba da ba zuwa za tayi ba, a hankali ta bude kofar ta shiga ko sallama babu, kan kujera ta zauna tana kallan Ummi ciki ciki ta ce “Ina kwana” Ummi dake hadawa Rafi’ah tea ta ce “Lafiya” Anty Amina ta ce “Ya mai jiki” Ummi ta ce “She’s getting better”, bude kofar toilet Rafi’ah tayi ta fito, towel kadai ne a jikinta ta karaso ta zauna akan gado tana turo baki, ganin hararan da Ummi ke mata yasa ta danyi kasa da murya ta ce “Good morning” Anty Amina ta mike tana kallan Ummi ta ce “Sai anjima” daga haka ta bude kofar ta fita. Verseline Rafi’ah ta shafa sannan tasa riga da wando ta koma kan gadon ta kwanta, tinaninta Ummi zatai mata fada amma kuma sai taga akasin haka, Ummi ta mika mata tiree me dauke da tea sai bread da chips a gefe ta ce “Tashi kici abinci” Mikewa Rafi’ah tayi ta kar6a tiree din sannan ta faracin abincin, few minutes ta gama ci ta ajiye sannan ta goge hannunta da tissue ta kwanta, waya Ummi ta mika mata ta ce “Ga Anty Halima, jiya ta kira kinyi bacci” kar6an wayar tayi ta kara a kunne ta ce “Mummy” from the orther side Mummy ta ce “Daughter how are u?” a hankali ta ce “Da sauki sosai” Mummy ta ce “To adai dinga kiyayewa, ni dama hankalina bai kwanta ba da kikace zaki raka waccen matar shopping, wallahi badan kar Muhammad yace ina shiga hurumin gidansa ba da babu inda zaki, muka sani ma ko ita ta jawo miki ciwan ya tashi” dariya Rafi’ah tayi ta ce “Sai bayan fa mun dawo Mummy” taja tsaki ta ce “Ke dai kibar mace Rafi’ah, mata akan kishi babu abinda basayi, bari dai na dawo kasar fuskarki ma ba zata gani ba” Rafi’ah ta ce “To Allah ya kaimu” ta ce “Ameen” daga haka ta mikawa Ummi wayar. Bude kofar dakin akayi Yusuf ya shigo da sallama, Ummi ta amsa tana kallansa, ya karaso ciki ya dan tsuguna ya ce “Ina kwana Umma” ta ce “Lafiya kalau” ya ce “Ya mai jiki?” Ta ce “Da sauki, sai godiya” daga haka ya ajiye babban bakin ledan dake hannunsa ya dan kalli Rafi’ah data takure waje daya ya ce “How are u feeling?” A hankali ta sunkuyar da kanta ta ce “Da sauki” daga haka Yusuf ya juya ya ce “Allah ya sauwake, sai anjima” Ummi ta ce “To mungode Allah ya saka” daga haka ya fita ya rife kofar. Ummi ta kalli Rafi’ah ta ce “Who is he?” Dago kanta tayi ta ce “Doctor ne, shine ai wanda yamin injection jiya da daddare” Ummi bata sake cewa komai ba ta nemi waje ta zauna, Gwalalo ido Anty Khadija tayi ta ce “Yusuf nake gani a nan? Naga jiya yace yazo ya kar6i magani, in fact ai ba nan ake zuwa ba” ta wuce Nurse din da suke magana tare tabi bayan Yusuf, cikin few minutes ta karaso shi ta ce “Malam meya kawoka nan? Meyasa bakaje aiki ba?” Yusuf ya juyo yana kallanta ya ce “Nazo na duba abokina ne baiji dadi ba” Anty Khadija ta ce “To bari naje na ganshi, kaga ai zaiji dadi” daga haka ta nufi room din da Rafi’ah take, cikin sauri ya tare ta ya ce “Aiba dole saikin je ba, baima sanki bafa” Anty Khadija ta tsaya tana kallansa, ta karasa bakin kofar da sauri tasa hannunta akan handle din kofar zata bude Yusuf yayi saurin janye hannunta ya ce “Why won’t u mind ur own business? Nace maki baima sanki ba”.

*SHARIK HAYATI*

Dedicated to Maryam Shehu 馃А

_08103810398_
[6/9, 11:00 AM] Teemarh: *_…卮乇賷賰 丨賷丕鬲賷…_*
_{MY LIFE PARTNER}_

*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
銆帮笍銆帮笍銆帮笍銆帮笍銆帮笍銆帮笍銆帮笍銆帮笍銆帮笍銆帮笍
_We are here to Educate, Motivate and Entertain our Readers_
銆帮笍銆帮笍銆帮笍銆帮笍銆帮笍銆帮笍銆帮笍銆帮笍銆帮笍銆帮笍

*BY FATIMA* _{Real~Teemarh}_

_15~16_

Kiran da CMD yayi wa Anty Khadija yasa ta juya tana hararan Yusuf ta bar wajen, sanyayyar ajiyar zuciya ya sauke hade da limshe ido sannan ya juya ya fita shima, direct parking space ya nufa ya shiga motarsa ya bar clinic din. Misalin karfe 5 na yamma akai discharging din su Rafi’ah, bayan an gama kai komai mota Abba ya shafa kanta looking into her eyes ya ce “Sannu Mamana, i hope u are not feeling any pain?” Ta daga masa kai tana gyara wuyan hijabinta ta ce “Ehh Abba” ya kalli Ummi dake nade bedsheet din kan gadon ya ce “Let’s go Madam” ta ce “Ina fitowa yanzu, akwai sponge dinta a toilet da sauran abubuwa zan dauko” Abba ya kama hannun Rafi’ah suka fita a dakin, sai sannu yake mata har suka isa mota, ya zaunarta a back seat ya durkusa daidai fuskarta yana murmushi ya ce “What do u want to eat?” Ta mayar masa da murmushi ta ce “Nothing Abba” ya shafa fuskarta ya ce “In siya maki Shawarma, i know u like it” ta zaro ido tana dariya ta ce “Abba bayan a asibiti shawarma nayi ta ci, nidai a’a banaso” ya ce “To me kikeso?” Ta ce “Dan~wake, nasan Ummi zata dafamin idan muka koma” Abba ya zaro phone dinsa a aljihu ya ce “Let your stepmother cook, kinga muna zuwa idan kikai wanka sai kici” ita dai murmushi kawai tayi tana kallan Abbannata, yana fada mata bai jira cewarta ba ya kashe wayarsa, Ummi na karasowa ta shiga front seat Abba ya zagaya mazauninsa yaja motar suka tafi. Cikin 15 minutes suka isa gida, Mustapha ya bude gate suka shigo, bayan Abba yayi parking ya fito yana kallan Rafi’ah dake kokarin bude kofa ya ce “Let me get the food for u” ta daga masa kai tana satan kallan Ummi, suna hada ido tayi saurin sunkuyar da kanta, Ummi dake kallanta ta ce “Which food?” Rafi’ah ta rife kofar motar ta ce “Dama Abba ne yace wai tamin dan wake” Ummi ta ta6e baki ta nufi entrance din gidan, tana danna bell Abdul ya bude yana mata sannu da dawowa, daga haka ya wuce ta ya rungume Rafi’ah yana patting bayanta ya ce “Welcome home dear” ta shafa bayansa itama ta ce “Thank u bro” daga haka ya kama hannunta suka shiga ciki, suna shiga ta kwanta kan sofa tana limshe ido, Ummi ta ce “Get up Rafi’ah” ta dan turo baki ta ce “I just want to rest Ummi i’m not sleeping” Ummi ta ce “Won’t u bath?” ta ce “Ba yanzu ba” Ummi ta dagata ta ce “Tashi kije kiyi wanka” tashi tayi dan ba yadda zatai ta wuce upstairs. Cikin fishi Abba ya shigo farlon ya zauna, kana kallansa kasan ransa a 6ace yake, kallan direction din inda yaji footsteps yayi, Ummi ta ajiye flask din hannunta akan dinning ta ce “What are u taking for dinner?” Abba ya girgiza kai ya ce “Ki hadawa Mamana abinda tace tana so, i think tea is ok for me” ba tare da Ummi ta kalleshi ba ta ce “Dama ban jira tamin ba ai, na riga na gama komai ruwa kawai nake jira ya tafasa” Abba ya juyo yana kallanta, ganin ta koma kitchen yasa ya mike ya nufi mosque danyin sallan magrib, ba jimawa Rafi’ah ta sauko cikin sleeping dress dinta iya knees, Ummi ta juyo tana kallanta ta ce “Have u pray?” Ta ce “Yes” Ummi ta ce “Abincin yana kan dinning, and after all ki tabbar kinyi combing gashinki” Rafi’ah ta shafa gashinta dake daure da ribbon tana kallan Ummi ta ce “Dan Allah kimin” Ummi ta dalla mata harara ba tare da tace komai ba. Anty Khadija ce zaune gaban Umma tana mata bayanin inda taga Yusuf, Umma ta numfasa ta ce “To ke a ganinki wajenwa yaje?” Anty Khadijah ta ta6e baki ta ce “Ina xan sani Umma, ai badan CMD ya kirani ba wallahi saina shiga dakin, kuma abin haushi dana gama aiki naje room din na samu ba kowa ciki” Umma na jijjiga kafarta dake kan kujera ta ce “Bari dai yazo, nasan maganinsa kuma” tana rife baki sai gashi ya shigo da sallama, duk cikinsu babu wanda ya amsa, Anty Khadija ta wani hade rai ta juya kai gefe, a hankali ya karaso cikin parlorn ya zauna kan sofa ya ce “Sannu da gida Umma” sai a sannan ta kalleshi ta ce “Ai da wucewarka kayi Yusuf, how many times kake diban kafafuwanka kabar gidan nan ba tare da kaje ka gaisheni ba, sai yanzu zaka wani zubamin jaar fuskarka kacemin sannu da gida, gadin gidan nakeyi?” Tinda ta fara magana kansa na kasa, sai da yaji ta dasa aya ya dan dago kansa ya ce “I’m sorry, almost sometimes banasan naje kina bacci ne na tasheki shiyasa, amma insha Allah bazan kara ba i apologize” Umma taci gaba da taunar chewing gum dinta ta ce “Inaso kuma ka fara hada lefe, saika turomin kudi ta account dina” Cikin sauri ya dago kansa yana kallanta ya ce “Lefe kuma Umma, ni ban tsayar da matar aure ba har yanzu” Umma ta dalla masa harara ta ce “Jiddan uban waye yace yana santa?” Yusuf ya gyara hulan kansa ya ce “It’s before Umma, but ni yanzu bani da ra’ayin aurenta, sabida she isn’t my type” Anty Khadija ta juyo tana kallansa ta ce “Kama samu zata aureka kenan? Kai har kanada hurumin za6ar matar aure, kaida kake fama da ciwon zuciya mutuwa ko yau ko gobe” nunata Yusuf yayi da yatsa ya ce “Enough Khadijah, don’t let me show u d bad side of me, i Yusuf don’t fight, but idan kika kara shiga rayuwata i swear to almighty Allah u will regret” daga haka ya kalli Umma ya ce “Saida safe Umma” Umma data hangame baki tana kallansa ta ce “Lalalala karka sake ka kirani da Umma dama, ai zaifi maka ka kirani da Fatima sunan da ubana ya rada min, Khadijan daka fada Aisha ka kira baka saya ba, shekara biyu ta baka a duniya idan baka sani ba yau ka rubuta ka ajiye, wawa kawai” ba tare daya juyo ba ya shige dakinsa ya rufo kofar, Anty Khadija da ranta ya gama 6aci ta mike zata nufi kofarsa Umma ta rikota ta ce “Sa ido kiga ikon Allah Dije, maza kwantar da hankalinki” cije baki Anty Khadija tayi ta koma ta zauna tana huci tana huhhuro hanci.

_Two week ltr_
Rafi’ah ce kwance a gefen Abba tana fada mishi abubuwan da zatai na saukarta, Abba ya dan kalleta yana shafa kanta ya ce “Bafa aure bane Mamana” ta dan turo baki cikin shagwa6a ta ce “But Abba ya kamata amin duk abinda nace gaskiya, nice fa first born dinka” yana murmushi ya ce “Kuma Mamana hakama, to kimin list din duk abinda kikeso” ta washe baki ta ce “Insha Allah, i will do so when i have time” Abba ya ce “Good, are u not celebrating world heart day today?” Ta mike zaune tana kallan Abbannata ta ce “I am Abba” ya ce “What have u done for the day?” Ta saki murmushi tana kallansa ta ce “Nayi addu’a Allah ya bani lafiya, dama duk wanda yake suffering da wannan ciwan, and i thank God for giving me such a loving parents like you, i love u Abbana” daga haka ta rungumeshi, Abba ya shafa bayanta gentle ya ce “Allah ya miki albarka ya kuma baki lafiya, but i think u have to go and celebrate there” ta zame jikinta a nashi ta ce “Zanje Abba, ina jiran Ummi ta dawo a office, because i can’t leave you alone” Abba yaja hancinta yana dariya ya ce “Thank u mother, zo ki gayamin me ake a taron naku idan kunje” ta gyara zamanta ta ce “Firstly we introduce ourselves but not all, after then ana bada shawarwari akan yadda mutum zai kula da kansa sabida kar yana samun attack sosai, da kuma what medicine to take idan ka samu attack, after then u rushed for emergency, but the main abinda ake ta fada is heart rest, anaso a kullum mutum ya dinga nutsuwa ya daina sawa kansa damuwa da yawa” Abba ya bata side hug ya ce “Excellent, i hope kina bin duk abinda aka fada?” Ta daga masa kai ta ce “Sosai ma Abba, i really enjoyed this day in life that’s 29 of September” Abba ya bata light kiss a forehead dinta ya ce “Proud to have u daughter, gobe insha Allah zan kaiku gidan Umma tinda yanzu kinji sauki sosai” Rafi’ah ta sauke ajiyar zuciya ta ce “Do u mean gidansu Anty Amina?” Ya ce “Of course, Ita kadai ce uwar data ragemana a yanzu” Rafi’ah ta kwantar da kanta akan shoulder dinsa ta ce “Allah ya jikan Baban Kaduna” Abba ya ce “Ameen” ta dago kuma tana kallan Abba ta ce “Wai Abba da Babanka da Umman Anty Amina waye babba?” Ya ce “Babana ne babba, sai Baba Mu’azu sai kuma Umma” Rafi’ah ta ce “Ohk, i was thinking itace Babba fa” Abba ya girgiza kai ya ce “No, just because she a female”.
Karfe 3 da rabi Ummi ta shigo gidan, a tare suka amsa sallamarta, Rafi’ah ta mike tayi hugging dinta tana mata sannu da zuwa, Abba ya kalleta ya ce “U are welcome, but u look so tired Ummu Rafi’ah” Ummi ta danyi murmushi ta ce “Na gaji kam, yau nayi lectures biyu two~two hours, after then mukai meeting sai to 3 muka fito” Abba ya mata sannu sannan ya mike yana kallan Rafi’ah ya ce “Call Abdul for me, it’s time for prayer” Rafi’ah ta nufi dakinsa tana fadin “Tin da muka dawo a school yau Abdul yake bacci, wallahi Ummi babanki ya zama kasa” Ummi ta dalla mata harara ta ce “Be careful with me” dariya sosai take ta shige dakin Abdul ta hau kan gadon ta dinga mintsilinsa a baya tana ya tashi, da kyar ya mike ya shiga toilet sannan ta fito tana dariya ta ce “Ummi yau 29 of September, zanje taron heart day” Ummi ta ce “But not alone, Mustapha ya kaiki ya jiraki, sannan karki yarda magrib yayi maki a titi” ta ce “To insha Allah, in kawo maki abinci?” Ummi ta girgiza kai ta ce “I want to bath first” Rafi’ah ta nufi upstairs zuwa dakinta ta shiga wanka, ba dadewa ta fito shafa body lotion sannan tasa peach din doguwar riga, kanta ta fara combing tana ta aush tana 6ata rai kamar an sata dole, bayan ta gama ta saka scarf sannan ta yafa veil din rigar tayi simple make up, woooow!!! fans just say masha Allah here, the beauty can’t be describe in one sentence, saina gama page dinma ban gama gaya muku irin kyau din datai ba loooool, turare masu kamshin gaske ta fesa sannan ta dauki flat shoe ta saka ta dauka small side bag ta jefa phone dinta da tissue a ciki sannan ta fita. Tana saukowa downstairs ta samu Ummi zaune nan inda ta barta, ta danyi murmushi ganin kallan da mahaifiyarta ke mata ta ce “Nasan nayi kyau ko Ummi?” Ummi ta maida hankalinta ga TV ta ce “Karki kai magrib Rafi’ah, fatan kuma kinyi sallan la’asar?” Ta ce “Insha Allah Ummi bazan kai magrib ba” Ummi ta ce “Sallan fa?” Ta ce “I’m on period” daga haka ta nufi kofa ta ce “Saina dawo” Ummi ta ce “Allah ya tsare” da Ameen ta amsa sannan ta fita ta kullo kofar, a parking lot ta samu Mustapha yana ta goge mota, yana kallanta ya washe baki ya bude mata back seat ya ce “Kaga turawan asali, Gaskiya Hajiya karama saurayinki yaji dadi, koda wannan kyan aka barshi yaci nasara, bare aje ga hankali, nutsuwa, kyauta, mutunci ga kuma kin fito gidan manya” Rafi’ah couldn’t hold her laugh, ta dinga dariya kafin ta ce “Nikam naji dadina da wannan zancen” Mustapha ya ce “Allah kuwa gaskiya nake fada miki hajiya karama, sai wani walkiya kike kina haske ido” Ita dai dariya kawai take yaja motar suka fita a gidan.
15 minutes ya kaisu inda zasuje, bayan yayi parking Rafi’ah ta fito tana kallansa ta ce “Ka jirani anan, ba dadewa zanyi ba” ya duka cikin girmamawa ya ce “An gama kyakkyawa” daga haka ta juya tana dariya ta shiga cikin hall din, everywhere is silent sai muryar mutumin dake kan stage yana magana da loud speaker, Rafi’ah ta samu seat ta zauna ta maida hankalinta gun mai maganar, shawarwari sosai ya bayar ga masu fama da ciwan zuciya, kusan minti 10 yana bayani sannan yayi musu fatan alkhairi ya bayar da loud speaker, mutumin daya kar6i loud speaker ya danyi karin bayani sannan ya kira Doctor Yusuf akan shima ya fito ya bada tasa gudummawar a matsayinsa na likita kuma mai fama da wannan cuta, cikin light steps Yusuf ya karasa kan stage din ya kar6i loud speaker, shadda ce fara ajikinsa tsaha aiki sai hula baka da half shoes dinsa baki, daga hannunsa kuma kana iya hango wristwatch dinsa black colour sai zoben azurfa dake kyalli a yatsarsa ta tsakiya, cikin sweet voice dinsa yayi wa kowa sallama sannan ya fara bayani da english kamar haka “If you are opting to celebrate this day, it is important to try and be more attentive to your own heart health. There are a number of different ways that you can do this. This includes following a healthy diet, quitting alcohol, stopping smoking, and getting involved in physical exercises…” The hall is so quite harya gama bayaninsa in his good and meaningful English, bayan ya gama ya mikawa na gefensa loud speaker sannan ya sakko akan stage din, daga haka the audience break into rapturous applause. Saurin mayar da kanta gefe tayi ganin ya nufo inda take, bayan ya karaso yaja kujera ya zauna yana kallanta ya ce “Hy” ba tare data juyo ba ta ce “Why not salamu alaikum?” Yusuf ya shafa beard dinsa yana kallanta ya ce “I’m sorry, Assalamu alaikum” ta danyi murmushi ta ce “Wa’alaikumus salaam” ya ce “How are u?” Ta ce “I’m fine and u?” Ya ce “Alhamdulilah also” tayi shiru tana kallan mutum dake bayani akan stage, Yusuf ya ja chair dinsa kusan nata ya ce “Is that all for d greeting?” ta ce “What again? Naga ai mun gaisa” ya girgiza kai ya ce “Actually no, wannan karan shine na hudu da muka hadu, i think we have to introduce ourselves to each other” Rafi’ah ta danyi murmushi ta ce “Ok, but u start” ya ce “Noo, u start” ta dan turo baki sannan ta ce “Ai kasan sunana” ya ce “Amma kuma na manta” ta dan harareshi ta ce “Ohk Sunana Yusuf Muhammad, I’m the first born of the family, kanina guda daya sunansa Abduljalal, my father works with CBN in Abuja, mother is a lecturer, i’m in SS2 now, ina hadda 5 a islamiyya, Abbana dan Kaduna, shi kadai iyayensa suka haifa, Ummi na kuma ‘yar nan Kano ce, su biyu a familyn su ita da yayarta Anty Halima, she is living here in kano also, amma bata ta6a haihuwa ba, Matan Abbana guda biyu ne, so i think this should be my brief history” Yusuf ya saki murmushi yana kallanta ya ce “Nice to meet u Yusuf, hope u are ready to hear mine?” Ta daga masa kai tana murmushi, ya ce “As u know sunana Fatima Muhammad, but they do called me Rafi’ah, ni kadai iyayena suka haifa, sun rasu ta dalilin accident when i was 18 then, lokacin dana gama secondary school dina, both Father and mother are from kano, i did my first degree in Dubai where i studied Medicine, and then goes for PHD where i specialize in Pediatrics, i’m now staying with my father’s sister and her daughter, Ammina ma su biyu ne agidansu, akwai sister dinta dake unguwar rimi” Rafi’ah ta sauke ajiyar zuciya jin iyayensa duk sun rasu, a hankali ta ce “Allah ya musu rahama” ya ce “Amee, Can u pls help me with your digit?”…

_More comments is needed pls, let me see how much u appreciate the book SHARIK HAYATI_

*Join my Facebook grp @Real~Teemarh fans*

*Follow me on wattpad @Real~Teemarh192*

*SHARIK HAYATI*

_08103810398_
[6/9, 11:00 AM] Teemarh: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation
*_…卮乇賷賰 丨賷丕鬲賷…_*
_{MY LIFE PARTNER}_

*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
銆帮笍銆帮笍銆帮笍銆帮笍銆帮笍銆帮笍銆帮笍銆帮笍銆帮笍銆帮笍
_We are here to Educate, Motivate and Entertain our Readers_
銆帮笍銆帮笍銆帮笍銆帮笍銆帮笍銆帮笍銆帮笍銆帮笍銆帮笍銆帮笍

*BY FATIMA* _{Real~Teemarh}_

_17~18_

A hankali Rafi’ah ta dago kanta ta kalleshi, tayi saurin dauke idanta ganin kallanta yake, Yusuf ya gyara hulan kansa yana kallanta ya ce “Ko bazaki bani ba?” Still kanta na kasa bata ce komai, ya ce “Fatima” ba tare data kalleshi ba ta ce “Na’am” ya ce “Won’t you give me?” Juyowa tayi ta dauka phone dinsa dake kan table ta rubuta masa digit dinta sannan ta ajiye wayar, ya dauka yana murmushi yayi dialing phone din, ba jimawa wayarta dake cikin jaka ta fara kara, Yusuf yayi hanging call din yana kallanta ya ce “Thank u much” ta ce “U are welcome” mikewa tayi ta dauka side bag dinta zata wuce yayi saurin riko hannunta, tsayawa tayi cak ta kasa juyowa, ya sake mata hannunta ya ce “Won’t u say bye” a hankali ta ce “Sai anjima” ya ce “Ki zauna kici abinci gashi suna kawowa” Rafi’ah ta girgiza kai ta ce “I’m ok” ya mike yana kallanta ya ce “Let me drop you” ta ce “Tare nake da driver” Yusuf ya ce “Ohk safe, Allah ya kaiku lpy” a hankali ta ce “Ameen” daga haka ta kama hanyar fita a hall din, tsayawa tayi jin sunanta daya sake kira, ya karaso inda take tsaye ya ce “Naga mood dinki ya canza, hope ban maki komai ba” ta girgiza kai a hankali ta ce “Not at all, i just want to rest” daga haka tayi gaba ta barshi tsaye a wajen. Tana isa parking space Mustapha ya bude mata back seat ta shiga ta zauna shima ya shiga mazauninsa ya ja motar suka wuce, tinda suka fara tafiya Rafi’ah ta limshe idanuwanta ta jingina da kujerar motar kamar dai me bacci, a zahirin gaskiya kuma labarin Yusuf kawai take tunawa, duk sai taji tausayinsa deep down her, tin yana kamarta kenan ya rasa iyayensa duka biyu kuma at the same time, hawaye masu zafi taji sun sakko mata, tasa gyalen jikinta tayi saurin gogewa, daga haka ta maida fuskarta jikin window tana kallan mutane. Suna isa gida ta fito a hankali ta shiga ciki, ba kowa a parlor sai karar Fan dana TV, ta wuce upstairs tana kiran sunan Ummi, a bakin kofa suka kusan cin karo, Ummi dake kallanta ta ce “Lafiya kamar an jefo ki?” Veil dinta ta cire ta ce “Lafiya kalau, Ina Abbana?” Ummi ta ce “Ya fita dazu, ya taron?” Silently ta ce “It was fine” daga haka ta wuce dakinta ta rufo kofa.
Da daddare Rafi’ah na kan dinning tana cin indomie data dafa, Abba ya kalli Ummi dake yayyanka Mango ya ce “Why is Abdul don’t want to stay with us always? I have been monitoring him since, sai yayi ta zama a daki what’s the essence?” Ummi ta ajiye knife din hannunta ta ce “Kasanshi da san kallan ball, yanzu haka yasa laptop a gaba yana kai” Abba ya girgiza kai baice komai ba, bayan ya gama shanye mago dinsa ya mike yana kallan Rafi’ah ya ce “Mamana Good night” ta dan turo baki ta ce “Night” Abba ya ce “What again, bakyaso na tafi ne?” Ta ce “Bayan gobe zaka koma kuma yauma saika tafi caan ka kwana” Abba ya ce “I’m sorry mother, i’m spending the night there, hope ba komai ko” daga masa kai tayi sannan ya kalli Ummi ya ce “Sai da safe Madam” ta ce “Allah ya tashemu lafiya” daga haka ya fita ya jawo musu kofar, Tashi Rafi’ah tayi ta dawo kusa da Ummi ta ce “Mummy fa yau saura sati 2 ta dawo ko?” Ummi ta ce “Hakane” Rafi’ah ta ce “I’m eager, cewa tayi fa gidanta za… ” shiru tayi jin phone dinta na ringing, ta karasa wajen TV stand ta dauka wayar, Ummi dake kallanta ta ce “Who’s that?” A hankali ta ce “Salmah ce, inaga maganar assignment din nan ne” daga haka ta nufi upstairs Ummi ta bita da kallo, tana shiga dakinta tayi picking call din ta kai kunnenta hade da sallama, on the other side Yusuf ya ce “How are u?” Ta zauna gefen gado ta ce “Fine, how is everyone?” Ya ce “Kowa lpy, hope kin isa gida safe?” Ta daga masa kai kafin ta ce “Sure” ya ce “Masha Allah” shiru tayi bata sake cewa komai ba, caan ya dan sauke ajiyar zuciya ya kira sunanta, silently ta amsa idanuwanta a limshe ya ce “When is ur marriage?” Rafi’ah ta zaro ido sai kuma ta ce “Aure kuma?” Ya ce “Ehh, ko baza kiyi inviting dina ba?” Ta danyi murmushi ta ce “Ba rana” Yusuf ya ce “Why, duk samarinki kice ba rana” dariya ta danyi har yana jiyota kafin ta ce “Nikam banida samari, im still young, SS2 fa kawai nake” ya bude eyes dinsa dake limshe ya ce “I disagree, kina da samari da yawa heart dina tamin searching na gani”. Dariya sosai ta kyalkyale dashi kafin ta ce “I’m serious Dr, i am not in any relationship yet” ya ce “Really?” Ta ce “Serious” kasa kasa yayi da murya ya ce “Can we meet tomorrow?” Ta danyi shiru sai kuma ta ce “Where?” Ya ce “Duk inda kika ga kina so, kona zo gida?” Ta zaro idanuwanta waje ta ce “Noo, gobe Sunday, zanje islamiyya” Yusuf ya ce “By what time?” Ta ce “8 muke zuwa mu dawo 12” ya ce “Alright i think we meet around 11” ta ce “How?” Ya ce “I will come and call u insha Allah” ta ce “But… ” Yusuf ya ce “Say it” ta danyi shiru sannan ta ce “Amma ba inda zan bika”, dariya yayi a hankali ya ce “Sure, a bakin gate zamu tsaya, i just want to tell u something” ta ce “What’s that Doctor?” Ya ce “There are a lot, nafiso na fada miki face to face” ta ce “Ohk, Allah ya kaimu” ya ce “Ameen”, jin kiran da Ummi ke mata yasa ta mike da sauri ta ce “Ummi na kirana, good night” ya ce “Sweet dreams” daga haka yayi hanging call din ya jingina kansa da gadonsa yana imagining yadda take dariya da kuma irin kunyarta, he always like yadda take sunkuyar da kai, the way she talks, and when she’s laughing…

*SHARIK HAYATI*

*The more u people comment the more i will type* 馃え

_08103810398_

https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation
*_…卮乇賷賰 丨賷丕鬲賷…_*
_{MY LIFE PARTNER}_

*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
銆帮笍銆帮笍銆帮笍銆帮笍銆帮笍銆帮笍銆帮笍銆帮笍銆帮笍銆帮笍
_We are here to Educate, Motivate and Entertain our Readers_
銆帮笍銆帮笍銆帮笍銆帮笍銆帮笍銆帮笍銆帮笍銆帮笍銆帮笍銆帮笍

*BY FATIMA* _{Real~Teemarh}_

_19~20_

Washegari da sassafe Ummi ta tashi ta fara hadawa Abba breakfast, tana cikin aiki taji an danna bell, ta wanke hannunta a sink sannan ta fito a kitchen ta bude kofar parlorn, Abba ya saki murmushi yana kallanta ya ce “Ina Mamana, hope ta hadamin breakfast” Ummi ta bashi hanya ya shigo ta ce “Indai Mamankan nan ne ai sai dai ka tafi da yunwa” Abba ya zauna kan sofa ya ce “Baki tasheta ba kawai Madam” Ummi ta danyi murmushi ta ce “Morning” ya ce “Morning, ya kwanan yaran?” Ta ce “Kowa lpy, karfe nawa zaku tashi?” Abba ya ce “By 9, baki gama bane?” Ta ce “Saura kadan” daga haka ta koma kitchen ta dauko flask din shayi ta ajiye masa akan dinning. Ba jimawa ta kammala duk wani abinda yake da bukata ta jera masa sannan ta wuce upstairs, a parlor ta sami Rafi”ah na kwance akan kujera tayi rub da ciki, Ummi ta ta6a jikinta to make sure she’s fine, tashi tayi ta zauna tana goge idanta silently ta ce “Ina kwana” Ummi ta ce “Lafiya, ki tashi kije Abba yana kasa” mikewa tayi a hankali ta wuce downstairs still tana goge siraran hawayen dake zubo mata time by time, Abba kadai ta samu zaune a kan dinning yana cin abinci, ya miko mata hannunsa na hagu ya ce “Come on Mamana” Rafi’ah ta saka hannunta daya cikin nasa ta karasa gefensa, har lokacin bata yarda sun hada ido ba, Abba ya zaunarta gefensa ya ce “How was your night?” silently ta ce “Fine, Abba tafiya zaka yi?” Ta karashe maganar tana san yin kuka, Abba ya shafa kanta ya ce “I’m sorry daughter, very soon zan dawo kinji, kinga tin last two week ya kamata na koma to ban samu ba saboda kinyi rashin lafiya, i hope u are not crying” ta sauke kanta kasa tana tare hawayen idanta, Abba ya share mata idanta tass, bayan haka ya tura plate din abincin gabanta ya ce “Let’s eat together” daga haka ta dauka fork ta faracin abinci. Suna cikin ci Abdul ya fito daga dakinshi, manyan kayane ajikinshi da sukai mataukar kar6enshi, yaja kujera ya zauna yana kallan Abba ya ce “Morning” Abba ya ce “How are u?” A hankali ya ce “Fine” daga haka shima ya dauka plate ya fara serving kansa, sai kallan Rafi’ah yake yana dariya kasa~kasa, bayan ya fara cin abincin ya ce “Ina kwana Anty” Bata amsa shi ba saima harara data dalla masa, Abba ya danyi murmyshi ya ce “Can’t u respond? Haba Mamana” mayar da kanta tayi gefe ta ce “Abba dariya fa yake min” Abba ya ce “To Abdul ka daina mata dariya, maza amsa masa gaisuwar da yayi” calmly ta ce “I’m fine” Abdul yayi dariya zaiyi magana Abba ya masa alamar yayi shiru, daga haka ya mike ya ce “Let me see ur Mum upstairs”.
A daki Abba ya samu Ummi tana waya da Anty Halima, ganinsa yasa ta ce “Zan kiraki anjima” daga haka tayi hanging wayar tana kallansa ta ce “Har kun gama?” Abba ya zauna gefenta ya ce “Ehh, na miki transfer ko kin gani” ta ce “Ehh na gani just few minutes from now, Allah ya kara budi ya kuma kiyaye hanya” Abba ya ce “Ameen, idan akwai wani abu u let me know” ta girgiza kai ta ce “Ba komai yanzu kam” ya ce “Alright, Amina na nan itama, nace mata ta jira next idan na dawo sai mu koma” Ummi ta ce “To” ya mike yana kallan agogon dakin ya ce “Yaran nan idan sun dawo a islamiyya akai su gidan Umma su gaisheta, naso muje but Allah baiyi ba” Ummi ta ce “To insha Allah” Abba ya mike ya ce “I think i have to go Ummu Rafi’ah” Ummi ta daukar masa karamar traveling bag dinsa ta ce “Allah ya sauke ku lpy”, suna saukowa Abdul ya kar6i jakar a hannun Ummi sannan ya fita da ita zuwa mota, Rafi’ah ta mike ta ce “Allah ya kiyaye Abba” ya ce “Ameen Mamana, hope ba zaki kuka ba?” Ta daga masa kai ta ce “Ehh Abba” daga haka ya kama hannunta, Ummi dake kallansu ta ta6e ta ce “Safe flight” ya ce “Ameen, Ameen” daga haka suka fita Ummi ta dawo ciki. har bakin mota Rafi’ah ta rakashi tana ta mishi bye bye, Abdul ya leka motar yana kallan Abba ya ce “Allah ya kiyaye Abba” Abba ya ce “Ameen, ayi ta kokari ayi ta karatu, Allah kuma ya muku albarka” a hankali Rafi’ah ta amsa da Ameen sannan ta rife masa kofar mota, hannu suka dinga daga masa har Mustapha ya fita da motar.
Rafi’ah na komawa parlor ta turo baki ta zauna gefen Ummi ta ce “Abba ya tafi” Ummi ta ce “Da kin bishi ai, ki tashi ku fara shirin islamiyya” Rafi’ah ta ce “Ummi ya Abba bai tafi da Anty Amina ba” Ummi ta ce “You can call him and ask” ta kara turo baki ta ce “Ni wallahi banaso ta zauna damu, gara ta tafi caan gidan Umma” Ummi ta ta6e baki ta ce “Sai ki koreta ai idan zamanki take” Rafi’ah ta kwanta ta ce “Sai tai ta yima mutane kallan banza” cikin tsawa Ummi ta ce “Cewa nayi ki tashi kiyi shirin islamiyya ko?” ta mike da sauri ta wuce upstair. Da yake atampa ne ajikinta zulelen himar dinta kawai ta saka ta shafa power da lipstick, tayi kyau sosai da sosai, daga haka ta dauka side bag dinta me dauke da Qur’an da sauran littafai sannan ta dauka phone dinta ta jefa a ciki, tana saukowa ta samu Abdul gefen Ummi yana rokonta ta bashi mota, Ummi ta mike ta ce “Idan baza ku hau keke Napeep ba kar kuje islamiyyan” Abdul ya ce “Ba ina fita dake ba, dan Allah ki bani” ta ce “Dani kace ai Babana, amma bazan baka mota daga kai sai Rafi’ah ba” daga haka ta ajiye musu 1k ta ce “Gashi idan kuna da niyya” Rafi’ah ta dauka kudin ta nufi kofa ta ce “Malam ka taso mu tafi” daga haka ta fice yabi bayanta yana gyara hulan kansa,
Anty Amina ce zaune gefen Ummanta tana sauraren abinda suke fada, bayan ta dasa aya Anty Rahama ta mike tana tafa hannu ta ce “Wallahi Umma bata isa ba, ninasan shiga tayi ta fita tasa yace bazai tafi da Amina ba” Umma dake zaune kan kujera ta ce “Ai kuwa kanta tayi wa, dan wallahi yanzu zata san ba’a ta6amin ‘ya’yana a zauna lafiya” Anty Amina ta share hawayen idanta ta ce “Abin haushinma Umma saida na shirya kawai jiya da daddare yake cemin na zauna saiya kuma dawowa, kuma Umma nasan matarsa ce silan komai, ni kuwa ban masa girki ba wallahi” Umma tayi wani shu’umin murmushi ta ce “Nace miki kanta tayiw Amina, zata gane ba’a ta6a min zuri’a a kwana lafiya” Anty Rahama dake huci ta ce “Idan batai wasa ba saina 6atar da ‘ya’yan da take takama dasu, idan yaso ta mutu kowa ma ya huta, da kyar idan tafiya aikin da take ba bin maza take ba” Anty Amina ta kwantar da kanta a cikinyar Umma ta ce “Dama mana, bakiga sai kudi take samu ba, banda haka ya za’ai ace kwanan nan ta canza mota sannan ba’a fi wata hudu ba har ta siyar ta sayi wata” Anty Rahama ta ce “Uhmm kinji ko Umma, idan ba maza take bi ba nawa ake bawa malaman jami’a da har take tara kudi haka” tashi Umma tayi ta bar musu parlor saboda phone dinta dake ringing a cikin daki. A hankali ya bude kofar dakinsa ya fito, kananun kaya ne a jikinsa sunyi masifar yi masa kyau, gashin kansa sai sheki yake, Umma ce kadai a parlon tana zaune, ta dago kanta ta kalleshi sannan ta dauke kai ta wani hade rai, Yusuf ya zauna a kan kujerar dake opposite dinta ya ce “Ina kwana” kamar ba zata amsa ba sai kuma ta ce “Lafiya” daga haka ya mike ya nufi kofa zai fita ta ce “Ka dawo ka zauna” dawowa yayi ya zauna ya zuba mata ido yana jira ta fadi abinda zata ce, kusan minti 3 yana zaune bata ce komai ba ya danyi kasa da kansa ya ce “Umma ina jinki” ta dora kafarta daya akan daya kafin ta ce “Banga ka turo kudin dana ce maka ba” ya sunkuyar da kansa ya ce “Ehh ban manta ba, akwai gyaran da zanyi a gidana wannan month din, sai dai ko next month na tura miki” Umma ta ce “To baka isa ba, saika bar gyaran gidan idan ka gama hadawa Jiddah lefe sai kayi” Yusuf ya sauke ajiyar zuciya ya ce “To, nawa zan tura miki yanzu” ta ce “300k, sai na fara dasu kafin wani watan” dago kansa yayi yana kallanta with disturb, Umma ta ce “Ko baza kai ba nasan abin yi” a hankali ya ce “Zanyi” daga haka ya mike ta ce “Ina kuma zaka naga yau Sunday” ya ce “Zanje gidan Mubarak ne, matanshi ta haihu yesterday night” Umma ta ta6e baki ta ce “Haka dai, yawan banzan baya karewa” shikam tin tini ya fita a parlon dan dama bai tsaya jin me zata ce ba, yana isa parking lot ya shiga motarsa ya kifa kansa akan kujera, kusan minti 10 yana haka kafin ya mike ya sawa motar ya fice a gidan. Duk yadda Rafi’ah zatai saida tasan yadda tayi ta bada haddanta da wuri, karfe 11 da minti 10 kiran Yusuf ya shigo wayarta, ta dauka a hankali tayi sallama ya ce “I’m outside” daga haka tayi hanging wayar ta mike ta dauka jakarta, durkusawa tayi gefen malaminsu ta ce “Ya Sayyadi Yayan nawa ya zo” ya dago yana kallanta ya ce “Allah ya kiyaye” ta ce “Ameen” daga haka ta mike ta fita a class din. Tin da ta fito Yusuf yake kallanta harta tsallako titi ta karaso inda yake tsaye, yayi folding hannayensa yana murmushi ya ce “Ashe zaki iya fitowa” ta danyi murmushi kanta a kasa ta ce “Good morning” ya ce “Morning, how was ur night?” Silently ta ce “It was fine” ya bude mata back seat ya ce “You enter” dagowa tayi tana kallansa, ya ce “Do i look like a kidnapper?” Ta ce “No, but i prepare to stay here” Yusuf dake kallanta ya ce “Pls ki shiga” ta ce “Here is also ok Doctor” ya sauke ajiyar zuciya yana cusa hannunsa a pocket dinsa ya ce “To akwai balcony a nan kwanar sai mu zauna” a hankali ta juya ta kalli direction din inda yake nuna mata, ganin wajen ba mutane yasa ta karasa wajen ta zauna, bayan ya rife motar shima ya karaso ya zauna gefenta yana murmushi, kauda kanta tayi gefe ganin kallanta yake, Yusuf yayi dariya kafin ya ce “How is Ummi?” Ta ce “Tana gida” ya ce “Daddy fa?” Ta ce “Dazu ya koma Abuja” Yusuf ya ce “Allah ya kai shi lafiya” ta ce “Ameen”, shiru duk sukai na tsawon lokaci, Yusuf yayi breaking silent din ta hanyar kiran sunanta, ta juyo ta kalleshi sannan ta amsa, ya ce “U told me that u aren’t in any relationship right?” Ta daga masa kai ba tare data kalleshi ba, Yusuf ya ce “Good” shiru yayi na dan lokaci kafin ya dan kalleta ya ce “I think it’s a care and pity before, but now i discover that it was love at first sight” dago kanta tayi da sauri ta kalleshi, suna hada ido ta sauke kanta kasa zuciyarta na bugawa, she never expect such speech from him, bayan haka this is the first time wani ya ta6a cewa yana santa, Yusuf ya gyara farin glasses din idansa ya ce “I know u are shock with my words, but pls do accept me, i Yusuf i promise not to disappoint, zan zauna dake har karshen rayuwata Rafi’ah, i will never ever cheat on you, wallahi wallahi words only can’t express how much u are to me, na fara sanki since from the first day i saw u”. Shiru Rafi’ah tayi ta dinga jujjuya ring din hannunta, she can’t just imagine herself wai ita ne aka furtawa kalmar so, cikin sweet and cool voice dinsa ya ce “But it isn’t by force, if u are not interested in me i can give up” shiru bata ce komai, ya dan shafa gashin kansa yana kallanta ya ce “Ohk, idan baki ce komai ba that means u accepted” da sauri ta juyo tana kallansa ta ce “No! pls” ya ce “Then say something” turo baki tayi ta ce “To ai ni ban san ya ake cewa ba, and this is the first time wani yace min yana so…” Shiru tayi ta rife fuskarta da himar din jikinta, Yusuf couldn’t hold his laugh, looking smiley ya ce “I know Fatima, but say something even if it is OK” har lokacin bata bude face dinta ba, ta ce “Sai dai ka zama Yayana tinda ni banda shi” ya ce “To kinsan me za’ai” ta girgiza kai still fuskarta a rife, ya ce “Ai Yaya baya auren kanwarsa, but let’s make ourselves to be cousins, kinga at the end zamu iya yin aure” ita dai bata ce komai ba banda murmushi da take, Yusuf ya janye hijabin a fuskarta ya ce “Ki daina rufemin cute face din nan” juya kanta tayi gefe ta ce “Pls stop Doctor” ya ce “To kice wani abu” ta make kafada, Yusuf ya ce “Pls beautiful” Mikewa tayi da sauri sakamakon bell da taji an kada, ta dan kalleshi ta ce “Zan tafi kar Abdul ya nemeni” ya ce “Muje to saina sauke ku a gida” ta ce “Driver dinmu zaizo” daga haka tabi ta gefenshi ta wuce ya bita da kallo yana murmushi.
Tana zuwa bakin gate din islamiyyan ta samu Mustpha yayi parking, ta bude back seat ta shiga sannan suka jira Abdul, bayan ya shigo Mustapha yayi reverse suka juya, Rafi’ah ta kalli direction din da motar Yusuf yake, a tsaye ta ganshi yana kallansu, yayi saurin daga mata hannu ta kauda kanta gefe. Within 10 minutes suka isa gida, Mustpha na parking suka fito suka nufi entrance din gida, Ummi ce zaune a parlor tana yanka pumpkin leaf, Rafi’ah ta zauna gefenta ta ce “Mun dawo” Ummi ta ce “U are welcome” ta cire hijabin jikinta ta ce “Pls Ummi ki samin credit na kira Mummy” Ummi ta ce “Never, Abba baya tura maki kudi ba?” Rafi’ah ta ce “A’a fa, bai bani ba” Ummi ta ce “Check now, dazu da mukai waya yace ya tura maki” wayarta ta dauko a jaka ta shiga messages, aikam tana budewa taga credit alert na 10k, ta danyi murmushi ta ce “Na gani, thanks” Ummi ta ce “Sai ki kirashi”. Recharging ta fara yi sannan tayi dialing phone din Abba, yana picking ya ce “How are u Mum? Kunje islamiyya?” Ta ce “Fine Abba, how was ur journey?” Ya ce “Alhamdulilah” ta ce “Yanzu naga alert thank u so much, Allah ya kara arziki” ya ce “Mention not, i will call u ltr” a hankali ta ce “Ohk bye” tana hanging wayar Ummi ta ce “Da yamma zakuje gidan Umma” Rafi’ah ta dan hade rai ta ce “Nikam gaskiya bazanje ba, dama dai da Abba ne” Ummi ta dalla mata harara ta ce “Sai ki kira wanda ya fada kice mishi baza kije ba” turo baki ta kara yi ta ce “Ni kam gaskiya ni banaso, Ummi fa basa dariya sai suyi ta hade rai, kuma wallahi wannan karan bazan musu shara ba” ko kallanta Ummi batai ba bare ta bata amsa, Rafi’ah ta ajiye wayarta gefen Ummi ta ce “Kuma ma Anty Amina tana caan, su taru suyi ta zagin mutum, ni wallahi gara nayi bacci akan…” cushion Ummi ta gefa mata ta ce “Idan sun zageki ajikinki zai fito ko naman jikinki suke gutsura? Wallahi idan baki shiga hankalin ki ba i’m going to deal with u honestly, ke ba kya shiru ne a rayuwarki? Must u talk? and let me hear u talk again kiga ikon Allah” shiru tayi ta kifa kanta akan kujera, deep down her kuma tayi alkawarin indai taje baza ta musu aiki ba, ba kuma za’a zageta ta kyale ba. Suddenly phone dinta dake ajiye kan sofa ya hau ringing, Ummi ta dinga kallan screen din ganin an rubuta Dr. Yusuf, tashi Rafi’ah tayi daga inda take ta dauka wayar sannan ta nufi upstairs Ummi ta bita da kallo. Direct dakinta ta shiga bayan tayi picking call din ta zauna bakin gado, Yusuf ya ce “How are u dear?” Silently ta ce “Fine” ya ce “Why the mood?” share dan guntun hawayenta tayi ta ce “Wai saina je gidan Umma ne” Yusuf ya shafa gashin kansa yana murmushi ya ce “Who said so? And who is Umma” a hankali ta ce “Kanwar Kakanmu ce” Yusuf ya dan zaro ido ya ce “To meyasa bakinsan zuwa? Is she not ur grandmother?” Sake share idanta tayi ta ce “She is, but basa sona ai” Cikin rarrashi Yusuf ya ce “Kiyi hakuri to kije kinji Baby” ta dan turo baki ta ce “Ni banaso” ya ce “I know but for the sake of ur parents, ai lada ma zaki samu idan kikaje, kinga kinyi ziyara” ta ce “Uhm, uhm” ya ce “Bakisan ladan Baby?” Ta ce “Inaso” ya ce “Then smile” ita kanta batasan lokacin data saki murmushi ba, ya ce “Alright, i will call u ltr ina driving ne” ta ce “Allah ya kiyaye” ya ce “Won’t u say bye~bye my love” ta danyi dariya kawai, ya ce “Oh na baki dariya kenan?” ta ce “Something like that” ya ce “ko?” Ta ce “Ehh” ya ce “To zan kiraki anjima, bye bye love” saurin rife ido tayi ta janye wayar a kunnenta tayi hanging call din, tana juyawa sukai ido hudu da Ummi, sai da zuciyarta ya buga at first, Ummi ta ce “Who’s that?” Shiru tayi ta sunkuyar da kanta kasa, Ummi ta ce “I’m i not talking to Rafi’ah?” A hankali ta dago kanta tana kallanta ta ce…

_I LUV U FANS_ 馃槃

*SHARIK HAYATI*

_08103810398_

https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation
*_…卮乇賷賰 丨賷丕鬲賷…_*
_{MY LIFE PARTNER}_

*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
銆帮笍銆帮笍銆帮笍銆帮笍銆帮笍銆帮笍銆帮笍銆帮笍銆帮笍銆帮笍
_We are here to Educate, Motivate and Entertain our Readers_
銆帮笍銆帮笍銆帮笍銆帮笍銆帮笍銆帮笍銆帮笍銆帮笍銆帮笍銆帮笍

*BY FATIMA* _{Real~Teemarh}_

_21~22_

Karfe uku da rabi Ummi ta shigo dakin Rafi’ah ta tashe ta a bacci, tayi mitsi~mitsi da ido tana kallan Ummi ta ce “Abdul din bai dawo ba shine na kwanta” Ummi dake kallanta ta ce “Abdul Baffa ya kirashi, ki tashi ki shirya Mustapha ya kaiki, shi yaje daga baya” turo baki tayi ta janye duvet din jikinta ta ce “But Abba said we should go together” Ummi ta wurga mata harara ta ce “To karki shirya ki sauko, continue arguing with me” tana dasa aya ta fita a dakin taja mata kofar, Rafi’ah ta sauke ajiyar zuciya kafin ta mike ta shiga toilet, few minutes ta fito da towel a jikinta, ta zauna gaban mirror ta shafe jikinta sannan ta bude press dinta ta dauko atampa ta saka, das~das dinkin ya zauna a jikinta, tayi combing hair dinta sannan ta daura head tie dinta ta saka hijabi iya knees dinta, babu ko powder a fuskarta amma tayi kyau sosai, ta dauka side bag dinta da phone sannan ta sauko downstairs. Ummi ce kadai a parlor da laptop a gabanta, Rafi’ah ta zauna gefenta ta ce “Na shirya” Ummi ta dago tana kallanta ta ce “Ko powder ba zaki shafa ba Rafi’ah?” dan bakinta ta turo ta ce “Ni haka nakeso” Ummi ta ta6e baki ta ce “Ga turare ki kaiwa Umma, my regards to them” ta karashe maganar tana mikawa Rafi’ah ledan da turaren yake ciki, kar6a tayi ta mike ta ce “Sai na dawo” Ummi ta ce “Ki gaishe su, bayan Magrib zai koma ya dauko ki” a hankali ta ce “Toh” sannan ta fita a parlor. 10 minutes with some seconds ya kaisu gidan Umma, Mustapha yayi parking a waje ta masa sallama sannan ta fito ta shiga gidan, ba kowa a compound din sai mota kwaya daya a parking lot, ta karasa entrance din gidan ta murda handle din kofar ta shiga da sallama, babu wanda ya amsa mata sai ido da suka zuba mata duk tasu, dan basuyi zatan zuwanta gidan ba, dama mostly da Abba suke zuwa. A hankali Rafi’ah ta karasa cikin parlor ta zauna a kan carpet ta ce “Ina wunin ku?” Ba yabo ba fallasa Anty Rahama ta ce “Lafiya kalau” Anty Amina kuwa kota daga kanta ta kalli inda take. Bayan 10 minutes Anty Rahama ta kalli diyarta dake kwance kan sofa ta ce “Ikleema tashi kuje ki nuna mata toilet dina ta wanke min” with surprise Rafi’ah take kallan Anty Rahama, tashi tayi tana gyaran wuyan hijab dinta ta ce “Dama Abba cewa yayi nazo na gaishe da Umma, ga wannan inji Ummina a bata” daga haka ta nufi kofar fita, Ikleema ta ce “Ai gara da kika tafi gayyar tsiya” Rafi’ah ta juyo tana kallanta ta ce “Ga tsiya kam ai kina cikin ta” ganin Anty Rahama ta taso tana kunduma zagi yasa taja musu kofar da gudu ta nufi gate ta fita, cikin sauri ta karasa bakin titi ta tsare me Napeep ta shige, sai sauke ajiyar zuciya take tana huci, bayan minti 2 mai Napeep din ya juyo yana kallanta ya ce “Ina zakije ‘Yammata?” A hankali ta fada mishi inda zai kaita sannan ta kifa kanta tana kokarin dai dai ta numfashinta. Bayan ta iso gida ta cire 500 a jakarta ta bashi ya bata change sannan ta shiga gida, tana bude kofar parlor Ummi ta ce “Zo nan Rafi’ah” baya ta dan ja ta ce “Wallahi Ummu ba abinda na musu” Ummi da ranta ya gama 6aci ta ce “Of all abinda na fada miki baki jiba Rafi’ah sai da kikaje kika jawomin magana” Rafi’ah ta dan zaro ido ta ce “I swear Ummi ni ban ce musu komai, bafa dasu nake ba, nida Ikleema nake” Ummi ta ce “I’m that kind of mother who doesn’t talks but kika kaini karshe billahil azeem u will regret” Rafi’ah dake tsaye bakin kofa ta share guntun hawayenta ta ce “Ai dama nasan Abba zasu kira suce na zagesu, kuma wallahi ni ba dasu nake ba, Ikleemah ce ta fara cemin gayyar tsiya” daga haka ta fashe da kuka ta tsuguna a wajen, Ummi taja tsaki ta ce “Tinda kinsan dama neman fada suke data zageki ai saiki mata shiru, gashi nan yanzu sun hada karya da gaskiya sun gayawa Abba, sai kuma kisan abinda zaki ce masa ya sauko” daga haka Ummi ta mike ta shiga kitchen, tashi Rafi’ah tayi ta share idanta ciki ciki ta ce “Wallahi duk wanda ya hadani da Abba shida Allah” Ummi da fitowanta a kitchen kenan ta ce “Ke dai kika sani kuma, and don’t involve me in this case, ko sunana ban yarda ki kira ba, banasan abinda zai 6ata min rai ina zaman zamana” Rafi’ah ta sake tare hawayen idanta ta wuce dakin Abdul.

_Two weeks ltr_
Ummi ce Zaune a kitchen tana hada coleslaw cikin bowl Abdul na 6are maggi a gefenta, bayan ya gama ya mika mata ta ce “Keep it there” a kan drawer ya ajiye ya dawo gefenta ya zauna, dai dai lokacin Rafi’ah ta shigo kitchen din, ta dan tsaya bakin door ganin sun gama aikin da suke, karasawa ciki tayi tana kallan Ummi ta ce “Wai meyasa bazata sauka anan ba Ummi?” Ummi ta ce “Da gidanta dan meyasa zata sauka a gidanku” Ta dan turo baki ta ce “To nidai caan zan tafi” a takaice Ummi ta ce “Abba yace babu me zuwa, tinda zasu kai karfe 12 kafin suyi landing, kuma itama cewa tayi ku zauna gobe da safe zata zo” Rafi’ah dake kallan Ummi ta ce “Har sai gobe zamu ganta” Ummi ta dalla mata harara ta ce “Keep shut quite now, ke bakisan tara ki nake bako Rafi’ah? tinda muka fara aikin nan kika tafi kika kata waya baki dawo ba sai yanzu, kinzo kuma kin isheni da surutu, better mind ur words, bari kuma Abba ya dawo ki masa bayanin da uban wa kike waya da bazaki gayamin ba” a hankali ta sunkuyar da kanta ta ce “Kiyi hakuri” Ummi bata ko kalleta ba taci gaba da abinda take. Bayan ta gama ta hada komai cikin basket ta bawa Mustapha ya kai gidan Mummy da yake akwai mai aikinta a gidan. Ganin ba kaisu caan gidan za’ai ba yasa Rafi’ah tayi sallan ishanta ta shiga daki ta kwanta, harta fara bacci phone dinta ya fara ringing, ta dauka a hankali ta kara a kunne hade da sallama, Yusuf ya dan zaro ido jin muryarta ya ce “Are u sleeping Baby?” Ta dan turo baki ta ce “I’m tired that’s why” ya ce “Sorry, kinyi wa Mummy abinci ne?” Ta danyi murmushi ta ce “Sure” ya ce “Ohk let me leave u rest” ta ce “Uhm, till tomorrow” ya ce “Byee” tana hanging wayar ta kasheta duka duka ta koma baccinta. Washegari tinda Rafi’ah tayi sallan asuba tayi wanka, bayan ta shirya tayi dialing number Mummy, bata dauka ba har kiran ya katse. Karfe 7:30 Mummy ta iso gidan, Abdul ya mike jin horn ya leka ta window, dan murmushi yayi yana kallan Ummi ya ce “It’s Mummy” daga haka ya bude kofar ya fita da sauri, rungumeta yayi yana ta bubbuga bayanta looking happy ya ce “You are welcome mother” Mummy ta kama hannunsa ta ce “How are u, ya sai tsayi kake?” Abdul ya danyi dariya yana kallan saurayin dake tsaye jikin motarsa ya ce “Ina kwana?” Cike da fara’a ya ce “Lafiya kalau and u?” Abdul ya ce “Also fine”, Mummy ta juyo tana kallansa ta ce “U come in Jawad” daga haka suka nufi entrance din gidan tana rike da hannun Abdul, Suna shiga ciki Ummi ta rungumeta ta ce “Sannu da zuwa Anty, ya hanya?” Mummy ta ce “Alhamdulilah, ya muka sameku?” Ummi dake murmushi ta ce “Lafiyar kowa kalau” sai lokacin Jawad ya tsuguna bakin kofa ya ce “Ina kwana” Ummi ta ce “Lafiya kalau, Jawad, kaine yau a gidanmu” ya danyi murmushi yana shafa kanshi, Mummy ta ce “Ai ba zaman kasar yake ba, shima day before yesterday ya dawo daga Ukraine” Ummi ta ce “Ayya, kayi masters kenan” ya daga mata kai yana murmushi, Mummy ta ce “Yanzu zai ci gaba da aiki ba” Ummi ta ce “Masha Allah that was great, yasu Mamanku?” Yayi kasa da kansa ya ce “Suna nan, gobe zasu wuce Abuja” yana rife bakinsa Rafi’ah ta sauko a guje ta rungume Mummy kam kam, Mummy ta shafa bayanta ta ce “How are u daughter?” A hankali ta dago kanta ta ce “Fine Mummy, ya hanya?” Mummy ta ce “Masha Allah” daga haka ta kara rungume Mummy tana murmushi, Ummi ta mike tana kallan Jawad ta ce “Ka zauna kan sofa mana” Rafi’ah ta dago kanta jin an kira Jawad, suna hada ido ta dauke kanta tana kallan Mummy ta ce “Abbana ma ya kusan dawowa, saura kwana uku” Mummy ta ce “Munyi waya ai jiya, ga Jawad baku gaisa ba” Rafi’ah ta dan turo baki ta ce “Shida bayawa mutane magana, in munje sai yayi ta hade rai da fishi” Mummy ta dan zaro ido ta ce “Wai hakane Jawad?” Shidai baice komai ba yayi murmushi yaci gaba da danna phone dinsa. Breakfast Ummi ta jera musu akan dinning ta ce “Anty Halima ga abinci, Jawad u come forward”. mikewa Mummy tayi ta koma dinning ta zauna, Rafi’ah ta dawo gefenta ta ce “Let me serve u Mummy” daga haka ta dauka plate ta fara zuba mata abinci, few minutes Mummy ta gama breakfast dinta, ta mike tana kallan Jawad dake danna waya har lokacin ta ce “Bismillah Jawad” ya tashi a hankali ya ce “To” Mummy ta wuce upstair tana fadin “Ina Zainab din take ne”.
Jawad na zama akan dinning ya kalli Rafi’ah dake cin chips and egg ya ce “Can’t u great?” Ta dan 6ata fuska ta ce “Bayan baka ma mutane magana a gidanku” ya ce “To ai yanzu gidanku nazo” a hankali ta ce “Morning” ya ce “How are u?” Ta ce “Fine”, kusan minti 10 basu kara cewa komai ba, Jawad ya ajiye cup din tea yana kallanta ya ce “Ya jinki kuma?” With surprise ta dago tana kallansa, taya yasan bata da lpy to? Jin tayi shiru yasa ya ce “Allah ya kara sauki”, suddenly phone dinta dake gefensu ya fara ringing, Jawad ya kalli screen din sannan ya kalleta, daukan phone din tayi ta wuce kitchen, bayan tayi picking tayi sallama, Yusuf ya ce “How are u Baby? I just saw ur text now” ta danyi murmushi ta ce “Yanzu ka tashi kenan?” Ya ce “Of course, fatan sun iso lpy?” Ta ce “Ehh Alhamdulilah” limshe idanuwansa yayi murya caan kasa ya ce “I want to see u Baby” ta sunkuyar da kanta tana murmushi ta ce “Ohk, anjima zanbi Mummy gidanta sai kazo caan” cike da farinciki ya ce “Woow thank u luv, mezan kawo maki?” Ta saki murmushi ta ce “Nothing” ya ce “No say something pls” a hankali ta ce “Khairiyya” ya dan zaro ido ya ce “Ba yanzu ba, but i promise she would come one day” turo baki ta danyi ta ce “Pls Doctor, inasan na ganta ne?” Ya ce “I promise u zan kawota watarana kinji Baby” ta ce “To” ya ce “Hope you’re not angry” ta kara sakin murmushi ta ce “No” ya ce “Alright by what time zanje caan din” ta dan juya idanta kamar yana gabanta ta ce “I think after Asr” ya ce “Ohk, which area?” ta fada masa sunan anguwan da kuma house number, Yusuf ya ce “Understood, thank u so much love” rife fuskarta tayi da tafin hannunta ta ce “Sai anjima” ya ce “Bye” daga haka yayi hanging wayar, tashi yayi ya janye duvet din jikinsa ya tsaya gaban mirror, farar riga ce a jikinsa sai tree quarter ash colour, comb yasa ya taje gasjin kansa sannan ya dauki laptop dinsa ya fito a dakin, Da sauri ya tsaya ganin Umma a parlor da Anty Khadija suna ta daddaga kayan da umma ta siyo na lefe, Yusuf ya dauke kansa ya ce “Ina kwana Umma” cike da fara’a ta ce “Lafiya Yusuf, kaga dai kayan dana fara siyowa” ba tare daya kalli kayan ba ya ce “Sunyi kyau” Umma ta taso da wani tsadadden lace a hannunta ta ce “Kaga wannan ai yayi kyau ko Yusuf, ko kuma kafisan red color?” A hankali ya ce “It’s ok” Umma ta koma ta zauna ta ce “Atoh, jidda fara ce idan aka tara mata jaa ai ba kyau zatai ba” shidai bai ce komai ba ya wuce kitchen ya hada tea sannan ya fito ya koma daki, Anty Khadija ta kalli Umma dake jera kayan cikin akwati ta ce “Umma wai fara’ar me kike tayi ne?” Umma tayi murmushi ta ce “Khadija kenan, ke bakisan idan ana son buri ya cika sai an saki fuska ba, kema dai ki lalla6ashi ku shirya, hanya daya kenan da jidda zata samu ta shiga gidansa ba wata caan daban ba” Anty Khadija ta dan ta6e baki ta ce “Ai wallahi bai isa ya auri wata caan daban ba, kisha wahalar rainonsa sannan yaje ya auri wata ta moresa” Umma ta ce “Kema dai kya fada, gara ya auri za6ina ta yadda zata bini sau da kafa mu mallakeshi” murmushi Anty Khadija tayi ta mike tana kashewa Umma ido daya ta nufi dakinsa.
Mummy ce zaune a dakin Ummi suna hira, Ummi ta sauke ajiyar zuciya ta ce “Amma tin daga ranar bai kara tashi ba” Mummy ta ce “Allah ya kara mata lpy” Ummi ta mike ta ce “Yanzu kenan Maman Jawad Abuja zasu koma?” Mummy ta ce “Haka ta tsara masa wai zasuje hutun sati biyu kafin a koma school” Ummi ta ce “Allah ya kyauta, ya kannen Jawad din?” Ta ce “Duk suna nan, sai shegen taurin kai da rashin kunya irinna uwarsu, nidai bana shiga harkarsu dan kakkarya yara ba abu me wahala bane a wajena, Jawad ne kawai me hankali a cikinsu, Sadeeq kam ba’a magana, ita kuma wancen sa’ar Rafi’an rashin kunyarta yafi karfinta, ana gobe zamu dawo ma sai da uban yayi mata dukan tsiya” Ummi dake saurarenta ta ce “Allah ya shirya mana” Mummy ta ce “Ameen” daga haka suka hau hirarsu ta yaya da kanwa.
Karfe uku Mummy tace wa Rafi’ah ta shirya zasu tafi, ta dauka handbag me dan girma tasa kayanta kala hudu aciki, Ummi dake kallanta ta ce “Kwana nawa zakiyi ne?” Ta ce “Sunday zan dawo da daddare, kwana 2 kenan” Ummi ta ce “Ki fadawa Abba dama, and make sure u don’t forget ur drugs” ta ce “To”, bayan ta gama shirya kayanta ta kira Abba ta fada masa, ya mata Allah ya kiyaye, har bakin mota Ummi ta rakasu, Mustapha ya bude motar Rafi’ah ta shiga, suna tsaye bakin motar Anty Amina ta shigo gidan, ta kauda kanta gefe tayi apartment dinta, Mummy ta bita da kallo ta ce “Ita dan kiban ma da matan manya suke ita batayi, daga ina take kuma?” Ummi ta ta6e baki ta ce “Ina zan sani Anty” Mummy ta ce “Allah ya kyauta” daga haka ta shiga motar Mustapha yaja suka bar gidan. Minti 15 ya kaisu gidan Mummy, suna horn aka bude gate din, Mustapha yayi parking suka fito sannan ya musu sallama ya juya, bin bayan Mummy Rafi’ah take har suka iso entrance din gidan, Mummy ta murda handle din ta shiga Rafi’ah tabi bayanta, Abi ne zaune a parlonsa yana kallo, ya danyi murmushi ganin Rafi’ah ya ce “Future Barrister” ta boye fuskarta tana dariya, dan bata manta sanda take haukar ita lawyer ce, har zare take daukowa tana daurawa mutane a kafa wai shine handcuff, Abi yayi dariya ya ce “Ina dai baki fasa zama barristern ba?” Zama tayi a kasa still smiling ta ce “Ina yini Abi” ya ce “Lafiya kalau Fatima, how are u and them” a hankali ta ce “Kowa lafiya” ya ce “Ya jikinki kuma?” Ta ce “Da sauki sosai” ya dan kalli Mummy ya ce “Ya kuka samesu?” Ta ce “Duk lafiya suke” tana rife bakinta mahaifiyar Jawad ta fito daga side dinta, ta wani hade rai, Rafi’ah ta ce “Ina wuni” ciki ciki ta ce “Lafiya” Mummy ta kalli Rafi’ah ta ce “Tashi ki shiga ciki Rafi’ah” mikewa tayi ta shiga bangaren Mummy, Abi ya tashi yana gyara babban rigarsa ya ce “Madam zan fita fa” ta ce “Zuwa ina?” Ya ce “Nace Sadeeq yazo muje shopping, naga ba komai ne akwai a gidan ba” ta ce “Allah ya kiyaye hanya” daga haka ta ya fita ita ma ta mike ta shiga bangarenta.
Bai fi 10 minutes da fita ba Jawad ya shigo gidan hannunsa rike phone sai car key dinsa, direct side din Maminsa ya nufa, Ikram ce kadai zaune a parlor tana kallo a system, ta dan dago kanta ta kalleshi ta ce “Sannu da dawowa Yaya” ya ce “Sannu, ina Sadeeq?” Ta ce “Sun fita da Abba” mikewa yayi zai fita yaji maganar Mami ta bayansa, ya juyo yana kallanta ya ce “I thought kin fitan ai” ta dalla masa harara ta ce “Ka sameni a dakina yanzu” daga haka ta juya ta koma ciki, kusan minti biyu yana tsaye kafin ya zura hannayensa cikin aljihun wandansa ya nufi dakin ta, yana shiga ya tura kofar ya rufe ya tsaya jikin mirror, ta ce “Sai nace ka zauna kenan?” zama yayi akan stool din dake wajen, Mami da ranta ya gama 6aci ta ce “Maimakon da ka kai matar uban naka ka dawo ka kaini saika nemi waje ka zauna” ya dago kansa yana kallanta ya ce “Naje court ne Mami, na samu urgent call around 9, Anty kuma Abi ne yasa ni na sauketa a gidan kanwanta” Mami ta ce “Ai dama kai duk inda zakai suna nan kake xua, da yace ka sauketa why not go and leave her, in yayi magana kace ka manta” a hankali ya ce “Kiyi hakuri” taja tsaki sannan ta mike, shima mikewa yayi ya ce “Zan kaiki din ne?” Ba tare data kalleshi ba ta ce “Zaman jiranka zanyi, Sadeeq dake neman lada ai ya kaini” sunkuyar da kansa yayi ya ce “Sai anjima” daga haka ya fita a dakin.
Yusuf ne tsaye gaban mirror yana gyara zaman hular kansa, farar shadda ce ajikinsa tayi bala’in masa kyau, sai kamshi yake, ya dauki key din motarsa da wayarsa ya fito a dakin, Anty Khadija ce kwance a parlor tana gyangyadi, jin kamshin turarensa yasa ta zabura ta bude ido, sai da ta saki murmushi kafin ta ce “Doctor daga nan kuma sai ina?” Ya dan kalleta sannan ya dauke kai ya ce “Somewhere” bai jira cewarta ba ya fice ya jawo mata kofar, yana zuwa parking lot yasa key ya bude motarsa ya shiga, kunnata yayi yana jira tayi warming dan yau tun safe ba inda yaje, ko sallar juma’a ma a unguwa yayi baiyi nisa ba. Jiddah ce ta shigo gidan duk a gajiye, kana kallanta kasan daga school take, suna hada ido ta saki murmushi ta karasa inda yake ta ce “Yaya sannu da dawowa” a hankali ya ce “Sannu kema” ta ce”Umma tace ka bada kudi a fara hada min lefe nago…” Kallan daya watsa mata yasa tayi shiru tana kallansa, ya ce “Akai forcing dina dai, tin farko ai nunawa sukai basa so, saboda haka nima na hakura, u go and find someone but not Yusuf” Kallansa kawai Jiddah take with expression, she’s just lost of words, nan da nan idanuwanta suka kawo ruwa ta ce “Amma kasan ina sanka Yaya, wallahi bazan iya rayuwa babu kai ba” jaan motarsa yayi ya wuce ya barta tsaye a wajen, kuka me karfi ta saki ta nufi cikin gida da gudu tana kiran Umma.
Sai da Yusuf ya tsaya yayi sallan la’asar sannan ya karasa gidan Mummy, dai dai kofar gidan yayi parking bayan ya duba house number, bayan yayi parking ya fito ya jingina jikin motarsa ya fara kiran wayar Rafi’ah, suna zaune ita da Mummy suna hira kiran ya shigo, ta mike ta dauka wayar sannan ta shiga daki, ya ce “I’m outside dear” ta ce “Alright gani nan” daga haka ta ajiye wayar ta daukar well ironed himar dinta ta saka, powder kawai ta shafa da lip stick sannan ta fito rike da wayarta a hannu ta ce “Mummy bari naje waje” Mummy ta washe baki ta ce “To ya shigo compound mana” Rafi’ah ta dan zaro ido ta ce “Kaiii Mummy class mate dina ne fa” Mummy ta ce “Hmmm, shi class mate din ba zai shigo cikin gida ba sai ya tsaya a bakin gate” ita dai Rafi’ah bata ce komai ba ta fita a parlorn, tana fitowa ta samu Ikram a parlorn Abba tana zaune, suna hada ido kowacce ta dauke kai Rafi’ah ta nufi kofar fita. Tin fitowarta Yusuf yake murmushi yana kallanta, bayan ta karaso tasa tafikan hannayenta ta rife idanta ta ce “Ni kadaina kallo na” ya danyi murmushi ya ce “U look more beautiful in hijab, kinyi kyau sosai” a hankali ta ce “Kaima kayi kyau” ya ce “Sure?” ta daga masa kai, ya ce “To ai baki kalleni ba kuma” sai lokacin ta bude fuskarta ta kalleshi sannan ta ce “Da gaske kayi kyau” ya ce “Thank u so much, how is Mummy” ta ce “She’s fine” ya ce “Khairiyya na gaisheki, she always asked for you” Rafi’ah ta dan turo baki ta ce “Ba kaki kawota ba” ya ce “Sai kinje kin gaishe da Amminta, kinga by then small mum dina ta sanki sai itama in kawota taga Antynta” Rafi’ah ta danyi mirmushi ta ce “To sai wataranan” ya ce “Allah ya kaimu, Amma wannan karan idan Abba yazo zan sameshi na fada mishi” da sauri ta ce “Me?” Ya ce “Ina neman izini a bani ke” tayi saurin rife fuskarta bata ce komai ba, ya ce “Ko wajen Mummy zan kama kafa?” Ta girgiza kai kawai tana murmushi.
Sun kai minti 30 tsaye a wajen suna hira, ita dai Rafi’ah sai uhmm ko murmushi duk shi kadai yake surutun, ya lankwashe kansa irin yadda tayi ya ce “To sai yaushe zamu sake haduwa Baby” ta kyalkyale da dariya ta ce “Aini ba haka nake magana ba” ya ce “Ko, to bari na sake gwadawa” ya dan shagwa6e fuska just like she used to ya ce “Ni dai banaso mu kara kwana 2 ban ganki ba” dariya sosai ta kyalkyale dashi harda sunkuyawa, dai~dai lokacin Jawad ya bude kofar gida ya fito, ya kura musu ido yana kallansu, Yusuf dake murmushi ya ce “Serious haka kike, and i like it” ta tsaya da dariyar da take cewa “That’s what u said dai” ya ce “Allah kuwa, sai munyi waya ko, i have to go, zan je gidan abokina” ta ce “Alright safe” Yusuf ya ce “Waye wancen?” Ya karashe maganar yana kallan inda Jawad ke zaune, suna hada ido ya hade rai ya kauda kansa gefe, Rafi’ah ta ce “Dan gidan ne” ya ce “Ohh Mummy tana da rival ne?” Ta ce “Yess, but ya fara auren Mummy kafin mamansu, shi ne babba” Yusuf ya dan daga kafada ya ce “Ohk, yanzu sai yaushe?” Ta ce “Sanda kace” ya ce “To sai munyi waya” ita da kanta ta bude masa kofar motar, bayan ya shiga ta rife sannan ta durkusa tana kallansa ta glass ta ce “Allah ya kiyaye, ka tafi very gentle” Yusuf yayi murmushi ya ce “Thank u LIFE PARTNER” ta sunkuyar da kanta tana murmushi ta matsa jikin motar tana daga masa hannu ta nufi cikin gidan. Yusuf yayi reverse yana ta dariya, yana juyawa ya dagawa Jawad hannu, dauke kansa ya sake yi ya maida gefe, bayan Yusuf ya wuce ya bi motarsa da wani irin kallon da baza’a kirashi da harara ba. Daga haka ya mike ya shiga cikin gidan, a parlorn Abi ya zauna ya kurawa TV ido, Mami ta fito tana kallansa ta ce “Kai ba abinda zaka dauka ne na tafiyar?” Ya dago kansa yana kallanta ya ce “I’m not going” Mami ta masa kallan kama isa kafin ta ce “Wannan kuma karyane wallahi, kafata kafarka a gidan nan, sai dai idan kaje Abujan kayi ta zama a daki” Tashi Jawad yayi ya fice a parlor, Mami ta bishi da harara ta ce “Wawa kawai, wallahi ba dan a gida na haifoka ba cewa zanyi canzamin kai akayi” daga haka ta koma dakinta tana dialing wayar Abi.

*I’m writing this to the notice of my fans/followers, zan bar typing daga yau sai na gama exams insha Allah.*

_08103810398_ [7/29, 6:47 AM] Zarah: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation
*_…卮乇賷賰 丨賷丕鬲賷…_*
_{MY LIFE PARTNER}_

*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*

_By FATIMA 鉁嶐煆籣

_23~24_

______________Jawad ne zaune a parlorn Abi Mami na zaune a kan kujerar dake opposite dinsa, tinda ya shigo parlorn kansa na kasa bai yarda sun hada ido da Mami ba ya zauna akan carpet, bayan Abi ya gama answering call din da yake ya dago kansa yana kallan Jawad ya ce “Why will u not follow them Ahmad? Or do u have something to do?” Ba tare daya dago kansa ba ya ce “Sure, i have alot to do Abi” Mami dake dalla masa harara ta ce “Munafikin Allah, babu wani abinda zakai a garin nan, saboda haka keep this at back your mind, wallahi saika tafi Abuja, i swear to God and i won’t regret telling you such” ta karashe maganar tana jijjiga kafarta fuskarta babu walwala, ta dinga hararan Jawad da baisan tanayi bama, Abi yayi gyaran murya yana kallanta ya ce “Iook Hadiza, i see nothing to bother in this case, is Jawad still a kid? ko Ikram bazata zauna nan ba in taga batasan tafiya ballantana Jawad? Pls u keep this issue aside, tinda yace bazai je ba let him stay” Abi na rife bakinsa ya jawo newspaper dake gefensa yaci gaba da karatunsa, kasa daina kallan Jawad Mami tayi, shima kuma yaki yarda su hada ido, caan taja tsaki ta mike ta wuce part dinta tayi banging kofar da karfi, kallan direction din Abi yayi sannan ya girgiza kai yaci gaba da abinda yake, gently Jawad ya mike yana kallan Abi d hankalinsa ke kan newspaper, kallan part din Mummy yayi, caan ya wuce dakinsa ya rufo kofa. Zaro ido Rafi’ah tayi tana kallan Mummy ta ce “Dan Allah Mummy karki gayama Ummina, nifa ba saurayina bane” Mummy dake murmushi ta ce “I can’t promise u bazan gaya mata ba, haka zamu zuba maki ido kiyi ta tsayuwa a titi da saurayi sai kace daga wancen garin muke, ai yafi kuyi hirar a gidan auranku, kince sunansa Yusuf ko?” Turo baki Rafi’ah tayi bata ce komai ba, ga kirjinta dake bugawa sosai, babban tsoronta idan Ummi taji wannan zance, ajiyar zuciya ta sauke tana kallan Mummy dake shirya kayanta cikin wardrobe ta ce “Dan girman Allah Mummy don’t let her know, Allah it won’t be good for me, zata iya dukana” Mummy ta ta6e baki tana kallanta ta ce “Sai kuma kiyi, baki isa kula samarin bane ko me da zakice zata dakeki, ni shekarata goma sha uku sanda nayi aure, duk karatun danayi a gidan mijina nayi” hawayen daya gangaro a idanta ta goge ta kara turo baki ta ce “To ai ku lokacinku haka ake, ni kuma Abba yace saina gama degree zanyi aure” ba tare da Mummy ta kalleta ba ta ce “U better wipe those tears, dan babu abinda zai hanani bashi dama ya turo magabatansa, dama faduwa ne yazo daidai da zama, kina karasa karatunki kiyi aure, idan yaso daga nan kiga karshen boko, shi kuma ubanki idan bazai aurar dake ba, inada kudin da zan iya miki komai ni kadai na, atooh in baka dashi ne saika jira an maka” Tashi Rafi’ah tayi ta fito parlor ta kwanta kan kujera tana goge hawayen idanta, imagining kawai take idan iyayenta suka saan wannan labarin, what will she even tell Abba bayan kullum burinsa tayi karatu me zurfi, taja dan karamin tsaki tana regretting zuwan Yusuf gidan Mummy.
Umma ce zaune a parlor jidda tayi pillow da cinyarta, kana kallanta kasan taci uban kuka ba kadan ba, idanta duk sun canza kala sunyi jazir, Umma ta dan shafa kanta ta ce “Nace kiyi shiru ko Jiddah?” Cike da karfin hali ta ce “Nayi Umma” daga haka tasa hannayenta ta sharce hawayen daya sakko a idanta, Umma tayi patting bayanta cikin rarrashi ta ce “Ai Jiddah idan baki auri Yusuf ba sai dai idan ba raina, ki kwantar da hankalinki duk kukan nan da kike ki daina, kuma karki nuna masa komai, aure kuma kamar anyi an gama” tashi Jiddah tayi tana kallan Umma cikin muryar kuka ta ce “Allah Umma inasan Ya Yusuf, mutuwa zanyi idan ban aure shi ba” daga haka ta rungume Umma ta fashe da kuka, Ta6e baki Anty Khadija tayi ta tashi ta haura sama, ita haushin Jiddah ma takeji har ranta musamman idan ta tuna akan Yusuf take wannan kukan.
Har dare yayi Rafi’ah bata samu tayi convincing Mummy ba, hakan yasa bugun zuciyarta ya karu, ta jawo ledan drugs dinta tasha sannan ta dake kirjinta ta limshe ido, har kusan karfe 10 tana a haka, jin an bude kofar dakin yasa ta bude idanta, Mummy ta zauna gefenta ta ce “Are u sick?” Ta girgiza mata kai kawai, Mummy ta ce “Tona menene dafe kirji? ko ciwo yake?” A hankali ta kara girgiza mata kai, Mummy ta ce “Then u stand up and take ur dinner” tashi tayi ta zauna tana yamutse ta ce “Tea kawai zan sha” Mummy ta ce “To kije ki hada a kitchen” daga haka ta fita a dakin ta koma dakinta. Sai bayan few minutes Rafi’ah ta janye duvet din dake jikinta ta sakko akan gadon, dogon hijabi ta saka saboda kayan baccin jikinta, daga haka ta fito a dakin, ba kowa a parlorn Mummy hakan yasa ta kashe faan da sockets sannan ta fita main parlor, Sadeeq ne kawai zaune a parlor yana kallo, ta danyi kasa da murya ta ce “Ina yini” a takaice ya ce “Lafiya” daga haka ta wuce kitchen, tana shiga taji kamar ta juya ta fito ganin Ikram da Jawad a kitchen din, kowa kuma harkar gabansa yake, shiga tayi ciki a hankali ta durkusa dai dai inda taga cups ta dauka guda daya da tea spoon sannan ta karasa inda taga flask ta bude zata bebi ruwan zafi, Ikram na gama juye indomie a cikin plate ta dauka tana ta6e baki ta fita a kitchen din. Sugar da milo tasa a cikin tea din, ta dinga bin kitchen din da kallo ko zata ga milk, dai dai inda Jawad ke tsaye ta hango tin din, ta karasa a hankali tasa hannunta zata dauko tin din suka hada ido, sauke kanta tayi kasa ta ce “Zan dauka madara ne” bai sake kallanta ba yaci gaba da abinda yake, ta dauki tin din ta bar wajen, bayan ta zuba ta dauka cup dinta zata fita taji ya ce “Who was that guy?” Juyowa tayi tana kallansa, yana tsaye inda yake kuma bai juyo ya kalleta ba, ta juya a hankali zata fita ya ce “Baki ji bane?” Silently ta ce “A friend” daga haka ta fice a kitchen din, har lokacin Sadeeq na zaune a parlor, Rafi’ah ta ce “Sai da safe” ya ce “Allah ya kaimu” daga haka ta shige part din Mummy.
Washegari da safe Mummy ta shiga kitchen saboda girkinta ne ranar, Rafi’ah najin ta fita ta saka hijabi ta bita suka fara aikin tare da mai aiki, Mummy batai wani aiki ba tana dai zaune tana ce musu suyi wancen suyi wancen, bayan sun kusan gamawa Rafi’ah ta kalli Mummy ta ce “Nifa anjima zn wuce gida Mummy, i have school tomorrow” Mummy ta ce “Ki bari da yamma saina saukeki idan zan fita” girgiza kai tayi ta ce “No, inasan inje islamiyya ne da yamma, kinga jiya banje ba” Mummy dake kallanta ta ce “Ko kuma saurayinkin ne zaizo?” Turo baki Rafi’ah tayi ta ce “Nifa bance ba islamiyya nace miki zanje” Mummy ta ce “Sau nawa kina fashin islamiyyar for no reason, zaki wani fake zakije islamiyya” Ita dai bata ce komai ba banda hade rai da tayi, Hindatu me aiki nata dariya kasa kasa. Bude kofar kitchen din akayi Mami ta shigo, fuskarnan a daure ko walwala babu, sai data dauki abinda zata dauka tazo fita ta ce “Mun kwana lafiya?” Mummy ta ce “Alhamdulilah”, abinda yake hadasu kenan a gidan, shima gaisuwan Abi ne yasa Mami tana gaishe da Mummy each and every day, wani lokaci ko Mummy tai mata magana sai taga dama take amsawa, hakan yasa itama tayi watsi da ita dan ita bata iya daukar rainin hankali. Bayan sun kammala komai aka jera akan dinning din Abi, Mummy tasa Rafi’ah ta dibar musu nasu a warmer, plate da cups Mummy ta dauko zata wuce part dinta, Jawad da fitowansa kenan yayi kasa da kansa ya ce “Ina Kwana” ta ce “lafiya Jawad, ya gajiya” ya ce “Alhamdulilah” daga haka ta wuce ciki, Mami sai hararansa take, bayan ta gama dibarwa Ikram abinci ta wuce part dinta ta rufo kofa, Jawad ya dawo kan dinning din ya zauna yayi sarving kansa ya hada tea, sai daya gama sannan ya mike ya nufi part din Maminsa, da sallama ya shiga parlor, Mami ta hade rai ganinsa taci gaba da bawa Ikram tea a baki, zama Jawad yayi yana kallansu ya ce “Take it yourself” ya karashe magana yana kallan Ikram, hannu tasa zata kar6i cup din a hannun Mami, Mami ta ce “Ina ruwanka to? Kai ka sani na bata?” Girgiza kai yayi yana kallanta ta ce “Then u mind ur words, babu ruwanka da abinda nayi niyya a cikin gidan nan” kansa ya kara saukewa kasa ya ce “Amma Mami yanzu Ilkram bazata sha tea da hannunta ba saikin bata, just because ta tashi da zazza6i, ita raguwar inane? shekara 17 fa” Hararansa kawai Mami take harya gama magana, ta ce “To saika hanani abinda nayi niyya tinda kaika haifeni, ko kishin uwarka bakayi ka bude baki ka gaishe da waccen matar, kana gani ‘yar kanwata na ganina ina zirya ko sannu bata ce min ba, amma saboda kai kafi kowa ladabi ka gaishe da uwarta” shiru yayi baice komai ba, bayan few seconds ya ce “Kiyi hkr, amma dai kun fasa tafiya yau din?” Ta ce “Inafa tafiya Ikram ta tashi ba lafiya” a hankali ya ce “Allah ya sauwake” Mami ta ce “Yanzu ina zakaje?” silently ya ce “Court” ta ce “Saboda neman suna ko me?” Ya mike yana kallanta ya ce “May b i will just continue my work there, tinda sun bukaci hakan” ta6e baki tayi ta ce “A banza zaka musu aikin kenan?” Ya shafa kansa ya ce “No, ai dama sunce inna dawo zan iya ci gaba kona nema wani waje, end of d month zanci gaba da kar6an salary” beedsheet ta rufawa Ikram ta ce “Allah ya taimaka, Allah kuma yasa da gaske kake, danni yanzu lamuranka tsoro suke bani” murmushi ya danyi ya fita a parlorn ta bishi da harara.
Fitowa yayi a dakinsa cikin manyan kaya, sai kamshi yake ya dauka lab coat dinsa dake kan kujera ya daura akan kayansa, kaan dinning ya zauna yaga babu komai cikin warmers din, hakan yasa ya mike ya shiga daki ya dauko wasu files sannan ya nufi kofar fita hannunsa rike da key din mota, da sauri Jiddah tabi bayansa tana murmushi ta ce “Good morning Ya Yusuf” juyowa yayi yana kallanta ya ce “Morning Jiddah” idanta ne ya ciko tapp da hawaye, tayi kasa da murya ta ce “Dan Allah Yaya mena maka kace ka fasa aurena, ka fadamin koma menene Allah zan daina, i promise u Yaya” ta karashe magana tana goge hawayen idanta, duk jikinsa sai yayi sanyi, shima Allah na gani yana saan Jiddah but tinda Umma taki yarda tun farko ya janye jikinsa, hannunta ya kamo ya bata side hug ya ce “Keep quite” tayi shiru tana kwantar da kanta akan fadarshi taji ya ce “I luv u Jiddah, but i don’t like some of ur attitude sometimes” dago kanta tayi tana kallansa ta ce “Na daina Yaya trust me” ya danyi murmushi ya ce “Then zaki aureni?” Ta daga masa kai ya ce “Kinyi alkawari bazaki kara yin abinda na hanaki ba?” Ta kara daga masa kai, ya sake murmushi yana kallanta ya ce “Kenan kinyi alkwari zaki zauna da wacce zan hadaku, but u are my first wife, she will come after u” turo baki ta danyi sannan ta daga masa kai, yayi patting bayanta ya ce “Then stop crying” zame jikinta tayi ta koma cikin gida ya bita da kallo, daga haka ya juya ya wuce parking lot. Da yamma liss Mummy ta sauke Rafi’ah a gida, bayan sun shiga duk da sauri take sai data labartawa Ummi Rafi’ah nada saurayi, Ummi batai wani mamaki ba sabida taga yadda take making calls, sai dai bata ce komai ba, Mummy ta mike tana kallanta ta ce “Na tilasta mata dai ta bani numbersa, tinda gobe ubanta zaizo sai a kirashi yazo suyi magana” kai kawai Ummi ta daga mata, daga haka ta rakata har paking lot kafin ta dawo ciki.
Har dare Ummi bata cewa Rafi’ah komai ba, ita kuwa tinaninta kawai aiki ne ya mata yawa saboda taga tana ta marking, bayan sallan isha ta sakko downstairs daga ita sai ‘yar rigar baccinta iya gwiwa, kanta ba dankwali hannunta rike da phone dinta, tana zama ta kalli Ummi ta ce “Gobe Abba da wuri zai iso ko sai caan yamma?” ba tare da Ummi ta kalleta ba ta ce “Sai ki kirashi ki tambayeshi” ta dan turo baki ta ce “Amma Ummi ai zai gaya miki” tana rife bakinta phone dinta ya hau ringing ta kalli screen din tayi murmushi ganin Yusuf ne, daga haka ta mike ta wuce upstairs Ummi ta bita da harara. Cikin cool voice dinsa yayi mata sallma ta amsa, ya danyi murmushi ya ce “I am happy Babyluv, and it’s all because of u” zama tayi gefen gado ta ce “What hapoend Dr” ya limshe idanuwansa kamar tana kllansa ya ce “Mummy just called me, tace Abba zai dawo gobe around 12 na rana” Rafi’ah ta dan zaro ido ta ce “Then what?” Yusuf ya ce “I will come and see him insha Allah, tace min ta mishi magana” kamar zatai kuka ta ce “Pls ka bari ba yanzu ba Dr” Yusuf yayi murmushi yayi hanging call din, dama kawai he just call to let her know, tashi tsaye tayi ta fara zagaye dakin, duk tabi ta rikice, wayarta ta dauka tayi dailing number Mummy taji not reachable, ta kara kiran na Yusuf still d same thing, kwanciya tayi akan carpet ta rasa ta ina zata fara tsayar da Yusuf, Allah na gani batasan hukuncin da Abba da zai dauka ba, jin an bude kofa tayi surin rife idanuwanta kamar me bacci, Ummi ta shigo ta dauko wasu takardu kan stool sannan ta fice a dakin, Rafi’ah ta sauke jiyar zuciya ta mike zaune ta buga uban tagumi.

*Thank u so much for the calls and du’ah, ubangiji Allah ya biya maku bukatanku na alkhairi aduk inda kuke, i so much appreciate the way u people cares, especially when reading ur messages, na gode sosai da sosai* 馃グ
[7/29, 6:47 AM] Zarah: *_…卮乇賷賰 丨賷丕鬲賷…_*
_{MY LIFE PARTNER}_

*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*

_By FATIMA 鉁嶐煆籣

_25~26_

Washegari da safe Ummi na kitchen Abdul ya shigo cikin shirinsa na makaranta, ya dafa kafadarta ya ce “Good morning mother” ta ce “Morning, how are u?” Ya ce “Fine” Ummi ta ce “Go and take your breakfast” ya ce “Anty bata fito ba Ummi? And It’s almost time” Ummi ta juya ta fita a kitchen din bata ce komai ba, upstairs ta wuce ta shiga dakin Rafi’ah, ta sameta gaban mirror ta gama shirinta tana zaune da dan karamin hijab dinta a hannu, strictly Ummi ta ce “Idan baza kije school din ba Abdul yayi wucewarsa” ta mike a hankali tana kallan Ummi ta ce “Na gama” Ummi ta ce “If u like keep sitting” daga haka ta fita a dakin taja mata kofar. Kamar wacce bata da jini ta zira hijabin sannan ta dauka school bag dinta, har zata fita taga phone dinta dake kan gado tana haske, dago wayar tayi tana kallan screen din, ta6e baki tayi ta kashe wayar ta jefa cikin press hade da jaan karamin tsaki. Tana saukowa downstairs ta samu Abdul har ya gama breakfast dinsa, ta ajiye school bag dinta sannan ta zuna ta hada tea ta fara kur6a, kana kallanta kasan a dole take sha, duk abinda take Ummi na kallanta sai dai bata ce komai ba, bayan tasha half ta mike ta haura stairs ta shiga dakinta, phone dinta ta kunna sannan tayi dailing number Yusuf, yana dagawa ya ce “Why are u not picking my calls Fatima?” Cikin fishi ta ce “Pls don’t come to my house i beg u, dan Allah karka zo, i’m begging u for the sake of Allah Dr” fashewa da kuka tayi bayan ta dasa aya, Yusuf dake saurarenta ya danyi murmushi ya ce “But do u want me to break the promise i made to ur Mummy? Or what do u want me to do? so kike nace bazan zo ba kenan, she will take me non serious Rafi’ah, maganar neman aure fa ba wasa bane” sassauta kukanta tayi ta ce “Dan Allah karka zo nikam, if not i will pretend i don’t know u” shiru yayi na few seconds kafin y ce “It’s ok, bazan zo ba, nasan abinda zance mata, stop crying and wipe ur tears” tayi shiru tana goge idanta da bayan hannunta, ya ce “Kin goge?” Ta daga masa kai, ya ce “Baza kije school bane?” Silently ta ce “I’m going now” ya ce “Ohk safe, say your du’ah and cool down your heart, babu abinda zai faru” ta danyi shiru sai kuma ta ce “Ba kace ka fasa zua ba?” Ya ce “To kije school idan kika dawo zamuyi magana” ta ce “Ohk” daga haka tayi hanging wayar ta ajiye ta fito, tana saukowa a stairs taji Ummi na cewa Abdul “Ku tafi abinku, idan yaso ta hau cab” turo baki tayi bayan ta karaso ta dauka school bag dinta da 500 din da Ummi ta ajiye mata a gefen jakar sannan ta fice a parlorn.
Da sauri da sauri Anty Amina ta tattara magungunan da suka kar6o wajen malaminsu tasa a handbag dinta, duk ta haddace yanda akace tayi, Ikleemah dake kallanta ta ce “Wai Anty Amina tafiya zakiyi?” Ta ce “Ai ina wanka tafiya zanyi ikee, kinga yace da wuri zai taso, jirginsu karfe 9 zai tashi, to ina Abuja ina Kano a tafiyar jirgi” Ikleemah ta mike ta ce “To kona biki ne?” Anty Amina ta ce “Tambayi uwarki idan zata barki, banaso muje tayi ta damuna a waya ki koma, idan zama zama” Ikleemah ta kalli mahifiyarta dake zaune gaban TV, Ikleemah ta ce “Mami bazan bita bane?” Anty Rahama ta ce “Idan kinaso, ni Umma nakeji idan kika tafi, inna fita ita kadai kenan zata zauna” jin haka yasa Anty Amina ta dauki handbag dinta ta shige dakin Umma dan tasan dama ba bari zatai taje ba sai dai idan Umma tayi magana. Tinda Rafi’ah taje school zuciyarta ke bugawa, gashi dai Yusuf yace bazai zo ba amma duk jinta take wani iri, babu yadda Ameerah batai ba amma taki fadin abinda ke daminta, koda akai break a class ta zauna bata fita ko ina ba, ana tashi kuwa Mustapha yazo daukansu, Abdul dake kallanta ya ce “Are u sick Anty?” Ta girgiza kanta ta shiga mota, Mustapha yaja motar yana murmushi ya ce “Hajiya karama Abba ya iso tin sha biyu saura” da sauri ta dafe kirjinta ta ce “Ai nasan zai zo” daga haka ta kwanta ta limshe ido, suna isa gida yayi parking a waje ya ce “Hajiya ta aikeni kasuwa, amin afuwa” Abdul ya ce “Ba komai” Rafi’ah ta dauki school bag dinta ta fito tabi bayan Abdul, ba kowa a parlorn da suka shiga, Abdul ya fara hawa stairs itama tabi bayansa, da sallama Abdul ya shiga parlorn, Ummi ta amsa masa, ya karasa gefen Abba yana murmushi ya ce “Sannu da hanya Abba” Abba ya kama hannunsa yana murmushi ya ce “How are u Son, ya karatu?” ya ce “Lafiya kalau Abba” ciki ciki tayi sallama ta shigo parlorn, kasa zuwa ta rungume Abba tayi just like she used to, ta zauna gefen Ummi kanta a kasa ta ce “Sannu da dawowa Abba” ya danyi murmushi yana kallanta ya ce “How are u Mamana?” a hankali ta ce “Fine” daga haka ta mike ta wuce dakinta. Bayan Abdul yayi sallan azahar ya dawo wajen Abba sukai ta hira, Ummi ta mike ta shiga dakinta saboda bacci da takeji, Rafi’ah dai tinda ta kule a daki bata fito ba har akai la’asar, jin ba muryar su Abba yasa ta fahimci sun fita masallaci, kamar 6arauniya ta sauko downstairs ta debi abinci sannan ta dauki bottle water ta koma sama da sauri, tana gama hawa suka hada ido da Ummi dake tattara cushions tana daurawa kan sofa, sauke kanta tayi ta shiga daki ta rufe kofarta. Ummi ta zauna akan kujera tana kallan TV, ba jimawa Abba yayi sallama, Ummi ta amsa tana kallansa, zama gefenta yayi yana kallan TV ya ce “Halima ta kirani wai yaran nan me neman Rafi’ah zaizo, shine ya kirani yanzu” Ummi ta juyo da sauri tana kallansa, dama tin dazu take jira ya mata maganar baiyi ba, with surprise ta ce “Zaizo kuma?” Abba ya ce “Eh, tinda ya bukaci hakan ai baza’ayi discouraging dinsa ba, let him come” Ummi ta ce “Kenan dai aurar da Rafi’ah za kai yallaboi” ya ce “Idan har nayi bincike na gano ba matsala why not? Tinda da bata sanshi ba zata hadashi da wani nata ba” Ummi ta sauke ajiyar zuciya ta ce “Ni gaskiya i’m not in support, ina laifin idan ta gama secondary school, saurin me ake shekarunta fa 17 ne kacal a duniya” Abba ya juyo yana kallanta ya ce “I know she’s 17, kinga Zainab a zamanin nan idan yarinya ta nuna aure takeso then let her, dan bamusan me zai faru ba Allah ya kiyaye, and I’m not saying zan aurar da ita immediately, no..till when she finish her secondary school” Ummi bata ce komai ba sai ajiyar zuciya data sauke, bayan mintuna kadan Abba ya mike yana kallanta ya ce “Bari na shiga apartment din Amina kafin ya karaso” ta ce “A dawo lafiya” daga haka ya nufi downstairs.
Tashi Ikleemah tayi daga kwancen da take ta fito parlor, ta buga uban hamma tana kallan Anty Amina ta ce “Anty ki bani 500 dan Allah naje shago” Anty Amina ta ce “Uban me zaki siyo harna dari biyar Ikee? Ni kinga duk kudadena sun kare, kwanakin da nayi a gida duk uwarki ta yasheni, saboda haka bani dashi” Ikleemah ta ta6e baki ta ce “To bani 200, kati fa kawai zan siyo dan Allah” Anty Amina ta juyo tana kallanta ta ce “Ke nima 200 ce daukeni ki siyo katin” tana rife bakinta Abba ya shigo, hakan yasa Ikleemah ta shige daki tana kunkuni.
Tsaye yake gaban mirror yana daura wristwatch dinsa a hannu, sosai yayi bala’in yin kyau sai kamshi yake, bakin yadi ne ajikinsa me laushi, ko a ido ka kalla kasan me tsada ne sai wane da wane, kayan sun matukar kar6enshi kasancewarsa farine shi tass, kallan gashin kansa yayi yana murmushi, raban da ya rage gashin kansa kusan shekara kenan, sai dai ya taje ya shafa mai, amma yau shine yaje aka rage masa gashi, sai ya ga ya kara kyau ma, key din motarsa da phone dinsa ya dauka sannan ya zira well purnished half shoes dinsa, ba kowa a parlor dan duk mutanen gidan na sama, ya fita ya jawo musu kofar sannan ya wuce parking lot ya bude motarsa ya shiga, yana horn gateman ya bude mishi ya fice a gidan. 10 minutes ya kawo shi cikin GRA, ya duba street name din to confirm ko layin ne, daga haka ya danna kan motar cikin layin, gida biyu ya wuce kafin ya fara tinanin na ukun ne kona hudu, ya dinga kallan gate din ko zaiga an fito amma shiru, hakan yasa ya bude motar ya fito yayi knocking gate din, mutumin na budewa Yusuf ya ce “Sannu Baba, dan Allah tambaya nake” mutumin ya ce “Allah yasa na sani yaro” Yusuf ya ce “Gidansu Abduljalal nake nema, nasan dai nan layin ne amma kuma ban gane gidan ba” mutumin ya ce “Allah sarki kace gidan Alhji Muhammad, yana da yarinya wata fara doguwa me suna Rabi’ah ko?” Yusuf ya danyi murmushi jin yace Rabi’ah ya ce “Nan ne Baba” kamo hannunsa Mutumin yayi ya nuna masa next house ta dayan side din ya ce “Ga caan gidan yaro” Yusuf ya zira hannu a pocket dinsa ya ciro 2k yasa masa a hannunsa ya ce “Godiya nake Baba” cike da fara’ah Mutum ya ce “Na gode yaro, ubangiji ya biya maka bukatunka na alkhairi” “Ameen” kawai yace ya shiga motarsa ya karasa bakin gate din su Rafi’ah yayi parking, fitowa yayi walking slowly sannan ya karasa gate din yayi knocking, Mustapha ya bude kofar yana kallan Yusuf, hannu ya mika masa ya ce “Nazo wajen Abba ne” Mustapha ya ce “To bari a sanar masa” daga haka ya juya ya nufi apartment din Anty Amina. Ikleemah ya samu tana zaune a balcony tana danne dannen waya, Mustapha ya ce “Dan Allah ‘yammata kicewa Alhaji ana sallama dashi a waje, idan ya tambaya kice saurayi ne, me farar mota” Ikleemah ta mike ta bude kofar falon, bayan ta shiga ta tsaya bayan kujera ta ce “Abba wai ana sallama da kai” ya juyo yana kallanta ya ce “Waye?” Ikleemah ta ce “Mustapha dai yace saurayine me farar mota” Abba ya mike yana duba phone dinsa ya ce “And he didn’t call me, je kice ya shigo a kaishi parlon BQ” Ikleemah ta juya ta fita bayan ta amsa da “To”. Kallansa Anty Amina tayi ta ce “Ko wanda kuka dauka aiki ne? Wanda ka bani labari” Abba ya ce “No, wannan wanda yake neman Rafi’ah ne” Wani katon abu ta hadiye hade da zaro ido bata dai ce komai ba, Abba ya fita a parlorn bayan yasa takalmansa.
Har bakin gate Ikleemah taje tace wa mustapha Abba yace a kaishi BQ, Mustapha ya bude kofar yana kallan Yusuf dake jingine jikin mota ya ce “Oga yace ka shigo” Yusuf ya shigo yana kallan Mustapha ya ce “Nagode fa” Mustapha nata washe baki ya ce “Bismillah” daga haka Yusuf ya fara binsa a baya, juyowa Ikleemah tayi suka hada ido da Yusuf, sai da kirjinta ya buga ganin yadda yayi kyau, ta dan saki murmushi ta juya, sai kuma ta fara tafiya slowly har suka iso dai dai da ita, ta sake kallansa cikin iyayi ta ce “Ina yini” ya ce “Lafiya kalau” daga haka ta shige apartment din Anty Amina, har bakin kofar parlorn Mustapha ya rakashi ya ce “Nan ne, zaka iya shiga” Yusuf ya gyada masa kai sannan ya murda handle din a hankali hade da sallama, Abba ya amsa shi cike da fara’ah ya ce “Bismillah”, kan carpet ya zauna kansa a kasa ya ce “Ina yini Abba” Abba ya ce “Lafiya kalau, ya aiki” Yusuf ya ce “Alhamdulilah ka iso lafiya?” Abba ya ce “Lafiya kalau”, shiru ne ya biyo baya, Abba ya kira layin Ummi bayan ta dauka ya ce “A kawo abinsha BQ” daga haka yayi hanging wayar, Abba na murmushi ya sake kallan Yusuf ya ce “Your name” Yusuf ya kara kasa da kansa ya ce “Sunana Yusuf”,
Ikleemah na shiga parlornsu dama ta samu Anty Amina jikin window tana leken wanda zai wuce, Ikleemah ta zauna gefenta ta ce “Naga halittar ubangiji Anty, kinga kyansa kuwa?” Anty Amina ta ce “Ni dama nasan wannan santa yake” Ikleemah ta ce “Kinsan shi Anty? Wallahi na kamu da san shi” Anty Amina ta ce “Saurayin Rafi’ah ne, taab ai wallahi ba zatai auren jin dadi ba, sai tayi auran wahala tazo tana rokona na sammata abincin da zasu ci” Ikleemah dake kallanta ta ce “Anty wallahi kyakkyawa ne” Anty Amina ta ce “Yanzu tashi na hada miki fruits ki kai masa” cike da murna Ikleemah ta ce “Yauwa Anty, zan kare masa kallo” daga haka tabi ta zuwa kitchen.
Gajiya Ummi tayi da jiran Rafi’ah ta tashi ta haura sama, tana nan ta dukunkune a karshen gado tana rera kuka, Ummi ta dalla mata harara ta ce “Idan bazaki kai ba sai ki tashi kije ki fadawa Abban cewar baza ki iya ba” cikin kuka ta ce “Allah Ummi ni bazan iya ba, ni dai ki bawa wani ya kai” Ummi ta ce “Ni kikeso naje na kai kenan? Ai iyayin dayasa kika bari Anty Halima tasan shi, shi zaisa ki dauki hijab dinki ki kai masa ruwan sha” daga haka Ummi ta fice a dakin, Tashi Rafi’ah tayi ta leka ta window dinta ta hango motar Yusuf, hakan yasa ta kara fashewa da kuka ta zube a wajen, Ummi ne ta bude dakin ta dawo rike da wayarta yana ringing ta mikawa Rafi’ah ta ce “Sai ki fada masa bazaki kai ba” daga haka ta ajiye mata a kan gado ta fita. Tashi tayi a hankali ta shiga toilet ta wanke fuskarta sannan t fito ta bude press dinta ta dauko gogggen himar dinta har kasa tasa akan gown din jikinta,
Sai sauke ajiyar zuciya take ta sauko downstairs, Ummi ta nuna mata babban tray akan dinning ta ce “Gashi caan ki dauka” Rafi’ah ta dinga kallan kan tray din ganin drinks har kala 4 sai kankana a yayyanke cikin dan bowl da pineapple sai Apple a gefe, turo baki tayi ta dauka ta fita a parlorn Ummi ta bita da kallo harta fita.
Murmushi Abba yayi bayan ya gama sauraron meaningful words din Yusuf ya ce “Amma iyayanka ‘yan nan garin ne?” Yusuf ya ce “Ehh, sunan mahaifina Muhammad saraki, amma Allah ya musu rasuwa shida mahaifiyata shekara 7 kenan, akwai dai kanwar Mamana a unguwar Rimi, yanzu dai ina zaune ne wajen kanwar mahaifina da suke uba daya” Abba ya girgiza kai looking so sad ya ce “Allah ya musu rahama” Yusuf ya ce “Ameen”.
Rafi’ah na zuwa dai dai apartment din Anty Amina Ikleemah ta fito rike da tray itama, fruits salad ne a gefe sai fanta da glass cup, Rafi’ah ta dalla mata harara ta wuce, itama harara ta dalla mata tabi bayanta, ajiye tray din Rafi’ah tayi ta bude kofar parlorn, Ikleemah ta shige da sauri, harara Rafi’ah ta bita da shi, daga haka ta dauka tray dinta ta shiga da sallama, a gefen Yusuf ta samu Ikleemah ta zauna wai tana gaishe shi, ta dire tray din hannunta ta juya ta fice a parlorn Yusuf ya dan saci kallanta, bayan sun gama gaisawa da Ikleemah ta mike tana ta rangwada ta fita a parlorn itama. Abba ya ce “Bismillah son, ga abinsha da abinci” Yusuf yayi kasa da kansa yana murmushi, bayan few seconds Abba ya ce “Kace kana aiki a Aminu kano TH ko?” Yusuf ya ce “Ehh” Abba ya danyi shiru kafin ya ce “But kasan class din da take a school?” Ya dirgiza kai, nan kwa yasan a SS2 take , Abba ya ce “To tana SS2 yanzu, sannan koda zatai aure sai ta gama secondary school, na kuma maka alkhawarin in har na gama bincikena zan baka auran Rafi’ah but on one condition” sai lokacin Yusuf ya kalli Abba sannan ya maida kansa kasa, Abba ya ce “Zata ci gaba da karatunta a gidanka” Ajiyar zuciya Yusuf ya sauke ya ce “Insha Allah Abba, nayi alkawari” Abba ya ce “To masha Allah, Allah yayi albarka, bari na amsa waya”
Yusuf ya ce “To Abba” daga haka Abba ya mike ya fita. Rafi’ah na komawa apartment dinsu ta wuce dakinta taci gaba da kukanta, abinda yake kona mata rai yadda Ikleemah keta washe baki tana kallan Yusuf, sannan shima yace mata bazai zo ba ya tashi ya zo, tana tina wadannn abu biyun saita fashe da kuka.
Har Abba y gama making calls dinsa ya shigo Yusuf ko abu daya baici ba, Abba ya ce “Baka ci komai ba Son” ya dan girgiza kai ya ce “I’m full Abba, na gode sosai Allah ya saka da alkhairi” Abba ya ce “Ameen, a huta gajiya” daga haka Yusuf ya fita a parlorn, very gentle ya dinga tafiya harya iso gate ya fita, ya shiga motarsa ya mata key ya bar layin, sai murmushi yake, kana kallansa kasan he’s so happy.
[7/29, 6:47 AM] Zarah: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation
*_…卮乇賷賰 丨賷丕鬲賷…_*
_{MY LIFE PARTNER}_

*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*

_By FATIMA 鉁嶐煆籣

_27~28_

Washegari bayan sallan asuba Rafi’ah ta sauko downstairs ta shiga kitchen, yunwa takeji bata wasa ba, dan rabanta da abinci tin jiya data dawo a school, cup ta dauka ta debi ruwan zafi sannan ta hada tea, ta bude fridge ta dauko bread ta zauna kan kujera ta fara sha, bayan ta gama ta dafa indomie tasa a warmer sannan ta koma upstairs, tana kokarin bude dakinta Ummi ta fito, ta dan sunkuyar da kanta ta ce “Ina kwana” Ummi ta ce “Lafiya, what did u want for breakfast?” Dago kanta tayi tana kallan Ummi ta ce “I already cooked indomie” Ummi ta ce “To aje a shirya” wucewa tayi cikin dakin tana fadin “Insha Allah”. Yusuf ne zaune a parlor yana shan tea, sai kiran number Rafi’ah yake amma taki picking, ya danyi murmushi ya ajiye phone din a gefensa dai dai nan Jiddah ta sauko da plate a hannunta, sai side bag dinta da laptop, ta ajiye plate din akan dinning ta karasa gefensa ta zauna, juyowa yayi yana kallanta ya ce “Good morning madam” ta dan kalleshi ta ce “Ina kwana” ya ce “Lafiya, jiya baki tsaya munyi hira ba why?” Ta6e baki tayi ta ce “Bayan kai kake bani labarin waccen yarinyar” Yusuf ya dan zaro ido ya ce “To kiyi hkr, yanzu dai yaushe zamuje gidansu ku gaisa” ta dalla masa harara ta mike ta ce “Ba dai dani ba” kamo hannunta yayi ya ce “Dake mana, bari na gaishe da Umma sai mu fita na ajiyeki a school” ta danyi murmushi tana kallansa, shima din kallanta yake, ya sauke murya kasa a hankali ya ce “U look beautiful Jiddah” ta dan boye fuskarta a bayan laptop ta ce “Kaima kayi kyau Yaya, but jiya kafi kyau” sake hannunta yayi yana murmushi ya ce “U wait me here” daga haka ya wuce upstairs. Da sallama ya shiga dakin Umma, tana zaune gaban mirror taci tsadadden lace, sai powder take shafawa, ta juyo tana kallansa ta ce “Yauwa Yusuf dama yanzu nake cewa Khadija ta maka magana kafin ka fita” zama yayi yana kallanta ya ce “Ina kwana Umma” ta ce “Lafiya kalau, zanje gidan Hajiya Saratu, idan ka tashi a aiki ka biya ka daukoni” a hankali ya ce “To, kenan bada mota zaki fita ba?” Ta ce “Ehh, Khadija zata saukeni yanzu” ya ce “To insha Allah” daga haka ya mike ya fita a dakin. Yana saukowa ya samu Jiddah tsaye tana jiransa, ya dauka key dinsa da lab coat yana kallanta ya ce “Let’s go” daga haka tabi bayansa suka fita, hira sosai Jiddah ke masa har suka iso school dinsu, yayi parking yana kallanta ya ce “Study hard Jiddah” ta danyi murmushi ta ce “Insha Allah Yaya” daga haka ta daga masa hannu ta fita a motan. Sadeeq ne ya fito a part dinsu yana jaan trolley, ya dan kalli Jawad dake zaune shiru a parlor ya ce “Good morning” Jawad ya dago yana kallansa ya ce “Morning” daga haka ya limshe idanuwansa ya jingina kansa jikin sofa, bayan few seconds Ikram ta fito, ta dan tsaya tana kallan Yayansu kafin a hankali ta ce “Yaya” bude idanuwansa yayi yana kallanta ta ce “Ina kwana” ya ce “Lafiya, how are u feeling?” Ta ce “Naji sauki, Mami tace ka sameta a ciki” da kai ya amsa mata sannan ta koma ciki, ya mike ya shiga part dinsu hade da sallama, a parlor ya samu Mami tana ta zuge Jakar kayanta, ya zauna yana kallanta ya ce “Gani” bayan ta gama zuge jakar ta dago tana kallansa ta ce “Dama na yanke shawara ka koma gidan Kawu Audu kafin na dawo” ya dago da sauri yana kallanta ya ce “Why Mami?” Ta masa wani kallo ta ce “Is an instruction i’m giving u Ahmad, idan ka dama ka tsallake karka bi” ya sauke kansa kasa baice komai ba, Mami ta ce “I’m just spending two weeks there, idan ka tattara kayanka ka tafi banasan ka sake lekowa gidan nan sai idan na dawo, dan ba zaka zama driver din matar ubanka ba” ba tare daya dago kansa ba ya ce “But what if Abi call me” harara ta galla masa ta ce “Wannan kuma ya rage naka” daga haka ta mike tana gyara zaman sarkan Gold dinta ta yafa veil dinta ta fito, jawo trolley dinta yayi yabi bayanta har zuwa parking lot, Sadeq ya kar6a yasa a boot, karasawa yayi wajen motar yana kallan Mami ya ce “Allah ya tsare” ta ce “Ameen” Ikram na kallansa ta ce “Yaya till we come back” ya daga mata hannu sannan ya koma cikin gida bai tsaya yaga tafiyarsu ba. Da yamma Rafi’ah na shigowa dakinta ta ga phone dinta na haske, ta dago wayar tana kallan screen din, ganin Yusuf ne tayi dan karamin tsaki ta ajiye wayar, daukan laptop tayi ta fito a dakin, ta zauna kan kujera tana kallan Ummi ta ce “Abba yace idan anyi hutu zan bishi Abuja” Ummi ta kalleta kafin ta ce “Ba inda zakije” dan zaro ido tayi tana kallan Ummi ta ce “Nifa ba ruwana da matarsa, kawai inasan zuwa ne” ba tare da Ummi ta kalleta ba ta ce “Waya ce maki tare zasu koma?” Ta bude hannayenta alamar bata sani ba ta ce “Kawai nayi tinanin tare zasu koma ne” Ummi ta dan harareta ta ce “Saboda ke kika haifeshi ko?” dariya ta farayi ta ce “To ai dama ni mamanshi ne” Bude kofar parlorn akai Abdul ya shigo da sallama, Ummi dake kallansa ta ce “Why are u in a hurry?” Ya wuce dakinsa da suri ya ce “Ummi akwai match” Rafi’ah taja tsaki ta ce “Akwai wahala dai, wahalalle kawai” da shirinsa na zuwa ball ya fito, sai kamshi yake kayan kuma sun masa kyau ba kadan ba, Rafi’ah ta ce “Yanzu zai dawo duk doyi” ko kulata baiyi ba ya dauka table water a fridge ya fice, few minutes da fitansa Mustapha yayi knocking, Ummi ta ce “Waye?” Mustapha ya ce “Nine Hajiya, wai Yusuf ne yake sallama da Rafi’ah” sosai kirjin Rafi’ah ya buga, ta dan zare ido tana kallan Ummi kafin ta sauke kanta kasa, Ummi ta ce “Kace tana zuwa” Mustapha ya amsa da toh sannan ya juya, kallan Rafi’ah Ummi ta sakeyi for the second time ta ce “Wa kika cewa Yusuf zaizo yau?” Ta dan kara zare ido ta ce “Wallahi Ummi i don’t know he’s coming, nima bansan zaizo ba” Ummi ta mike ta ce “This should be the last, banasan haka, idan zaizo u let me know” a hankali ta amsa da toh, Ummi ta ce “Sai ki tashi kije ai” ta mike duk jikinta a sanyaye ta haura sama, wayarta ta dauka taga 16 missed call dinsa sai text messages guda 5, ajiye wayar tayi ta dauka veil dinta ta yafa sannan ta sauko, walking slowly ta fita a parlor tana turo baki harta fita gate.
Yana tsaye jikin motarsa yayi folding hannayensa, har ta karaso ta tsaya a gefensa murmushi yake, ya sauke ajiyar zuciya ya ce “Thank God u came out, how are u Baby?” ta juya kanta gefe bata ce komai, ya ce “Pls talk Fatima, or have i wronged you?” Juyowa tayi ta dalla masa harara, Yusuf ya shafa gashin kansa yana kallanta ya ce “Did..u just eye me Rafi’ah?” ta sake jujjuya idanuwanta tana turo baki, ya ce “Ohk, if that would cool your heart keep eyeing me” shiru tayi bata ce komai ba sai jujjuya ring dinta take, ya danyi murmushi ya ce “Kin gama hararan nawa kuma kin hakura?” ta daga masa kai, ya ce “Good, how are u then?” girgiza kanta ta hauyi a hankali, nan da nan idanta ya ciko da ruwa, Yusuf ya ce “What happened again Rafi’ah, or are u sick?” Ta girgiza masa kai ta ce “I’m not sick, is just u that offended me yesterday” zaro ido Yusuf yyi yana kallanta ya ce “But u just finished eyeing me, ba kin rama ba” ta turo baki tana goge hawayen idanta ta ce “To dan meyasa kake kallan Ikleemeh data kai maka abinci” with surprise Yusuf yake kallanta, ya ce “Who’s she?” Ta ce “Jiya bata kai maka abinci ba” har lokacin kallanta yake da mamaki ya ce “To kiyi hakuri insha Allah i promise i won’t smile at her again” kanta na kasa tana ta jujjuya ring dinta, ya ce “To kimin murmushi” ta noke kafada, ya ce “Dan Allah Rabi’ah ta” ta dago tana kallansa ta ce “I’m not Rabi’ah” ya danyi dariya ya ce “Haka wancen mai gadin yace min, wai sunanki Rabi’ah” sai lokacin ta danyi murmushi ta ce “That’s how he used to call me” ya ce “Then can i contribute” ta kara dariya ta ce “So u want us to fight again?” Yusuf yayi dariya ya ce “Noo, and we are not fighting Allah ma ya kiyaye” a hankali ta ce “Ameen” tana dariya. Zaune yake a parlor yana ta jujjuya tea din hannunsa da spoon saboda yayi sanyi da wuri, Mummy ce ta fito a part dinta tasha lace me kyau, sai kamshi take bugawa, kana kallanta kaga babbar Hajiya, Jawad ya dan sunkuyar da kansa ya ce “Ina yini” ta ce “Lafiya kalau Jawad, su Mami sun tafi ina bacci bamuyi sallama ba” da kai kawai ya amsa, ta ce “Are you not eating food? Gashi fa akan dinning” ya juya yana kallan kan dinning sannan ya ce “I will eat ltr” ta ce “To shikkenan, zanje gidansu Rafi’ah sai dare zan dawo” ajiye glass cup din yayi akan center table ya ce “Let me drop u” Mummy ta ce “A’a ka zauna kasha shayinka Jawad, u don’t have to worry zan iya driving ai” bin bayanta yayi yana murmushi ya ce “A’a zan kaiki Mummy” ta tsaya tana kallansa ta ce “To karna baka wahala anjima kuma” ya ce “A’a zan daukoki ai ba abinda nake” Mummy ta ce “To shikkenan muje” ya bude mata back seat ta shiga sannan ya zagaya seat dinsa yayi wa motar key, bayan sun hau titi Mummy ta ce “Abi yace kaci gaba da aiki ko?” Ya ce “Ehh” ta ce “To Allah ya sanya alkhairi” a hankali ya ce “Ameen” yana rife bakinsa phone dinsa ya hau ringing ya dan juya ya kalla screen din, ganin Mami ke kira yasa wayar a silent yaci gaba da driving dinsa.
‘Yar karamar yatsarta ta mika masa ta ce “then let’s bet” Yusuf dake dariya ya ce “You will soon get used to the idea… So i won’t bet on it” Rafi’ah ta danyi dariya ta ce “Kaji tsoro” shima dariyar yake ya ce “No, i’m not scared, but u know what?” tayi saurin girgiza masa kai, ya ce “When ever i marry you, you will stop wearing veil” ta dan zaro ido ta ce “Why Doctor” ya ce “U look more beautiful in hijab” rife fuskarta tayi da gyalen rigarta ta ce “Kaima ai manyan kaya yafi maka kyau” ya ce “To ai jiya nasa” ta ce “Yeah, nima kuma nasa Hijab” ya ce “Keda baki tsaya mun gaisa ba, kishi ya rufe maki ido” harara ta dan masa ta ce “I don’t want” yana dariya ya ce “Ur wish is my command Hajiyata, is Abba at home?” Ta juyo tana kallanshi ta ce “Me zaka mishi?” Ya ce “Zance asa ranar auranmu ne” dan zaro ido tayi sai kuma ta ce “This is impossible” ya zura hannunsa a pocket dinshi yana kallanta ya ce “Fatima Abbanki mutumin kirkine, after Abbana he’s the second person i can trust, he’s a nice person i ever seen, he welcomed me happily, ya saurari bayanai na from d beginning till end and kinsan abinda yafi birgeni dashi?” Girgiza kanta tayi tana murmushi, Yusuf ya ce “He promised that…” Shiru yayi ganin mota tayi parking a gefensu, ya dan kalli Rafi’ah da itama motar take kalla, ganin Mummy ta fito a ciki yasa Yusuf ya karasa kusanta yana murmushi, har kasa ya durkusa ya ce “Ina yini Mummy” cike da fara’a ta ce “Lafiya kalau Yusuf, how is work?” Ya ce “Alhamdulilah” ta ce “Masha Allah” daga haka ta wuce cikin gida, tashi Yusuf yayi yana kallan Rafi’ah ya ce “Dear, i think i have to go, ko zaki zo muje shopping?” Ta dan girgiza kai ta ce “So kake Ummi ta kakkaryani?” dariya ya danyi ya ce “We are not going far” ta noke kafada ta ce “I’m not going anywhere” har lokacin Jawad na cikin motarsa yana kallansu ta cikin tinted glasses dinsa, after some seconds ya bude kofar motar ya fito, da fara’a Yusuf ya mika masa hannu, shima hannu ya mika masa suka gaisa, sai dai bai kalleshi ba, ya zame hannunsa ya nufi gate, Rafi’ah ta ce “I’m not saying i won’t follow u anymore, watarana ai zamuje shopping din but not now” juyowa Jawad yayi ya kalleta kafin ya tura gate din ya shige. Yusuf ya ce “When is that time?” Ta ce “Idan na gama exams dina, and we are going with khairiyya” ya ce “Sure, zan kawota ranar Saturday ta gaisheki” cike da farinciki ta ce “Yess thank u Doctor” ya ce “Mention not, bana tafi dan naga kinfi son Khairiyya akai na” murmushi tayi me kyau kafin ta ce “And it’s impossible, after Abbana da Ummina, Mummyna then it’s you” daga haka ta boye fuskarta ta nufi gate ya bita da kallo yana murmushi, sai data shige sannan ya shiga motarsa ya bar layin.
Da sallama ta shiga parlor’n tana kallan Mummy ta ce “Sannu da zuwa” Mummy ta ce “Yauwa Daughter” kallan Jawad tayi dake magana da Ummi ta ce “Ina yini” ya ce “Lafiya” Ummi ta kalli Rafi’ah dake kokarin daukan laptop ta ce “Ki kawowa Jawad abinci Rafi’ah” toh kawai tace ta nufi kitchen, Mummy ta mike tana kallan Ummi ta ce “Kuma baima ci abinci ba tinda safe” shi dai sunkuyar da kansa kawai yayi, Ummi ta ce “A dinga kula fa Jawad, are u not afraid of Ulcer” ya danyi murmushi kawai baice komai ba, Ummi ta ce “A dai kiyaye gaskiya” daga haka tabi bayan Mummy suka haura upstairs. Warmers din abincin ta dauko a kitchen ta dora akan dinning, ta koma kitchen ta bude fridge ta dauko drink da table water, tana fitowa ta sameshi zaune akan dinning din, ta ajiye abubuwan hannunta zata juya ya kamo hannunta, with shock ta juyo tana kallansa, idansa na kan warmers din abincin ya ce “Saurayi zaki bi ya kaiki shopping mall ko?” zame hannunta tayi cikin nasa ta ce “And so” Jawad ya dago kansa yana kallanta ya ce “Wannan mutumin da kike gani is just here to spoil ur life and use you, baso na tsakani da Allah yake miki ba, and ki bar ganin yana kaiki shopping malls stop thinking he will stop there, one day he will request for something else” zama tayi akan kujerar dake gefenshi ta ce “Ni bai ta6a kaini wani waje ba, and this is the first time he’s asking me to go for shopping, i trust him and he’s more than kind ” bayan tayi shiru ya ce “So be careful with guys most of them are of that intention of spoiling young girls, ba kuma a cewa an yarda da mutum, the person very close to u can deceive you, so u take very good care of yourself” sauke kanta tayi kasa a hankali ta ce “Thank u” har zaiyi magana phone dinsa ya fara ringing ya ciro wayar a pocket dinsa yayi picking call din hade da sallama, Mami ta ce “Ai sai ka kira kaji ko mun isa lafiya ko? Amma shiru~shiru ba call, or are u happy for my absence Jawad?” A hankali ya ce “No, aiki ne ya min yawa ko gida ban koma ba, but you’re on my mind to call” Mami tayi shiru kafin ta ce “To ka tafin gidan Kawun?” Ya ce “Till tomorrow ai ban koma gida ba har yanzu” ta ce “To shikkenan gobe da sassafe ka tattara ya naka ya naka ka bar gidan” silently ya ce “To Mami, a huta gajiya” ta ce “Yauwa, Allah ya kare min kai” daga haka tayi hanging wayar. Kallansa kawai Rafi’ah take jin karyar daya zuka, ya dago kansa yana kallanta ya ce “So is an advice” tashi tayi ta dauka laptop dinta dake kan sofa ta ce “Thanks for d advice” daga haka ta wuce sama ya bita da kallo.

*Barka da sallah fans, fatan anyi sallah lpy, anci nama lpy? Ina jiran nawa raban nima 馃槃 lol, Barka da sallah once again.*

08103810398
[7/29, 6:47 AM] Zarah: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation
*_…卮乇賷賰 丨賷丕鬲賷…_*
_{MY LIFE PARTNER}_

*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
_We are here to Educate, Motivate and Entertain our Readers._

_By FATIMA 鉁嶐煆籣

_29_

Murmushi Aliyu yayi yana shafa beard dinsa ya ce “Then what decision did u take?” Yusuf ya danyi shiru kafin ya ce “That’s what i’m thinking Aliyu, ita Umma ta dage saina fara auren Jiddah, to bansan kuma ya zan fara fadawa Fatima hakan ba” ajiyar zuciya Aliyu ya sauke yana kallan Yusuf ya ce “Wait Yusuf…. Wane shaidan dinne yake zugaka ka auri mata biyu?” Yusuf ya shafa gashin kansa ya ce “Haka Allah ya tsaramin Aliyu, but before ba haka naso ba” Aliyu ya ajiye glass cup din hannunsa ya ce “To Allah yasa haka ne alkhairi” Yusuf ya ce “Ameen, yanzu ya kake gani za’ayi” ya ce “Kawai tinda Umma ta dage ka fara auren Jiddah, sai ka lalla6a Fatima ka gaya mata ta hanyar da zata fahimta” Yusuf ya danyi murmushi ya ce “Thanks for saying something Aliyu, nagode sosai” Aliyu ya ce “You mention not Yusuf, i think that is the best solution”. Gently Jawad yake tahowa inda suke zaune, duk da hasken wutan dake compound din Yusuf ya dinga kallansa to confirm ko shidinne, ganin shine yasa Yusuf ya mike yana mikawa Aliyu hannu ya ce “I’m going Ali” Aliyu ya tashi yana bashi hannu ya ce “Till tomorrow, gobe da wuri zaka shiga clinic ko?” Yusuf ya ce “Insha Allah” daga haka ya dauka key din motarsa dake kan table ya ce “Night” yana juyawa suka hada ido da Jawad, Yusuf yabi gefe ya wuce parking lot.
Harya fita da motarsa Jawad bai ko kalli inda yake ba, bayan sun gaisa Aliyu ya ce “Yaushe ka dawo 9ja Ahmad?” Jawad dake danna wayarsa ya dago yana kallansa ya ce “Waye wannan wanda ya tafi yanzu?” Aliyu dake zuba masa drink cikin glass cup ya ce “Wai Yusuf? Friend dina ne” Jawad ya sauke kansa kasa ya ce “I need to know more about him” kallansa Aliyu keyi kafin ya ce “Ka san shi ne?” Jawad ya ajiye phone dinsa ya ce “Can i have my answer then?” Aliyu ya jingina da kujera ya ce “To nidai bansan komai a kansa ba, friend dina ne, a asibiti daya muke aiki sannan school daya mukai masters a Italy amma ya rigani gamawa, that’s all i know” Jawad ya limshe idanuwansa ya ce “Is he married?” Aliyu ya ce “No, but ya kusa” da sauri ya bude idanuwansa yana kallan Aliyu kafin ya ce “Wa zai aura?” Aliyu ya dan zaro ido ya ce “Kaiii Barisster, what’s all this question for?” Jawad ya kara limshe idanuwansa ya ce “Answer me pls” Aliyu ya ce “Cousin dinsa zai aura” Jawad ya ce “Alright yayi kyau” Aliyu ya matso da kujerarsa kusa dana Jawad ya ce “Kasan shi ne?” Jawad ya girgiza kai ya ce “No” Aliyu ya ce “Meyasa kayi parking a waje” Jawad ya ce “Is because i’m not staying long, na tsaya salla nan masallacin kusa daku, then i decided to branch and see u” Aliyu ya ce “Good, ka kyauta but not more” Jawad ya daga kafada alamar i don’t care ya ce “Zan wuce ka gaishe da Mama” daga haka ya mike tsaye, Aliyu ya ce “Ko ruwa baka sha ba” ya girgiza kai ya ce “I’m full, kuma sauri nake, zan mayarda Mummy gida” tashi Aliyu yayi suka jera suna tafiya harya rakashi mota sannan sukai sallama ya shigo gida Jawad kuma ya tada motarsa ya bar layin. Slowly yake tafiya yana tina maganar Aliyu “cousin dinsa zai aura” Jawad ya danyi murmushi ya kara speed din motar, few minutes ya kawoshi gidansu Rafi’ah, yayi horn gate man ya bude sannan ya shiga yayi parking ya nufi entrance din gidan, da sallama ya shiga parlorn, Rafi’ah dake kwance ba dan kwali tayi saurin mikewa ta dauka scarf dinta ta saka, Ummi da fitowanta a kitchen kenan ta ce “Ka dawo kenan Jawad, bari a kawo maka abinci” shi dai baice komai ba sai murmushi da yake, Mummy ta ce “Naga shiru baka dawo ba” ba tare daya dago ba ya ce “Nayi branching wajen friend dina ne” Mummy ta ce “Ohk, to kaci abinci mu tafi nasan Abi yana dab da komawa gida” ita dai Rafi’ah na zaune tana kallon wani indian film a laptop, ta dan daga kanta ta kalli Jawad suka hada ido, a tare duk suka sauke kansu kasa, Ummi ta ajiye masa abincin akan center table sannan ta jawo shi gabansa ta ce “Bismillah” daga haka ta dauko masa table water sai cup ta ajiye a gefen plate din, gefen Rafi’ah ta zauna tana tattara papers din da tai making, Rafi’ah ta dan zaro ido ta ce “Laah Ummi, Abba bai bani 5k dinba kuma ya shiga apartment din Anty” Ummi ta ta6e baki ta ce “Then u leave it till tomorrow” turo baki tayi ta ce “To ai ba lallai ya tashi da wuri ba” Ummi dai bata kulata ba taci gaba da abinda take. Jujjuya abincin kawai Jawad yake, shi dama cin abincin dare bai wani dameshi ba, bayan ya dan ci ya mike yana kallan Ummi ya ce “Thank u Ummi, sai da safe” Ummi ta kalli abincin kafin ta ce “What have u eaten Ahmad? Banga kaci komai ba” ya dan shafa kansa yana murmushi ya ce “Naci ai Ummi” ta ce “To Allah ya kyauta” tashi Mummy tayi tana kallan Rafi’ah ta ce “Ba rakiya ne Fati” Tashi tayi tabi bayan Mummy suka fita zuwa mota, Mummy dake kallan ta ta ce “Yaushe zaku gama exams din?” A hankali ta ce “Friday” ta ce “To sai kizo ki tayani zama ko” ta ce “To” daga haka ta ce “Allah ya kiyaye” Mummy ta ce “Ameen” juyawa Rafi’ah tayi ta koma ciki sannan Jawad yaja motar suka fita gate din.
Washegari bayan su Rafi’ah sun gama shirin makaranta sunyi breakfast tace wa Ummi zataje wajen Abba, da kai ta amsa mata sannan ta fita a parlorn su ta nufi apartment din Anty Amina, tana murda handle din tayi sallama, Abba dake zaune a parlor yana kallan news ya dago yana kallanta ya ce “Come in Mamana” Canvas din kafarta ta cire sannan ta nufi wajen Abba ta zauna gefenshi, sosai uniform din yayi mata kyau tana ta kamshi, a hankali ta ce “Good morning Abba” ya ce “Morning sweetheart how was ur night?” Ta ce “It was fine Abba, dama jiya ka manta baka bani 5k din ba” Abba dake kallanta ya ce “Ohh na manta, muje na saukeku kawai, tinda i’m doing nothing” murmushi kawai take ta mike tsaye, Abba ya ce “Jeki gaishe da Antynki a kitchen kafin na dawo” daga haka ya nufi upstairs, gently ta karasa kitchen din ta bude, a tare duk suka juyo suna kallanta, ta danyi kasa da murya ta ce “Good morning” juya kai Anty Amina tayi ta kalli Ikleemah dake hararan Rafi’ah ta ce “Jeki rufemin kofa” Rafi’ah najin haka ta juya ta bar wajen, Ikleemah tayi banging kofar tana jaan tsaki ta ce “Wai Anty dan jaraba da safen ma sai anzo miki, naga Abban a gidanki yake” Anty Amina ta ce “Yanzu haka uwarce ta turota, nidai nafi karfin kowa ba maganin da zasu barbada yayi tasiri akaina” Ikleemah ta ta6e baki ta ce “Sai kace aljana wallahi, anya bata bleaching Aunty? Gashi sai kyau take” Anty Amina ta ce “Caan nasu kuma”. Abba na saukowa ya wuce Rafi’ah na biye dashi har suka iso parking lot, ta shiga ta dauko school bag dinta sannan suka fito ita Abdul suka shiga mota Abba yaja suka fita, dama tuni mai gadi ya wangale gate, sai da suka hau saman titi Abba ya ce “Mamana u take good care of yourself, be a daughter of a respected man, calm yourself dear, insha Allah u won’t regreat in life Fatima, and never get tired to praying, idan zaku kwanta ku ringa alwala, tashi sallan dare even if it isn’t everyday, and u two should never get tired of reading qur’an” a tare duk suka amsa da “Insha Allah Abba” Abba ya ce “Allah ya muku albarka” suka sake amsawa da “Ameen”.
Anty Khadija ne zaune a dakin Umma tana bubbude kayan lefen da Umma tace ta gama hadawa, bayan ta gama budewa ta dago tana kallan Umma ta ce “Yanzu sai saka rana kenan” Umma ta ce “Insha Allah, na kira kanwar uwarsa ma na fada mata tazo taga kaya kar tace an wareta” Anty Khadija ta ta6e baki ta ce “Umma amma dai kin kara masa lokacin da yace zai auri yarinyar caan? Gara abar Jiddah taci amarcinta hankali kwance” Umma tayi dariya ta ce “Ke dai mun gama magana, ya auri Jiddah tukunna, ita kuma waccen ko bata aureshi ba sai tayi nadamar saninsa, dan Yusuf sai ya zame mata bala’i da tashin hankali a cikin rayuwarta” Anty Khadija dake murmushi ta ce “Yesss, nasan tinda kika fada saiya tabbata Umma, wayaga idon yarinyar taab” daga haka ta kwashe da dariya harda tafawa.
Ranar Friday Rafi’ah ta gama exams dinta a ranar ne kuma Abba ya kira Yusuf ya sanar masa ya bashi auren Rafi’ah, kar kuga murmushi da farinciki wajen Yusuf, sai dai idan ya tuna Rafi’ah bata saan da maganar auransa da Jiddah ba sai zuciyarsa ta tsinke, amma ya dauki alkhawari dole zai gaya mata ko zai samu nutsuwa ta wannan bangaren, ranar Saturday da yamma Rafi’ah na zaune a dakinta wayarta ya fara ringing, murmushi tayi ganin Yusuf ke kira sannan tayi picking call din hade da sallama, ya amsa mata sannan ya ce “I’m outside dear, ga kuma Khairiyya na kawo maki” cike da murna ta ce “Ohk im coming out now” daga haka tayi hanging wayar ta mike ta dauka dogon himar dinta cikin press ta saka, phone dinta kawai ta dauka ta sauko downstairs, ta danyi shiru tana nazarin me zata cewa Ummi, kamar daga sama taji muryarta tana fadin “Where are u going?” Tayi saurin sauke kanta kasa ta ce “Amm…dama..dama Doctor ne yazo yana waje” Ummi ta juya ta koma kitchen ta ce “Don’t stay long” murmushi Rafi’ah tayi ta zura flat shoes dinta sannan ta fita a parlorn, cikin nutsuwa take tafiya harta fito gate, Khairiyya ta fito daga front seat tayi hugging dinta ta ce “I missed u Anty” Rafi’ah taja hancinta tana gyara mata scarf dinta ta ce “I missed u khairiyya, how are u?” Ta ce “I’m fine, Yaya yace i’m spending the day with u” sai lokacin ta kalli Yusuf dake kallanta ko kiftawa babu, ta sauke kanta kasa ta ce “Ina yini Dr” ya ce “Fine sweetheart, ya hutu?” Ta ce “Alhamdulilah” ya ce “SS3 zamu shiga ko?” Tayi saurin rife fuskarta tana murmushi ta ce “Ni ka daina tsokala na” ya ce “No i’m counting my days” zaro ido tayi ta ce “So soon?” Ya ce “Ehh mana, aiba yawa lokacin” ita dai murmushi kawai tayi, ya sake kallan fuskarta ya ce “Bayan awa biyu zan dawo na dauketa, and i want to talk to u idan na dawo” a hankali ta daga masa hannu ta ce “Ohk till u come back” ya ce “Thank u” daga haka yayi reverse ya bar unguwar, Khairiyya ta kalli Rafi’ah ta ce “Anty kawai sai ki boyeni mu kwana” Rafi’ah ta zaro ido ta ce “So kike yau Amminki tazo ta zaneni” Khairiyya tayi murmushi looking happily, Rafi’ah ta kama hannunta ta murda handle din suka shiga, kallansu kawai Ummi take har suka karasa shigowa, Khairiyya ta zauna a kan carpet tana kallan Ummi ta ce “Ina yini” Ummi ta ce “How are u?” Ta ce “I’m fine” kallan Rafi’ah tayi dake daukan abu akan dinning ta ce “Who is she?” Kanta na kasa ta ce “Cousin din Dr ce” Ummi ta ce “Ohk, tashi ki zauna kan kujera mana, what’s your name?” A hankali ta ce “Fatima Zarah, amma Ammina da Daddynah used to call me Khairiyya” Ummi ta danyi murmushi ta ce “Good”. Bayan Rafi’ah ta gama hada mata fruits salad ta mika mata ta ce “U take this Baby, and what will i cook for u” Khairiyya ta kar6a bowl din tana murmushi ta ce “Na koshi da abinci Anty, but i like this” daga haka ta dauka tea spoon dake gefen bowl din ta fara sha, Rafi’ah na zaune harta gama shanyewa, ta mike ta ajiye bowl din akan dinning, Rafi’ah dake kallanta ta ce “Ko in kara maki?” Ta girgiza kai, kama hannunta Rafi’ah tayi suka haura upstairs, bayan sun shiga dakinta Khairiyya ta limshe ido ta ce “Anty is this ur room, very neat and it’s smelling nice” Rafi’ah dai murmushi kawai tayi, Khairiyya ta daga kanta tana kallan hotunan Rafi’ah dake jikin wall tin tana ‘yar karama har izuwa yanzu, Rafi’ah ta ce “Khairiyya ko in kawo miki fried rice?” Zaro ido yarinyar tayi ta ce “Anty nifa bana cin abinci sosai da dai Yaya Sameer kika ce, shine Ammi tace ko a office ci kawai yake, shi kuma Yaya Faruk wai bayacin spaghetti” murmushi kawai Rafi’ah take tana kallanta, ta sake cewa “Allah Anty Yaya Sameer yana da ci, zai iya cinye abincin cikin gidan nan” Rafi’ah na dariya ta jawo laptop dinta ta ce “Which cartoon do u want to watch?” Cike da farinciki Khairiyya ta ce “Yess Anty, i love watching Angelina ballerina” Rafi’ah ta shiga YouTube tayi searching sannan ta saka mata, bayan ta fara kalla ta mike ta ce “I’m coming dear, just 5 minutes” daga haka ta fita a dakin.
A awa biyun da Khairiyya tayi wajen Rafi’ah taga kulawa sosai, duk abinda tace tanaso Rafi’ah zata bata, har 500 ta bawa Mustapha ya siyo mata chocolate, bayan Yusuf ya kira yana waje Rafi’ah ta kashe kallan tana kallan Khairiyya ta ce “Yaya is outside Khairi” Khairiyya ta rungume Rafi’ah ta baya ta ce “I will miss u Anty” kama hannunta tayi suka fita ta kaita har dakin Ummi ta ce “Zata tafi Ummi” Ummi ta bata packet din sweet sai ribbom da bead, ta dan rusuna tana dariya ta ce “Nagode” Ummi ta shafa kanta ta ce “A gaishe da Mama” da toh ta amsa tana ta dagawa Ummi hannu, bayan sun fito a dakin Rafi’ah ta ce “Wait here” daki ta koma ta dauko mata ledan chocolate dinta sai dan karamin tirare cikin wani kwali, ta hada mata chocolate da sweet din waje daya sannan tasa mata tiraren cikin ledan bead din ta ce “The perfume is also for u” Khairiyya ta wara ido ta ciro shi tana shinshinawa ta ce “Anty irin kamshin dakinki da jikinki, i love it, thank u Anty” shafa kanta Rafi’ah tayi sannan ta kama hannunta suka sauko downstairs, bayan sun fita a parlorn suka nufi bakin gate, yana tsaye jikin motarsa as usual, Khairiyya ta shiga nuna masa abubuwan hannunta, ya kalli Rafi’ah da kanta ke kasa ya ce “Thanks for everything love” ta danyi murmushi ta ce “Mind not, i will miss her much” Yusuf ya dan shafa kansa ya ce “To muje ki rakani mu kaita gida” ta ce “No, kaje dai ka dawo” ya ce “Pls, aiba nisa ba kince kinsan area ba” a hankali ta ce “Toh” ya bude mata front seat yana murmushi ta shiga, daga haka ya zagayo seat dinsa yayi wa motar key suka wuce, 5 minutes ya kaisu gidan Ammi, Yusuf ya juya yana kallan Khairiyya ya ce “Kije ciki Khairiyya zan maida Anty gida” kamo hannun Rafi’ah tayi ta ce “Thank u Aunt, baza kuje nima kiga Ammina ba?” Ta ce “Noo, some other time Khairi, zanzo kiyi ta bani labari” daha haka ta sauka a motan tana daga musu hannu ta shiga gate, juyowa Yusuf yayi yana kallan Rafi’ah dake murmushi. Jifa jifa suke hira har suka kusa isowa gida, ya samu dai dai kasan wata bishiya yayi parking ya juyo yana kallanta, nan da nan kirjinta ya hau bugawa, ya sakar mata murmushi ya ce “What?” Ta ce “Naga kayi parking a nan, and the street is very quite” Kamo hannunta Yusuf yayi yana kallan idanta ya ce “I want to say something Fatima, but pls don’t judge me wrong” dago kanta tayi tana kallanshi, ya ce “Sure nasan u are my happiness, u cause alot of changes in my life Fatima, i don’t know how much i luv u, and insha Allah i will continue caring till my last breath” sauke kanta tayi kasa tayi shiru, ya kara kamo dayan hannunta silently ya ce “Kafin na hadu dake akwai wacce nake soyayya da ita, she’s in my house, her name is Jiddah, and i promise to marry her too” kanta na jikin kujera tana jinsa amma ko dago kanta ta kalleshi bata yi ba, ya matsa kusa da ita ya ce “I hope zamu zauna tare dukkanmu?” Daga masa kai tayi, ya ce “Noo, u speak” a hankali ta ce “I’m hopping for d best, Allah yasa shine alkhairi” baisan lokacin daya rungumeta ba, tayi saurin janye jikinta tana turo baki, bai ta6a tinanin iya abinda zata ce ba kenan, ya kamo hannuta yayi kissing soft hand dinta ya ce “U are d best Rafi’ah, ke dabance a cikin mata, i luv u so much Fatima” murmushi ta danyi ta juya tana kallan waje ta cikin glasses din motar, ya tada motar yana kallanta ya ce “Bari mu wuce kar Ummi ta neme ki” daga haka yaja motar, har suka iso gida bata ce komai ba, sai da taga yayi parking ta ce “Nagode, Allah ya kiyaye hanya” ya kara kamo hannunta ya ce “Are u angry with me Fatima?” Ta girgiza kanta trying hard not to cry ta ce “Why will i Dr, Allah yasa haka shine alkhairi” daga haka ta zame hannunta ta fito a motar. Tabbas ita kadai tasan abinda taji a zuciyarta a sanda yake mata zancen Jiddah, but ya zatai, a yanzu babu wanda takeso fiye da Yusuf bayan iyayenta, haka Allah ya tsara mata me mata zata aura, so her own is to pray for d best, tana shigowa gate hawayen daya taru a idanta ya gangaro, Jawad dake tsaye a parking lot ya nufota yana kallanta ya ce “What’s it? Why are u crying” matsawa tayi gefe zata wuce ya kamo hannunta suka koma gate, lekawa yayi ya hango motar Yusuf daya kusan kaiwa titi, ya juyo yana kallanta ya ce “Meya faru?” Ta girgiza masa kai, ya ce “Tell me, koya maki wani abu ne?” Ta girgiza kai tana saan kwace hannunta amma ta kasa, ya kara jaanta zuwa parking lot suka nufi backyard din gidan, yana rike da hannunta kawai yaji tayi gefe zata fadi, yayi saurin rikota zuwa jikinshi yana kallan numfashinta dake shirin sarkewa, ta dafe kirjinta hawaye naci gaba da sakko mata, yana jiyo yadda zuciyarta ke bugawa da sauri da sauri, ya kai hannunshi bayanta yana patting dinta to make sure she remain calm.

*I’m on my way to Kano now, ur prayer pls*

_08103810398_
[7/29, 6:47 AM] Zarah: *_…卮乇賷賰 丨賷丕鬲賷…_*
_{MY LIFE PARTNER}_

*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
_We are here to Educate, Motivate and Entertain our Readers._

_By FATIMA 鉁嶐煆籣

_30_

Hannunta na rawa tayi saurin janye jikinta tana kokarin mikewa, Jawad ya durkusa yana kallan eyeballs dinta dake fitar da hawaye ya ce “Are you ok Fatima?” Ta daga masa kai tana san tafiya amma jiri takeji bana wasa ba, har lokacin yana rike da hannunta yana kallanta, ta dafa wall ta fara tafiya a hankali ya kamo ta ya ce “You sit down and rest first” girgiza masa kai tayi, ya kamo hannunta ya ajiyeta akan balcony ya ce “Don’t u there try to get up, keep quite and remain still” kanta ta kifa akan cinyoyinta ta fashe da kuka, Jawad ya zauna gefenta yana kallanta da mamaki, kusan minti 5 tana kukan kafin ta dago kanta tana kallanshi ta ce “Zan iya tafiya Yaya, i’m not feeling anything” ya ce “Ohk, but what happened” tayi saurin girgiza masa kai ta ce “I’m having headache but no one offended me” daga haka ta mike walking slowly ta bar wajen, har idanuwanta sun kada sosai ta tura kofar parlon su ta shiga tana dafe da kirjinta, ba kowa a parlor hakan yasa ta nufi upstairs, tana gama hawa stairs ta shige dakinta tasa key, zubewa tayi a kasa ta fara kuka me cin rai yadda ba wanda zaiji, da kyar ta karasa kan gadonta ta jawo wayarta ta kira number Ameera, tana dagawa ta ce “Dan Allah Ameera kizo gidanmu, let me tell u ko zanji saukin abinda nakeji” Ameera da hankalinta ya tashi ta ce “What are u saying Fatima? Is Ummi not at home” tsayar da kukan Rafi’ah tayi ta ce “I’m begging u Ameera, dan Allah kizo karna mutu” cikin tashin hankali Ameera ta ce “Ohk gani nan” daga haka tayi hanging wayar. Cikin minti 10 sai gata ta shigo gidan, ta murda handle din kofar ta shigo parlorn, dan murmushi tayi ganin Ummi a parlor tare da Jawad ta ce “Ina yini Ummi” Ummi dake kallanta ta ce “Lafiya kalau Zainab, ya hutu dasu Mamanki?” A hankali ta ce “Duk lafiya suke” kallan Jawad tayi shima ta gaishe shi ya amsa, Ummi ta ce “Gashi kamar ma ta fita fa Zainab, amma bari na kirata a waya” mikewa Ameera tayi ta ce “A’a ita ta kirani, tana sama ina ga” Ummi ta ce “Ohh ta dawo kenan, to ki shiga mana” Ameera ta ce “To Ummi” daga haka ta wuce upstair. Tana murda kofar dakin taji a kulle ta fara bubbuga kofar tana kiran sunan Rafi’ah, tashi tayi ta cire hijabin jikinta sannan ta karasa kofar ta bude, Ameera ta rungumeta ta ce “What is it Fatima? Are u sick?” Rafi’ah ta tura kofar ta kamo hannun Ameera ta ce “Ameera ya zanyi, my Doctor is getting marriage” zaro ido Ameera tayi tana kallan yadda ta fashe da kuka, ta kara rungume Ameera ta ce “Allah inason shi, kema kin sani Ameera, but suddenly yau yake cemin akwai wacce zai aura after then saiya aureni, Ameera my heart is beaten i dont want to have attack” tana magana amma hawaye sunki tsaya mata, Ameera ta shiga share mata idanta ta ce “Kiyi shiru, kinsha magani kuma?” Rafi’ah ta girgiza mata kai ta ce “I took all before u came” Ameera ta kamo hamnunta ta ce “To yanzu ya zamuyi, zaki rabu dashi ne?” Da sauri Rafi’ah ta kalleta zuciyarta na bugawa ta ce “Are u out of ur senses Ameerah, ya zanyi na rabu da abinda zuciyata take so, ai koda mata uku zai aura zanje ta hudu i don’t care” Ameera ta dalla mata harara ta ce “And if u don’t care why are u crying?” Rafi’ah dake share hawayenta ta ce “Kinsan dai i most…is a most… I repeat a most…a fada maka magana irin haka unexpected ace bakai kuka ba, but ya zanyi Ameera ina san Yusuf fiye da tinanin kowa, amma tinda haka Allah ya tsaramin i will accept my fate and i pray, nasan Allah ya ga zuciyana banajin zan iya rayuwa da kowa inba Doctor ba, he is just a half of me Ameera” tana rife bakinta wasu siraran hawaye suka shiga sauko mata, Ameera ta mike tana murmushi ta ce “That’s the best for u Teemah, kiyi ta addu’a kawai, and i will also contribute mine” rungumeta Rafi’ah rayi ta ce “Thank u friend, i luv u” Ameera ta share mata idanta ta ce “Dan Allah ki daina kuka, ai naga kece ma zakije a amarya ba’a tsohuwa ba” dariya ta bawa Rafi’ah, ta danyi murmushi ta ce “Haka ne mana, and nasan Doctor zai iya komai dan ya saki farinciki, kuma hakan da yayi shine adalci daya sanar dake tin yanzu, kinga kinsan da zamanta kenan, koda auransu yazo bazakiji kamar yadda idan baki sani ba, and last last u stop crying dear, i’m begging u” murmushi Rafi’ah ta sakeyi ta ce “Insha Allah i won’t Ameerah, nagode sosai” Ameera ta yafa veil dinta ta ce “I’m going, Mama bata gida na bar su Noor su kadai” tashi Rafi’ah tayi ta zura hijabinta ta ce “Bari na raka ki” daga haka suka fito a dakin, suna saukowa downstairs Ameera ta dan rusuna ta ce “Ummi zan tafi sai anjima” Ummi ta ce “To Zainab, ki gaishe da gida” daga haka suka fita Jawad ya bisu da kallo, bakin gate Rafi’ah ta rakata sannan ta juyo, tana shiga parlorn suka hada ido da Jawad, ya dinga kallanta to make sure she isn’t crying, ta wuce upstairs da sauri tana turo baki, a dakinta ta samu Ummi na duba abu a wardrobe, ta cire hijab dinta ta zauna bakin gado, Ummi ta gama tattara takardun ta juyo tana kallanta ta ce “Meya samu idonki? Kamar kinyi kuka” ta ce “Abune ya fada min” Ummi ta ce “Ya fita ne?” ta ce “Ehh” daga haka Ummi ta fita a dakin.
Shafa kansa yayi yana kallanta yana murmushi , Ammi ta ce “To meyasa baku shigo na ganta ba?” Ya ce “Zan kawota watarana ta ganki” Ammi ta ce “Ai shikkenan, muna ta bakayi aure da wuri ba ashe kaikam da biyu zaka fara” Farouk dake zaune yayi dariya ya ce “Ammi yanzu nan aka ce maki ba lokaci daya zai auresu ba” Ammi ta ce “Shekara daya kaam ai kamar yau ne Farouk” murmushi sukai duk tasu, Ammi ta ce “Gobe insha Allah zanje naga lefen Jiddan” ya ce “Ohk, amma karkije da Khairiyya bakinta baya shiru” Ammi ta ce “Kanku akeji kuma” da sallama Sameer ya shigo parlorn yana rike da key din motarsa, ya mijawa Yusuf hannu suka gaisa, bayan ya zauna Ammi ta ce “Saura kai Sameer, Yusuf ya kusan zama ango, dama ku biyun nan ku aka sawa ido, yana kaucewa saura kai kuma” Sameer ya daga kafada ya ce “Ni ai da hudu zan fara Ammi” Farouk dai na zaune sai dariya yake, Sameer ya ce “Na bawa Yusuf za6i ya samo min daya, na samo daya da kaina, keda Daddy sai ku samo daddaya” Yusuf ya ce “Aa ba ruwana nikam” Sameer ya mike yana dariya ya ce “Ehh mana, kaga sai ku tayani nema, amma kuma zanfisan waccen zan samo maganar gaskiya” a tare duk suka kwashe da dariya, Ammi ta ce “Ba zancen wasa ba Sameer, da anyi maganar aure saika waske da wasa shekara 34 kana zaune min a gida ga uban ci, gara ma Yusuf baya wani ci, amma kaikam duk wacce ta aureka ta shiga uku da girki” sai murmushi yake ya nufi kaan dinning ya dauki plate, Ammi ta ce “Ka gani ko Yusuf, to ko a office haka yake, yana aiki yana ci” Yusuf dai dariya kawai yake yana kallan Sameer, ya juyo yana kallan Farouk ya ce “Yaushe zaka koma Cyprus Umar?” Farouk ya ce “Next month, hutun dama ba yawa” Yusuf ya ce “Allah ya kaimu” daga haka ya mike yana kallan Ammi ya ce “Zan tafi Ammi” Khairiyya dake kwance jikin Ammi ta ce “Yaya ka gaishe da Anty” ya ce “To zataji, bye bye” daga haka ya daga mata hannu, Sameer ya daga masa hannu ya ce “Sai yaushe kuma?” ya ce “Sai dai kazo kawai” daga haka sukai sallama ya fita a parlor, yana isa parking lot wayarshi tayi kara, ya zaro ta a pocket dinsa yana kallan message din Jiddah kamar haka _”Hello, i just text to tell u that ansa ranar auranmu nan da 1 month, and i hope u will come back soon? Saboda mu nuna farincikinmu, na hada maka favorite food dinka I luv u Yaya”_.

*For the sake of Khadija KK, ga update nan very little 馃槦 ba dan nacin kiba da bazanyi ba 馃槃 i’m so tired wallah* .
[7/29, 6:47 AM] Zarah: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation
*_…卮乇賷賰 丨賷丕鬲賷…_*
_{MY LIFE PARTNER}_

*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
_We are here to Educate, Motivate and Entertain our Readers._

_By FATIMA 鉁嶐煆籣

_31_

Fifteen minutes ya kai Yusuf gida daga unguwar Rimi, bayan yayi parking ya fito rike da phone dinsa ya rife motar, yana juyawa suka hada ido da Jiddah dake tsaye tana sakar masa murmushi, tayi bala’in yin kyau sai kyalli take, a hankali ya zura hannunsa cikin pocket dinsa ya fara takawa gently har zuwa inda take tsaye, yayi kasa da murya ya ce “U look so cute Jiddah tah” ta kara sakar masa murmushi ta ce “Thank u Yayana, muje ciki kaga abinda na dafa maka” ya danyi murmushi yabi bayanta suka shiga parlorn, ba kowa a ciki sai TV dake ta aiki, ta zauna akan dinning tana kallansa ta ce “Here it is Yaya” ya bude karamar warmer yana kallan vegetable soup din data ji kayan hadi da nama, ya bude dayan yaga tuwon shinkafa, surprisingly ya juyo yana kallanta ya ce “So u have time to prepare this kike barina da yunwa Jiddah?” Ta farfara masa ido ta ce “Ai lokacin ina school ne yanzu kuma nayi hutu” daga haka ta mike ta fara serving dinsa, Yusuf ya dan shafa kansa yana kallanta ya ce “Hope haka zakina min a gidana?” Ta juyo tana kallansa sai kuma tayi murmushi ta ce “Accepted” hannunsa ya wanke ya fara cin tuwan yana kallanta, bayan few minutes ya kara kallanta yaga kallansa take, ya danyi murmushi ya ce “Naje wajen kanwarki yau, and u know what?” Nan da nan ta hade rai ta juya kanta gefe, ya ce “Ya akayi Jiddan Yaya?” Ta kara hade rai ta ce “Ni banasan zancen yarinyar” Yusuf ya wara ido yana kallanta ya ce “Really?” Ta daga masa kai, ya ce “To ai watarana tare zamu zauna, dan banda ra’ayin raba muku gida, kinga tun wuri gara ku saba, Fatima bata da matsala, she’s kind and nice to stay with” Yana rufe bakinsa taja wani dogon tsaki, ya juyo yana kallanta ya ce “Why the hiss Jiddah?” A fusace ta ce “Then what’s my business with her? nina ce banasan kana min maganarta akwai abinda na hada da ita ne” Yusuf ya wanke hannunsa ya dauki phone dinsa dake kan dinning ya ce “Ai kuwa ke kika hada abu da ita, tinda very soon zaku mallaki miji daya” mikewa tayi kamar zata tashi sama ta bar wajen ya bita da kallo. Kwana uku da faruwan haka Yusuf ya kira Abba ya sanar masa maganar auransa da Jiddah, bayan sun gama waya Abba ya sanarwa Ummi, ta nuna 6acin ranta karara a fili saboda bata ta6a tinanin haka ba, fitowa tayi a dakin Abba duk jikinta a mace ta wuce dakinta, Abdul na zaune yana kallo a laptop dinta, ta rife laptop din ya dago yana kallanta ya ce “Nayi sallah fa Ummi” zama tayi bakin gado ta ce “Kiramin Rafi’ah, kai kuma ka wuce” a hankali yace to sannan ya fita a dakin ya rufo mata kofa, fitowanta a wanka kenan tana goge jikinta Abdul ya shigo, ya tsaya bakin kofa ya ce “Anty, Ummi na kiranki” daga haka ya fice a dakin, cikin sauri ta shafa body lotion ta shirya cikin doguwar riga na atampa sannan ta daura dankwalinta ta fita zuwa dakin Umminsu, gently ta tura kofar ta shiga da sallama, Ummi dake zaune ta ce “Come here” sai da kirjinta ya buga ganin yanayin mahaifiyarta, a tsorace ta karasa ta zauna a kan carpet ta ce “I’m here” Ummi ta juyo tana kallanta ta ce “Da gaske ne Yusuf aure zaiyi?” Rafi’ah ta daga mata kai, Ummi ta ce “And that’s what u choose for yourself?” Kanta ta sauke kasa bata ce komai ba, Ummi ta ce “Well, kiyi duk abinda kika ga ya dace Rafi’ah, har nawa kike da zaki auri me mata? Don’t u see ur mates? Kowa kokari yake idan ya gama secondary school ya samu admission yaci gaba da karatu but ke aure kika sa a gaba” kanta na kasa duk tana sauraron mahaifiyarta, Ummi ta ta6e baki ta ce “Ya miki kyau, idan kinga haka kikeso fine, nidai addu’a shine nawa, kuma duk abinda ya faru dake mine is to say sorry” a hankali ta dago tana kallan Ummi ta ce “I’m sorry” Ummi ta ce “Noo u haven’t wronged me Rafi’ah, ina jiye miki gaba ne, shi aure nutsuwa yake bukata da kwanciyar hankali, nasan kuma indai zakije gidan wata to dole ne zakiyi facing challenges, u are too young for that Rafi’ah, bazaki hakura dashi ba idan kika gama Allah ya kawo miki wani kiyi auranki” sai a sannan ta juyo dai dai saitin Ummi ta ce “Dan Allah Ummi kiyita min addu’a, i don’t know what is coming over me, ina sanshi Ummi, kuma ita sun dade tare dashi, na miki alkawarin bazan ta6a neman fadan taba idan har Allah yayi shina aura, i promise u this Ummina, addu’ar ki kawai nake bukata” ajiyar zuciya Ummi ta sauke ta ce “Tooo, Allah ya za6a miki duk abinda yafi alkhairi” a hankali ta ce “Ameen” sannan ta mike ta fita Ummi ta bita da kallo.
Shirye~ shirye sosai Umma take na bikin Jiddah, gidansu ma kansa saida aka masa paint from head to toe. Almost everyday Jawad ya kanje ya gaishe da Ummi, wani lokaci ya kawo Mummy su yini, duk da ba’a gida yake kwana ba duk safiya saiya biya ya gaishe da Mummy da Abi kafin ya wuce wajen aiki, ta bangaren Yusuf kuwa tinda ya gama gyaran gidansa Umma ta sa shi a gaba, yau tace ya kawo dubu dari, gobe tace ya kawo dubu hamsin, haka dai kullum, ko kadan kuma baya nuna gajiyawarsa akan hakan, duk abinda suka tambaya ya kam basu, sosai da sosai kuma yake kula da Rafi’ah, baya kwana biyu baije sun gaisa ba, waya kuwa kullum cikin yinta suke hakan kuma na kona raan Jiddah ba kadan ba, idan tayi magana sai yace ai ita kullum suna tare, a haka har biki saura sati daya, a ranar ne kuma Mamin Jawad ta dawo daga Abuja saboda Ikram zata koma school.
Zaune take a gaban mirror tana waya aka bude kofar, tayi still tana kallan wanda zai shigo, ganin Ameera yasa ta sauke ajiyar zuciya dan a tinaninta Ummice, da yanzu ta hau fada, Ameera ta tsaya gabanta ta ce “Matar Doctor Yusuf” Rafi’ah ta danyi murmushi tayi hanging wayar ta ce “Matarsa na gidansu ai” Ameera ta ce “Kema very soon zaki zama ai” Rafi’ah ta sake murmushi ta ce “Daga ina kike” Ameera ta ce “Jiya bakije islamiyya ba, shiyasa nazo naga ko lafiya, kuma dazu nayi ta kiran wayanki baki dauka ba” Rafi’ah ta ce “Ohh, wayan na silent ne, kinsan Doctor used to called much, kuma Ummi fada take tayi wai ina waya da yawa, nikam kawai sai nasa a silent idan ya kira nayi ta wayana, yanzu ma akan idan na gama zan kiraki ne” Ameera ta ta6e baki ta ce “To aikuwa kamar a bakin Ummi” Rafi’ah nata dariya ta ce “Kamar da gaske”. Hira sosai sukayi kafin Rafi’ah ta rakata har bakin layi sannan ta dawo gida, tana dawowa ta samu Ummi a parlor ta dawo a aiki, ta zauna tana kallanta ta ce “Sannu da dawowa” Ummi ta ce “Sannu, Anty Halima nata kiranki wai baki dauka ba why?” Rafi’ah ta duba phone dinta aikwa taga 6 missed call dinta, ta ce “I don’t know she called” Ummi ta ce “Tinda yau saturday ki shirya Mustapha ya kaiki, batajin dadi ki tayata zama, gobe saiki dawo” dan zaro ido tayi ta ce “Meya sameta?” Ummi ta ce “Zazza6i take, yanzu nayi branching na duba ta” sama Rafi’ah ta wuce ta samu handbag din Ummi me dan girma ta saka kayanta da drugs dinta a ciki sannan ta canza hijabi ta sauko tana kallan Ummi ta ce “To zan tafi sai da safe” Ummi ta ce “Safe, zan kira Abba na fada masa” daga haka ta fita zuwa parking lot.
Mustapha na zaune a balcony din Anty Amina yana kallan idan film a wayarsa, dama nan yake zama indai tana Abuja, Rafi’ah ta karaso kusanshi ta ce “Zaka kaini gidan Mummy yanzu fa” ya mike yana nade tabamarsa ya ce “To Hajiya karama, wallahi wani film nake kalla, yarinyar cikin film din kamar ke, har kama kuke Hajiya” Rafi’ah ta dan juya ido ta ce “Taya za’ai ina Nigeria kace ina kama da Indians” ya ce “Allah kuwa Hajiya, hancinku ma iri daya ne” Rafi’ah ta danyi murmushi ta ce “To zan hadaka da Doctor kuwa” Mustapha ya washe baki yana dariya ya ce “Allah sarki, ai jiya ma daya zo kafin ki fito hira muka sha, ya bani dubu uku, gaskiya kinyi sa’a Hajiya karama, akwaishi da kyauta, gashi fari kaal dan gaye, amma dai bafulatani ne ko?” Rafi’ah na shiga mota ta ce “Sai dai ka tambayeshi idan yazo” Mustapha ya ce “Ai mutumina ne bari ya sake zuwa, anya ba tattarawa zanyi idan anyi aure ba in koma gidanki” Rafi’ah ta ce “Zakawa Abba butulci kenan?” Ya saki murmushi yana jaan motar ya ce “Ai Abba ubane Hajiya karama, tinda nake ban ta6a ganin mutum me fahimta irin Alhaji ba, Allah ya biya shi da gidan Aljannah” a hankali ta ce “Ameen” sannan tayi picking call din Yusuf.
Few minutes ya kaisu gidan Mummy, bayan yayi parking ta masa sallama sannan ta tura gate din gidan ta shiga, a hankali ta sauke kanta ganin Jawad na zaune akan farar kujera dake kan balcony, sai da ta iso dai dai saitinsa ta ce “Ina yini?” Ya ce “Lafiya kalau” daga haka ta shige ciki, Mami na zaune a parlorn da wata kawarta Hajiya Kareema, Rafi’ah ta dan rusuna ta gaishesu, Hajiya kareema ta amsa tana kallanta harta shige part din Mummy, a hankali ta zaro ido ta ce “Wannan yarinyar fa?” Mami ta ta6e baki ta ce “Diyar kanwarta ce, ni wallahi baso ma nake tana zuwamin gida ba, ciwan zuciya ne fa da ita” Hajiya Kareema ta zaro ido ta ce “Ciwan zuciya kuma? ‘yar yarinyar nan dako 18 inaga bata cika ba” Mami ta ce “Atooh, ni dai cewa nayi ma ko HIV ne da ita suke boyewa, kiganta fa a bushe sai farar fata, gashi idan ciwan ya tashi saita fita a hayyacinta, batasan ma waye a kanta ba, ni tsorona kar tazo ta ya6a mana wani kalan cutan mu shiga uku, kinga wancen zuwanta ma Ikraam kwana tayi da zazza6i” Haj. Kareema dake sauraron Mami ta ce “Ai gara kuyi nesa da ita” Mami ta ce “To kinga, ina dalili zata dinga min zarya a gida kaalan ta cuci ‘ya’yana ta ya6a musu ciwo”.
Rafi’ah na zaune gefen Mummy tana matsa mata kafa ta ce “Doctor yace zaizo gaisheki, kuma wai zai kawo maki maganin ciwan kafa, inaga wanda kike shafawa zaki barshi ki gwada wannan” Mummy ta mike zaune ta ce “To Allah ya kawo shi, Yusuf akwai hankali da nutsuwa dan Allah Rafi’ah karki watsa masa kasa a ido, ya soki tsakani da Allah, ki zauna da matarsa zuciya daya, ba ruwanki da kishiyarki ce kiyi iya kokarinki a kanta, i know u are good in caring but pls ki dage kinji Mamana” tana murmushi ta daga kanta ta ce “Insha Allah Mummynah, mezan dafa miki?” Mummy ta ce “Yanzu dai tinda nayi wanka ki hadamin tea, amma lipton kawai da lemon tsami banda sugar” Rafi’ah ta ce “To bari naje” daga haka ta mike ta fito a parlorn Mumny, yanzu kam ba kowa zaune a parlorn Abi, ta wuce kitchen ta dauka mug ta dauraye sannan ta debi ruwan zafi a flask tasa liptopn, tana bude fridge Mami ta shigo, cikin sauri ta ce “Ke dakata” Rafi’ah ta dago kanta tana kallanta, Mami ta rufe fridge din ta ce “Ba kowa ake bari ya bude fridge dinba, ga cututtuka sunyi yawa a duniya, kowa saiya da6a hannunsa a handle din ya bude, irin haka ai sai a dauki cuta” gefe Rafi’ah ta koma tana kallan yadda take goge handle din Fridge din da towel, bayan ta gama ta gefar da towel din ta bude fridge din tana kallan Rafi’ah ta ce “Me zaki dauka?” A hankali ta ce “Leman tsami” Mami ta dauko leman tsami daya ta ajiye mata a kan drawer ta ce “Dama daga yau kina kiyayewa duk abinda kikasan in kin ta6a wani zai ta6a wajen ki barshi kawai, ga mai aiki ki sata tana miko miki” sauke kanta tayi cikin cool voice dinta ta ce “Mami nifa banda wani cutar da za’a dauka” wani kallan rashin mutunci Mami ta mata ta ce “A hakan, ki kalleki fa, to nidai bazance komai ba, amma dai ki kiyaye duk abinda na fada miki, ciwan zuciyar da akace idan mutum yana dashi ka ta6a guminsa kaima saika kwasa fa?” tana rife bakinta ta fice a kitchen din Rafi’ah ta bita da kallon mamaki, kallan leman tsamin ta dinga yi kafin ta dauka ta wanke sannan ta dauki wuka ta yanka shi biyu, tana matsawa cikin tea din wasu hawaye masu zafi suka shiga sakko mata, yanzu har itane za’a ce bazata ta6a waje ba kar ta shafa musu cuta, to cutan me take dashi bayan ciwan zuciya? Shikuma tasan heredity ke kawoshi mostly, dan itama a familyn Abbanta ta gada, Jin kamar footsteps a bayanta yasa tayi saurin goge idanta ta dauka tea spoon, tana juyowa suka hada ido da Jawad, tayi saurin sauke kanta kasa tabi ta gefensa ta fita. Tana kaiwa Mummy tea din wayarta ya hau ringing, ta ciro a jaka sannan ta daga call din, “Ok” kawai tace sannan ta kalli Mummy ta ce “Yazo” Mumny ta ce “To ki shigo dashi parlorn Abi ba sai ya shigo ciki ba” ta ce “To” sannan ta zura hijabinta ta fita, a bakin gate ta sameshi ya jinginu da motarsa hannunsa rike da key, yaci manyan kaya yayi kyau sosai, ta sauke kanta kasa ta ce “U are welcome” ya ce “Thank u Baby, what’s wrong with ur eyes?” Ta ce “Daxu abu ya fadamin” ya ce “Ayyah sorry, hope ya fita?” Ta daga masa kai, ya ce “Alhamdulilah”, ta dan kalleshi ta ce “Ka shigo ku gaisa” ya ce “Ohk” daga haka ya bude mota ya ciro carton din Malt da leda cike da Apple, yana shigowa gate man ya kar6eshi, da sallama suka shiga parlorn, gate man ya ajiye abubuwan sannan ya fita Yusuf ya zauna kaan carpet yana kallan hoton Jawad dake manne a wall, ba jimawa Mummy ta fito Rafi’ah na biye da ita, tana murmushi ta zauna, ya sauke kansa kasa ya ce “Ina yini Mummy?” Ta ce “Lafiya Yusuf ya aiki kuma” ya ce “Alhamdulillah, ya karfin jiki?” Ta ce “Jiki yayi sauki, Allah ya saka da alkhairi” a hankali ya ce “Ameen” sannan ya ciro maganin ciwon kafan ya ajiye mata a gefe. Sun dan jima kafin Mummy ta shiga ciki, Rafi’ah ta zagayo ta zauna kusa dashi ta ce “Ya Anty Jiddah fa?” ya ce “Tana nan lafiya, yaushe zamuje wajen Ammi ne, ta damu kije mata” a hankali tayi murmushi ta ce “Ko ranar Monday inna dawo a school” ya ce “To Allah ya kaimu” mikewa tayi ta nufi fridge din parlor ta bude ta dauko mirinder da coke sannan ta dora akan tray ta dauki glass cup, tana juyawa Mami ta fito daga part dinta, ta dinga kallanta kafin ta ce “Ke wai wacce irin dabbar yarinya ce, ba ance miki karki sake ta6a mana fridge ba” still tayi waje daya jikinta na rawa, Mami ta kar6a tray din hannunta ta ajiye akan dinning ta ce “Haba, mace kamar mayya, aiko maye yana gane magana wani lokaci” Yusuf dai na zaune yana bin Mami da kallo, Rafi’ah ta koma ta zauna a hankali duk jikinya a mace, ganin sun hada ido da Mami ya ce “Ina yini” ta dalla masa harara, Yusuf ya mike yana kallan Rafi’ah da kanta ke kasa ya ce “Dear, i’m going” daga haka ya nufi kofa, kallan Rafi’ah Mami tayi ta ce “Dama karuwancin naki ba iya gidanku ya tsaya ba harda gidan mutane?” Caak Yusuf ya tsaya jin abinda ta fada, nan da nan hawaye suka shiga sakkowa a idan Rafi’ah, Yusuf ya juyo a hankali yana kallan Mami ya ce “Mama niba mazinaci bane, kuma abinda kika fada saam bai dace ba, saboda baki da shaidar abinda bakinki ya furta” Mami ta ta6e baki ta ce “Idan kai ba mazinaci bane ai ita kowa yasan nata, to tinda tare na ganku ai zance duk kanwar ja ce” Yusuf ya dinga kallan Mami with much surprise ya ce “Mama!!!”, bude kofar akai Jawad yayi sallama, Mami ta saki kuka ta zauna akan kujerar dinning, Jawad ya karasa kusanta da sauri ya riko hannunta ya ce “What’s wrong Mami?” Ta dago fuskarta hawaye sha6e sha6e ta ce “Wallahi wannan bawan Allan ne Jawad ya cimun mutunci, daga gani ma shaye~shaye yake, saboda kawai nace bako baka gaisuwa ne” nan da nan Jawad ya mike ya daga hannu yayi kaan Yusuf, Rafi’ah ta fashe da kuka, dai dai nan Mummy ta fito a part dinta da sauri har kamar zata fadi… [7/29, 2:12 PM] My Imaan: *_…卮乇賷賰 丨賷丕鬲賷…_*
_{MY LIFE PARTNER}_

*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
_We are here to Educate, Motivate and Entertain our Readers._

_By FATIMA 鉁嶐煆籣

_32_

Rike hannunsa Yusuf yayi yana kallan eyeball dinsa da sukai jaa ya ce “How there you?” Jawad ya kwace hannunsa ya cakumi wuyansa yana huci, salati Mummy ta saki tana kallansu ta ce “Na shiga uku, Jawad me nake gani haka?” ganin Mummy yasa Yusuf baiyi attempting ta6a shi ba, Mummy ta janye Jawad gefe tana kallansa ta ce “Maiya faru ne Ahmad?” Juyawa yayi ransa a 6ace ya shige dakinsa, dan shima indai a gaban Mummy ne he can’t do anything, Mummy ta kalli Rafi’ah dake kuka sosai sannan ta ce “Ikon Allah, me yake faruwa ne haka?” ganin hankalinta ya tashi yasa Yusuf ya gyara wuyan rigarsa yana kallanta with a little smile ya ce “Ba komai fa Mummy, Allah ya kara sauki” daga haka ya juya ya bude kofar parlorn ya fita. Mami ta dago kanta tana dariya kasa~kasa ta shige part dinta Mummy ta bita da kallo, saam ita kanta ya kulle, she is totally disturb to know what’s happening, kama hannun Rafi’ah tayi suka shiga part dinta, Mummy ta ce “Ki rifemin baki ki fadamin meya faru?” Goge hawayenta ta shigayi sannan ta bata labarin abinda ya faru tin zuwanta kitchen da zata hada tea har zuwa karshe, Mummy da ranta ya gama 6aci ta dauko wayarta tayi dailing number Abi.
duk ilahirin gidan na zaune parlor kowa ransa ba dadi musamman Jawad da har yanzu idanuwansa basu dawo dai dai ba, Mummy ce ta fito Rafi’ah na biye da ita a baya, caan gefe ta samu ta zauna kanta a kasa, Mummy ta zauna gefen Mami dake taunar chewing gum tana girgiza kafa, Abi yayi gyaran murya yana kallan Rafi’ah ya ce “Repeat what u just told me Fatima” a hankali ta dafe kirjinta jin zuciyarta na bugawa, Abi ya ce “Talk now” a hankali ta kara fadan duk abinda ya faru kamar yadda ta fada masa a farko, Jawad ya dago with shock yana kallanta sanda tace Mami tace mata karuwa, bayan tayi shiru ta dinga goge hawayen idanta da veil dinta, Abi ya juyo yana kallan Mami data juya masa keya ya ce “Amma kinsan girmanki ya fadi a gaban ‘ya’yanki ko Hadiza?” kin juyowa ta kalleshi tayi, Abi ya ce “Ai duniya ce watana u will regret all this, kin kira ‘yar mutane da karuwa, kin tafka abin kunya a gaban ‘ya’yanki wanda nasan har abada wancen yaro bazai miki kallan uwa me daraja ba, you hurt me today Hadiza, saboda haka kije gida saina nemeki” daga ita har ‘ya’yanta suka kalli Abi with shock, Jawad kadai ne kansa na kasa ya kasa cewa komai, Mami ta mike kamar zata tashi sama ta shige part dinta, Abi ya girgiza kai ya ce “Allah ya kyauta” daga haka ya mike yana kallan Mummy ya ce “Zan fita” ta ce “Allah ya kiyaye” mikewa Sadeeq yayi ya ce “Bari in sauke ka” daga haka ya bi bayansa suka fita, mikewa Jawad yayi ya wuce dakinsa, Ikraam dai na zaune banda kuka ba abinda take, caan ta mike ta wuce part dinsu, Rafi’ah kam duk jikinta yayi sanyi, musamman hukuncin da Abi ya dauka, idan ta tuna a sanadinta ne sai ta fashe da kuka, bayan awa daya Mami ta fito da katoton akwatinta Ikraam na biye da ita suka fita a parlorn. Ranar dai haka suka kwana duk gidan shiru, hatta ita Mummy jikinta yayi sanyi, ballantana Jawad, kwana yayi baiyi bacci ba yana tina abinda Rafi’ah ta fada, kuma duk ba wanda yaji bazai faru ba, yasan Maminsa zata iya aikata abinda yafi haka ma, ya dafe kansa yana addu’ah ciki ciki, da asuba yayi alwala ya wuce masallaci, tare suka dawo da Abi amma ko magana basuyi ba, ko daya gaisheshi ciki ciki ya amsa, hakan ya tabbatar masa Abi yana fishi dashi sosai. Tinda ya dawo dakinsa ya kwanta yake juyi, gaba daya ya rasa
abinda yake masa dadi, sai kusan karfe 8 sannan bacci ya daukeshi. Zaune take akan kujera duk ta takure waje daya, Mummy dake kallanta ta ce “Ki tashi kiyi breakfast” girgiza kanta tayi ta ce “I’m going home, banasan cin komai” Mummy data lura duk a tsorace take ta ce “To shikkenan, ga 500 kan kujera ki hau cab” a hankali ta mike ta dauka kudin, ta wuce daki ta dauko jakar kayanta sannan ta fito ta ce “Sai anjima” Mummy ta ce “Ki gaishe su” tana fitowa a parlorn ta sami Sadeeq zaune akan kujera yana waya da Mami, ta sauke kanta kasa ta ce “Ina kwana” ya amsa mata sannan ta bude kofar parlorn ta fita, a tsorace ta dinga tafiya a compound din harta iso bakin gate ta bude kofa, komawa baya tayi da sauri ganin Jawad tsaye a wajen, ta juya zata koma ciki ya kamo hannunta, kuka ta farayi tana kallan idansa da suka kumbura alamar dai yayi kuka, cikin kuka ta ce “Dan Allah kayi hakuri Ya Jawad, i caused all this, ni bansan haka zai faru ba da wallahi bazan fadi gaskiya ba” limshe idanuwansa yayi kafin ya budesu a kanta ya ce “Keep quite now” tayi shiru tana goge hawayen idanta, ya ce “U caused nothing, dama haka Allah ya tsara koda bakya nan may b zata tafi, And i don’t want to see that guy in this house again, let him be on his own, ya kuma kyaleki idan kina gidan nan” a hankali ta daga masa kai, ya ce “Ina zakije?” Ta ce “Zan tafi gida ne” ya ce “Let me drop u” daga haka ya sake hannunta ya bude motarsa dake waje, ajiyar zuciya ta sauke dan a tinaninta dukanta zaiyi da farko, ta bude front seat ta shiga yaja motar suka tafi. Suna hawa main road ya ce “How old are u?” A hankali ta juyo ta kalleshi, shiba kallanta yake ba sai driving kawai yake idansa akan titi, yana juyowa tayi saurin juyawa ta ce “17” baice kara cewa komai ba har suka iso gida, yayi parking yana kallan wayarsa dake haske, ganin Mami ke kira yasa ya rage volume ya kifa phone din, ta sauko a motar ta ce “Nagode” daga haka ta wuce cikin gida, sai daya ga ta shige sannan yaja motarsa yayi gaba. Tana shiga cikin gida ta ajiye jakar a parlor ta gaishe da Ummi sannan ta wuce kitchen ta hada tea ta dawo ta zauna, bayan ta gama ta dauki jakarta ta haura upstairs zuwa dakinta.
Karfe 2 Jawad ya tashi daga nauyayyen baccin daya daukeshi, wanka yayi ya shirya cikin kananun kaya, sunyi masa kyau sosai, ya dauki key din motarsa da phone dinsa ya fito a dakin, yana bude kofar parlorn suka ci karo da Abi, yayi saurin ja baya yana shafa gashin kansa ya ce “Sannu da dawowa Abi” Abi ya zauna kan sofa ya ce “Come back here” Jawad ya koma ya zauna akan carpet Abi dake kallansa ya ce “Where are u heading to?” Silently ya ce “Gidan kawu” Abi ya ce “Ohk, and i’m sorry with the decision i take, gara taje gida ta huta kafin ta dawo” a hankali ya ce “Toh” Abi ya ce “Ka kuma rage wannan gashin naka, ko kunya bakaji a cikin bokanka da wannan gashin” ya dan shafa kansa yana murmushi ya ce “Insha Allah” daga haka ya mike ya fice a parlorn, parking lot ya nufa ya bude motarsa ya shiga sannan yayi horn aka bude gate ya fita. Minti 20 ne ya kaishi gidan kanin baban Mami, yayi parking a waje sannan ya fito ya shiga gidan, ba kowa a compound din gidan sai mota kwaya biyu, knocking kofar ya farayi a hankali yana kallan flowers, bayan an bude ya wuce ciki ba tare daya amsa gaisuwar da me aiki ke masa ba, dakin dake farko ya bude, Ikram ce ciki sai Muhibba, kafin su gaishe shi ya ce “Ina Mami” Ikram ta ce “Tana dakin Mama, ina yini” ya ce “Lafiya” daga haka ya fice a dakin ya shiga dayan, Mami ce kadai a dakin tana waya da Haj. Kareema, ganin Jawad yasa tayi hanging wayar tana masa wani kallo, ya zauna a bakin gado ya ce “Ina yini” a fusace ta ce “Ban wuni ba, aida ubanka yace na taho gida bakai wani abu a kai ba, ko ayi hakuri baka ce ba, sannan nayi ta kiran wayarka baka dauka ba, tin sassafe Sadeeq yazo ya gaisheni amma kai da yake asara ta maka yawa sai yanzu kazo karfe 3 saura” limshe idanuwansa yayi yana jin haushin yadda take daga murya duk ilahirin gidan suna ji, ya sauke murya caan kasa ya ce “Kiyi hakuri, i don’t mean to hurt u, bacci ne ya daukeni saboda jiya banyi ba” ta wani hade rai ta ce “Uban me ya hanaka baccin?” Juyowa yayi yana kallanta kafin ya ce “Abinda naji” ta ce “Bangane ba” ya ce “Abinda Fatima ta fadawa Abi, Mami this isn’t fair, kinsa na aikata abin kunya kuma…” a mungun fusace ta ce “To ka dokeni Ahmad, yimin shegen duka sannan ka min fadan, ai fada kadai ba zai maka maganina ba” Haj. Fatima matar Kawu ce ta shigo dakin da sauri, tana kallan Mami ta ce “Lafiya Hadeeza kike ta ihu haka?” Cikin 6acin rai ta ce “Wannan wawan ne mana yakesan 6atasan rai bayan wanda ubansa yamin” Haj. Fatima ta ce “Kiyi hakuri dan Allah ki daina fada haka, da kannensa fa a gida” Mami ta nuna masa hanyar waje ta ce “Get out now” shi dai kansa na kasa yana zaune, Haj. Fatima ta ce “Jawad jeka kawai anjima ka dawo” tashi yayi a hankali ya nufi kofa Mami taja tsaki ta ce “Sai anyi magana yayi ta sauke kai kamar baya magana, nan kuwa idan ya fada miki magana sai kinyi mamakinsa” shidai bai juyo ba ya fice a dakin ya rufo mata kofar.
Da yamma Rafi’ah na zaune akan dinning wayarta ya hau ringing, murmushi tayi ganin Yusuf ne tayi picking call din hade da sallama, ya ce “How are u Baby?” Ta ce “I’m fine” ya ce “Zaki iya fitowa ina waje” ta ce “Ohk ina zuwa” hanging call din tayi ta mike ta haura sama, dakinta ta shiga ta saka Himar dinta sannan ta wuce dakin Ummi, a hankali ta bude dakin ta shiga, Ummi ta ce “What’s it?” ta sauke kanta kasa ta ce “Doctor ne ya kirani wai yana waje” Ummi taci gaba da abinda take ta ce “Don’t stay long” ta ce “Ok” sannan ta fita a dakin, wayarta ta dauka akan dinning bayan ta sakko sannan ta fita a parlorn, yana tsaye kamar yadda ya saba suna hira da Mustapha, ya sakar mata murmushi ya ce “Kinyi kyau” Mustapha ya shige ciki yana cewa “Ai oga taka ce insha Allah” murmushi Rafi’ah tayi ta ce “Kaima kayi kyau, ya shiye shirye?” ya ce “Alhamdulilah, how was yesterday nasan kinyi kuka sosai ko?” Ta sauke kanta tana wasa da fingers dinta ta ce “Not much” ya ce “To ki dinga hakuri, ita rayuwa haka take, u don’t bother much” ta ce “Hakane” ya ce “And shi kuma wannan yaran ya fita a rayuwana, dan wallahi idan ya kureni he won’t feel good, na tsane shi i really hate him with passion saboda haka let him not come into my life again” kallansa kawai Rafi’ah take jin yace yaro, tasan dai idan Jawad bai girmeshi ba to there are age mates, hancinta yaja ya ce “I luv u” tayi saurin janye fuskarta tana murmushi ta ce “Same to u” ya ce “Dama Invitation card na kawo wa Abba na daurin aure, dazu dana kira na gaishe shi yace he will come on Thursday” kar6a card din tayi tana jujjuya shi ta ce “Alright” ya ce “I’m going, zanje caan gidana Umma na kirana” ta ce “Safe, Allah ya kiyaye hanya” ya ce “Ameen” ya bude motarsa yana kallanta ya ce “Ya jikin Mummy?” Yana rife bakinsa Jawad yayi parking a gefensa, har lokacin idansa basu dawo dai dai, gashi Mami ta kuma 6ata masa rai, dauke kanta tayi akansa ta kalli Yusuf ta ce “Taji sauki ma sosai” ya ce “Haka akeso, sai munyi waya” daga haka ya shige motarsa ya kunna ya fara reverse, fitowa Jawad yayi yana kallan Rafi’ah ya ce “Ummi na ciki?” shiru tayi ganin Yusuf yayi parking ya nufo inda suke tsaye yana yiwa Jawad wani shegen kallo…

_08103810398_
[7/30, 9:03 AM] My Imaan: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation
*_…卮乇賷賰 丨賷丕鬲賷…_*
_{MY LIFE PARTNER}_

*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
_We are here to Educate, Motivate and Entertain our Readers._

_By FATIMA 鉁嶐煆籣

_33_

Gently Yusuf ya karasa inda suke ya kalli Rafi’ah sannan ya ce “Go inside” ta juya duk jikinta a sanyaye ta shige gate, dan murmushi Jawad yayi bai ko kalli inda yake ba yabi bayan Rafi’ah, tana nan tsaye bakin gate tana lekawa to see if they will quarrel, saurin ja da baya tayi ganin Jawad ya turo gate din, ta sunkuyar da kanta ta fara kame~kame ta ce “I’m…looking for my….for my earring…it just fall down here” durkusawa tayi ta dinga bin interlock din da ido, Jawad ya dinga kallanta kafin a hankali ya ce “Fatima” dagowa tayi ta kalleshi ya ce “U are just 17 and i’m 35 so don’t think zaki iya min karya ban gane ba, and don’t forget my profession, daga yadda mutum yayi magana i know if he’s lying, kawai kice kina kallan wancen mutumin ne” dan zaro ido tayi ta ce “Laa nifa ba shi nake kalla ba, na leka ne naga ko zaka shigo” murmushi Jawad yayi yana kallanta ya ce “This is strictly no, bani card din hannunki nagani” mika masa tayi sannan ta sauke kanta kasa tana ta wasa da zoben hannunta, sai daya karatanta tass sannan ya mika mata ya ce “And u are happy ko?” Ta girgiza kai sai kuma ta ce “That’s God plan” Jawad ya dinga kallan pink lips dinta dake motsi a hankali lokacin da take magana, shafa kansa yayi ya dauke idansa a kanta ya ce “Haka dai kika za6awa kanki, but ai there’s a way out, u can leave him and find another love” noke kafada tayi ta dan turo baki kafin ta ce “No, ni dai a’a” Jawad ya dinga kallanta with passion, juyawa yayi ya nufi cikin gida tabishi da ido kafin ta kara turo baki tabi bayansa. Ummi na zaune a parlor Abdul yayi pillow da cinyarta Jawad ya shigo da sallama, Ummi ta daga Abdul a jikinta tana murmushi ta ce “Barrister” murmushi shima yayi ya zauna akan carpet, dai dai lokacin Rafi’ah ta shigo da card a hannunta ta wuce upstairs, ya sauke idanuwansa daga kallan Rafi’ah ya ce “Ina Yini Ummi” ta ce “Lafiya kalau Ahmad, how is work? kwana biyu baka leko mu ba” shafa kansa yayi yana murmushi ya ce “Aikine yanzu yakemin yawa” ta ce “To Allah ya taimaka ya bada sa’a” ya ce “Ameen”, kwalawa Rafi’ah kira Ummi ta shiga yi, bayan ta sauko ta tsaya bayan kujera ta ce “I’m here” Ummi ta ce “Ki kawowa Ahmad abinci” juyawa tayi zata nufi kitchen Jawad ya mike ya ce “Zan wuce ne dama” Ummi ta ce “Abincin fa?” Ya ce “Fitowana naci abinci, and na samu call daga court” Ummi ta ce “To nagode Jawad, Allah ya saka maka da alkhairi, kana da kokarin zumunci keep it up” murmushi yayi ya fita a parlorn byan ya sake mata sallama.
Shirye~shirye Umma keta yi baji ba gani, kai kace Anty Khadija ce me yin auren, komai ta gani tace za’a raba a biki, musamman da yanzu biki ya rage saura kwana biyu, sai dai duk abinda take siya aljihun Yusuf ne yake yin kuka, kuma ko kadan baya nuna gajiyawarsa dan dai su rabu lafiya. Sai ranar Friday su Abba suka dawo Kano saboda aiki daya masa yawa, Mustapha ne ya daukosu a airport, bayan sun dawo yayi parking ya ciro karamar jakar Abba a boot ya nufi cikin gida, Anty Amina ta wuce apartment dinta, da sauri Ikleemah ta fito ta rungumeta ta ce “Anty gidanma ba wani datti fa, harna sallami me aikin ta tafi” Anty Amina ta ce “Uwarki bata zo ba ko?” Ikleemah ta ce “Sai anjima tace zata zo” daga haka Anty Amina ta kama hannunta suka wuce ciki. Rike da hannun Abdul Abba ya shigo parlor, Ummi dake kitchen ta fito tana murmushi ta ce “Ur welcome” ya ce “Thank u Madam, how is everyone?” Ta ce “All fine, sannu da hanya” daga haka ta daga masa cushion din kan kujera ya zauna, kan Abdul ya shafa ya ce “Babana ka fara tara gashi ko?” Abdul ya danyi murmushi ya ce “No, zanyi aski anjima” fitowa Rafi’ah tayi a kitchen ta dan zauna akan carpet ta ce “Sannu da dawowa Abba” hannunsa ya mika mata ta saka nata a ciki sannan ya ce “Come close Mamana i missed u, how are u?” Kanta na kasa sosai ta ce “Fine Abba, ya hanya?” Ya ce “Alhamdulilah” daga haka ya bata side hug, duk sai taji kunya sosai, bayan ya saketa ta koma gefe ta ce “Abba baka siyo mana Apple din nan ba” ya ce “Na siyo mamana, ki duba boot inaga basu fito dashi ba” har zata fita Abba ya ce “Come back, let ur brother go” daga haka ta dawo Abdul ya mike ya fita, kiran da Ummi ke mata yasa ta fasa zama ta wuce kitchen. Ummi ta mika mata carrot ta ce “Ki gyara sai ki hada komai ki kai dinning, after then sai ki daura wancen naman” turo baki tayi dan tin safe take aiki a gidan nan, duk ta gyara ko ina tayi mopping sama da kasa, kafin ta gyara kitchen suka dora abinci, Ummi dake hararanta ta ce “Idan ba zakiyi ba u let me know, ai ba yau na saba yin komai da kaina ba” daga haka ta fice a kitchen din, turo baki ta karayi ta dauko chopping board ta fara yayyanka carrot din, ta kusan gamawa kenan mistakenly ta yanka yatsanta na hagu, ta saki kara sosai ta jefar da knife din a kasa, da sauri Ummi ta shigo tana kallanta ta ce “What’s that shouting for Rafi’ah?” Rafi’ah ta fashe da kuka tana nuna mata yatsanta, Ummi ta dinga kallan yatsan da yankan ma is not that deep, jinin ma dan kadan ne ta fito, wukar ta dauka ta ci gaba da gyara carrot din bata kulata ba, Abba ne ya shigo rike da newspaper ya ce “Ya akai ne?” Ummi ta ce “Ba komai, ta tsorita ne” Abba ya juya ya ce “Alright, be careful Mamana” harara Ummi ta maka mata ta ce “Fita min a kitchen” ta goge hawayen idanta ta ce “Ummi zafi yakemin fa” cikin tsawa Ummi ta ce “I said get out here, dama aiba niyyar yi kikayi ba” tana fita a kitchen din Abba kuma ya shigo ya ce “Wai lafiya dai?” Ummi ta ce “Wai yankewa tayi shine takemin kuka, dama dai ba niyyar yin aiki tayi ba, banga abin kuka ba a wannan wajen” Abba ya kalli Rafi’ah data kifa kanta akan kujerar dinning, karasowa cikin kitchen din yayi ya ce “Pls u stop shouting at her, kiji tausayinta mana, after ciwan dake daminta kiyi ta mata tsawa, haba Ummu Rafi’ah, let her rest pls, ke kinki kuma a nemo mai aiki” Ummi dake sauraronsa ta ce “Allah ya baka hakuri, mai aiki ne banaso, sai dai idan aure tayi” Abba ya danyi murmushi ya ce “Nifa ba fada nazo muyi ba Madam, kinbi kin hade rai” a hankali ta ce “To ai kaine sai kaita nunamin kamar bani na haifi Rafi’ah ba” Abba ya ce “Pardon, amma u have to see her condition” ta ce “To” fitowa yayi a kitchen din jin phone dinsa na ringing.
Jiddah ce zaune a high table wajen Kamu, tayi masifar yin kyau, make~up very light aka mata amma kamar ka saceta a wajen, hall din babbane sosai kida nata tashi, a gaba gaba tawagar Umma take, manyan mata sun sha tsadadden lace dinsu yawancinsu da gold a neck dinsu, Anty Khadija ma ta cakare sai hotuna suke da friends dinta maza da mata, ganin Jiddah ta hade rai yasa Anty Khadija ta fara takawa steps din har inda take zaune ta ce “Ke dalla ki kwantar da hankalinki sai kace bakisan halinsa bane, Umma ta kirashi yanzun nan zakiga ya karaso” Jiddah ta marairaice ta ce “Anty dan Allah kiyi iya bakin kokarinki, Allah yaya zai iya kin zuwa ko waye ya kirashi” tashi Anty Khadija tayi ta kira number Aliyu, yana dauka ta fice a hall din saboda karan kida ta ce “Ali kuna ina ne? anata jiransa gashi har time ya tafi” Aliyu ya ce “Hajiya Anty yanzun nan zaki ganmu, muna jiran wani abokinmu ne” Anty Khadija ta ce “To kuyi sauri dan Allah, gashi karfe 7 time dinmu zaiyi expire su gyara wajen wasu zasu shiga by 8, Aliyu ya ce “Don’t mind Antyn mu gamu nan” daga haka yayi hanging call din yana kallan Yusuf dake zaune ya limshe idanuwansa, tin jiya yake kiran Rafi’ah a waya amma wayanta a kashe, Aliyu ya dafa shi ya ce “Kaifa ake jira Yusuf, sai kirana ake wallahi” Ajiyar zuciya Yusuf ya sauke ya ce “I’m not going Aliyu, sai da nace ni banason wannan kidan amma sai da akai” Aliyu ya matso kusa dashi ya ce “Yau ne fa kawai Doctor, pls entertain her baza taji dadi ba idan baka je ba” yana rife bakinsa wasu friends dinsu su shida suka shigo dakin, daga haka dai har sukai convincing dinsa yace zaije amma ba dadewa zaiyi ba, canza kaya yayi cikin milk gezna, tayi bala’in mishi kyau sosai, ga beard dinsa sun kwanta saman farar fuskarsa sai kamshi yake, daga haka suka shiga mota suke wuce shida Aliyu, sauran motoci hudun kuma suka bisu a baya. Ba karamin farinciki Jiddah tayi ganin Yusuf ba, gaba daya ta kasa dauke idanta a kansa, ta dinga murmushi tana kallansa harsu Aliyu suka rakoshi gefenta sannan suka koma table dinsu, sosai aka ci aka sha a wajen, aka cashe sosai musamman Umma da kawayenta, da kyar Yusuf ya tashi ya manna mata ‘yan 500, sannan ya juya ya mannawa Jiddah ma, Anty Khadija na rawa har zuwa wajensu ta dinga watsa musu kudi tana video, ba jimawa Ammin su Sameer ta fito itama ta dinga watsa masa kudi tana tsokalarsa, duk ‘yan uwa da abokan arziki saida suka manna masa kudi, musamman Sameer yafi kowa watsawa dan uwansa kudi, jin an kama hannunsa yasa ya juya, ya sakar mata murmushi ya ce “Khairiyyan Yaya” ta washe masa baki ta ce “Yaya banga Anty ba?” Ya ce “Wa?” Ta ce “Wannan faran, Anty wama sunanta? but you used to called her Fatima” a hankali yayi murmushi ya ce “Her name is Rafi’ah, she’s not here” Khairiyya dake kallansa ta ce “Why Yaya? Ba kace she’s ur best friend ba, why is she not presence at ur marriage?” A hankali ya ce “Soon zakiga tazo” a hankali ta sakeshi ta koma dai dai saitin kofa tana kallan masu shiga da fita ko zataga Rafi’ah amma babu, ganin Yusuf da abokansa sun fita a hall din ta 6ata fuska kamar zatai kuka, dan tasan an gama event din kenan.
Da dare Rafi’ah nasan kunna wayarta amma taki sabida batasan kiran Yusuf ya shigo mata, haka nan ta hakura har bacci ya dauketa. Washegari ya kama Sarurday, sassafe ta kunna wayarta ta masa text sannan ta kashe wayar ta sauko dan taya Ummi aiki. Yusuf na zaune a dakin Aliyu text din ya shigo, ya gama karantawa sannan yayi murmushi, ji yake duk duniya babu wacce yakeso irin Rafi’ah” Aliyu dake kallansa ya ce “What’s that” Yusuf ya ce “She send me message now, that i shouldn’t worry, ta bani time ne nayi hidimar aure naji da baki” Aliyu ya ce “Yanzu hankalinka ya kwanta kenan? Sai kayi baccin da bakayi da daddare ba kafin lokacin daurin aure yayi” Yusuf ya ce “But ba haka naso ba, i need to hear her voice, i missed her much” Ali ya ta6e baki ya ce “Kasan dai bazaka je wajenta a yau ba kam, ba kuma gobe ba, ba jibi ba, sai dai ko gata” Yusuf ya kai masa duka ya ce “Karka kaini har gata Malam, jibi zanga abata” daga haka ya kwanta yana murmushi jin answer da Aliyu ya bashi. Karfe 10 Abba ya fito cikin shirinsa na alfarma yayi breakfast sannan yayi wa Ummi sallama zai tafi daurin auren Yusuf, ta masa Allah ya kiyaye sannan ta ci gaba da gyaran dakinta. Jawad ne tsaye a kofar gidansu Aliyu ya jinginu da motarsa, Aliyu ya fito ya mika masa hannu ya ce “Barisster always behaving somehow, tinba yau ba muke tare amma sai kazo kayi parking a waje, kuma wallahi Mama jiya sai data tambayeka” Jawad ya danyi murmushi ya ce “Zanzo na gaisheta but gobe insha Allah” Aliyu ya ce “Allah ya kaimu, zakaje daurin auren Yusuf ne?” Harara Jawad ya dalla masa ya ce “Kai din dai daya zame maka dole, over my dead body” Aliyu ya dinga dariya ya ce “Pls, yana ma ciki yana shiryawa, kaga kaima kaci manyan kaya kuma kayi kyau sai dai ba babban riga” Jawad ya bude motarsa ya ce “Pls let me go Ali, nima daurin auren wani zanje, tare mukai masters” Aliyu ya ce “Friend dinka?” Jawad ya kalleshi sannan ya kunna motarsa ya ce “Kasan banda friends, i only have good mates” Aliyu na daga masa hannu yana dariya ya ce “Allah ya shiryeka kai dai, still dai friends din ne” Jawad baice komai ba ya juya kan motarsa ya nufi gidan Kawu daga nan ya wuce. Karfe 11:30 aka daura auren Yusuf Muhammad da Hauwa Sa’eed (Jiddah), uncountable people sun shaida dauruwar wannan aure, bayan nan akaci akasha sannan kowa ya watse. Yinin Ranar Rafi’ah a daki tayi shi tana kallo, duk da abin na damunta but she’s just trying to calm herself musamman da taji muryar Abba ya dawo, lokaci lokaci Ummi kan lekata taga kallo take hankali kwance, nan kuwa ita kadai tasan abinda ke daminta deep down. Bayan isha aka shirya amarya tsaf dan kaita dakinta, Umma tayi mata fada sosai da sosai a gaban jama’a, Jiddan na kuka haka aka tafi da ita gidan Yusuf, gidan yayi kyau sosai komai sabo ga kamshin turaren wuta dake tashi. Yusuf na zaune dakin Aliyu Sameer da wani abokinsu Mukhtar suka shigo, Sameer ya mika masa ledan kaza da fresh milk ya ce “Karfe 10 saura fa Yusuf, muje mu raka ka mu wuce gida” Yusuf ya mike suka fita, shima kansa jikinsa duk yayi weak, gani yake kamar Rafi’ah fishi take dashi. Har karfe 12 Rafi’ah batai bacci ba, da taji motsin Ummi zatai pretending kamar bacci take, har Ummi ta rufeta da blanket ta fita ko motsi batai ba, Ummi na fita ta mike ta zauna, sai a sannan hawaye ya gangaro idanta, tayi saurin sharewa sannan ta mike ta shiga toilet tayi alwala ta dawo tasa himar ta tada sallah. Washegari wajajen karfe 10 Jawad ya fito daga dakinshi ya nufi dakin Abi, yana nan zaune da newspaper a hannunsa yana karantawa, Jawad ya durkusa ya ce “Ina kwana Abi” Abi ya ajiye newspaper hannunsa ya ce “Lafiya kalau Ahmad, yau bazaka fita bane?” A hankali ya ce “Zan fita amma sai da yamma” Abi ya ce “Masha Allah, yau na kira Kawunka nace Maminku ta dawo” murmushi ya danyi ya ce “Allah ya saka da alkhairi Abi, Allah kuma ya kara kiyaye gaba” Abi ya ce “Ameen” shafa kansa Jawad yayi ya rasa ta ina zai fara wannan maganar, caan dai yayi karfin hali ya ce “Abi dama inaso muyi magana ne” Abi dake kallansa ya ce “Go on Son i’m all ears”…

_08103810398_
[7/31, 10:43 AM] My Imaan: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation
*_…卮乇賷賰 丨賷丕鬲賷…_*
_{MY LIFE PARTNER}_

*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
_We are here to Educate, Motivate and Entertain our Readers._

_By FATIMA 鉁嶐煆籣

_34_

Shiru Abi yayi bayan Jawad ya fita, he can’t believe this is what Jawad is seeking for, in dai kuwa hakan ya tabbata zaifi kowa farinciki, tashi yayi yana kallan clock din dake jikin wall sannan ya wuce dakinsa. Jawad bai tsaya ko ina ba sai gidan Kawu, bayan ya shiga gidan parlorn Kawu ya fara shiga ya gaishe shi sannan ya wuce dakin Mama, suna zaune ita da Mami bayan sun gama breakfast suna dan hira, Jawad na shigowa Mami ta hade rai kai kace ba ita ke hira tana dariya ba, a hankali ya zauna a kan carpet yana kallan Mama ya ce “Ina kwana” ta ce “Lafiya kalau Ahmad, ya mutanen gidan?” Ya ce “Kowa lafiya” daga haka ya dan kalli Mami ya ce “Good morning mother” ciki ciki ta ce “I’m fine” ya ce “Masha Allah” Mikewa yayi Mama ta kalleshi kafin ta ce “Bari Muhibba ta kawo maka breakfast” dan shafa kansa yayi yaja baya ya ce “Nayi breakfast Mama, zan wuce kawai” ta ce “To Allah ya kiyaye” daga haka ya kalli Mami ya ce “Sai anjima” bata amsa shi ba saima harara data bishi dashi harya fita a dakin, Mama ta ce “Bafa hake ake yiwa d’a ba Hadiza, jaan sa zakiyi a jiki amma ba ki dinga masa fada haka ba, yanzu fisabilillahi Jawad me shekara 36 dinne zaki zauna kina masa fada kamar Ikram” Mami ta ta6e baki tana kallan Mama ta ce “Kinga shi Jawad idan damuwa ya shiga bazai ta6a fada min ba, sai yayi ta shiru shiru ke kyace na Allah ne, wani lokaci sai ya gayawa matar ubansa abu ni bai fadamin ba” Mama ta ce “The best solution kawai yayi aure” Mami ta dan zaro ido ta ce “Aini bana tinanin yana hira ma wannan yaran, tinda nake da Jawad bai ta6a kawomin wata yace ta gaisheni ba, ke ko a waya ne, kinga kuwa ai watakila an sa mana hannu, amma idan ba haka ba yaro shekara 36 ace har yanzu shiru, ba aiki ya rasa ba, ga gidansa nan a gine sai aikin yin gyara ba mata a ciki, aini lamarin Ahmad yan firgitani Anty Fatima” shiru Mama tayi tana kallan Mami, caan ta danyi murmushi ta ce “Idan kin koma gida sai muyi magana” Mami ta sauke ajiyar zuciya ta ce “Toh”. Cikin shirinta na islamiyya ta fito tana kallan Abdul dake kwance saman kujera yana bacci, dogon hijabi ne har kasa a jikinta sai nikab a hannunta, jin footsteps yasa ta juya da sauri, juyowa tayi ta kara kallan Abdul dake kwance ta ce “Ummi why is he still sleeping?” ta kamo hannunsa taji da zafi, Ummi ta ce “Bashi da lafiya, ki tafi kawai” duk jikinta sai yayi sanyi, ta durkusa tana kallan fuskar lovely brother dinta, saam itama bataso taga bashi da lafiya, Ummi dake kallan idanta daya kowo ruwa ta ce “Don’t cry here Rafi’ah, ki tashi ki wuce Islamiyya” a hankali ta dafa goshinsa ta ce “Ummi what’s wrong with him, ba’a je clinic ba kuma” Ummi ta kamo hannunta tana murmushi ta ce “Stop crying daughter, insha Allah he will recover soon, munje clinic kina bacci” Rafi’ah ta share dan guntun tears dinta ta ce “Zazza6i yake yi Ummi?” Ta ce “Ehh, amma da sauki kinga yayi bacci ma yanzu” a hankali ta mike tana turo baki ta ce “Kuma baki tasheni naje ba” Ummi ta ce “To kiyi hkr, yanzu dai ki tafi karki makara” calmly ta ce “To” daga haka ta dauka jakarta akan sofa ta fita zuwa parking lot.
Sai karfe 12 Jiddah ta farka daga baccin daya dauke ta, ta dinga bude ido a hankali harta ware su duka, bata ga kowa cikin dakin ba sai dai kuma taji karar ruwa a toilet, ta mike a hankali ta zauna tana tino incident din jiya, limshe idanuwanta tayi tana jin kaunar Yusuf har cikin ranta, tana nan zaune harya fito a toilet da towel daure a waist dinsa, Jiddah tayi saurin komawa ta kwanta ganin sun hada ido, gently ya karasa kan gadon yana shafa fuskarta ya ce “How are u Jiddan Yaya?” Boye fuskarta tayi a kirjinshi tayi shiru, ya bata light kiss a forehead dinta ya ce “Thank u wife, you make me feel comfortable yesterday night” sai a lokacin ta dan dago kanta tana kallan fuskarsa ta ce “Kafa jikani da ruwan jikinka Yaya” rungumeta yayi ya dinga shafa mata sauran ruwa dake hannunsa, ta danyi murmushi ta ce “Zan rama ai” hancinta yaja yana smiling ya ce “Zamuyi dambe kuwa” ta danyi dariya ta ce “I know how to deal with u” matsowa jikinta yayi ya kai bakinshi dai dai kunnenta ya ce “And u cried yesterday night, why didn’t u deal with me” boye fuskarta tayi a jikinshi tana dariya kasa kasa, ya dagata yana kallan fuskarta ya ce “Go and bath” sauka tayi akan gadon ya dinga kallanta harta shige toilet, bin bayanta yayi ya bude toilet din yana kallan yadda ta yamutse fuska ya ce “What’s that” a hankali ta ce “Yaya my lap” ya kamo hannunta ya ce “Sorry dear, bari na hada maki ruwan zafi” daga haka ya hada mata just like he did before, bayan ya gama ya juyo yana kallanta ya ce “Ai kinga yadda mukai dazu, so u do exactly, kar kuma ruwan yayi sanyi” ta ce “To” daga haka yaja mata toilet din, few minutes ya shirya cikin kananun kaya ya dauki key din mota, yana shirin fita ta fito a toilet, kallansa ta tsaya yi kafin ta ce “Where are u going?” Ya ce “I want to get us something for breakfast” daga haka ya fice a dakin tabi shi da kallo, haka kawai kuma ta tsargu dashi, gani take kamar wajen Rafi’ah zaije, duk jikinta babu kwari ta shirya, tana shiryawa ta koma kan gadon ta kwanta, phone dinta taji yana ringing a kan stool, ta mika hannunta ta dauka sannan tayi answering call din, Anty Khadija ta ce “Ke bazaki kira mutane ki musu ya gajiyar biki bane? Tin da asuba nake kiran wayarki baki dauka ba” Jiddah ta kumburo fuska ta ce “Ban tashi bane lokacin” Anty Khadija taja tsaki ta ce “To sai ki tashi yanzu, anjima zanzo” ciki ciki ta amsa sannan tayi hanging call din, bayan nan ta kira layin mahaifiyarta, tana dagawa ta fashe da kuka ta ce “Anty kinji wai Anty Khadija zata zo min gida, dan meyasa bazasu barni na huta ba, kwana na daya fa” Mahaifiyarta da suke kira da Anty ta danyi murmushi ta ce “Yi shiru Auta, kyaleta tazo, watarana da kanta zata dauke kafafuwanta a gidanki, yanzu aka fara” Jiddah ta share hawayen idanta ta ce “Shi kuma kinga ya fice ya barni, kuma nasan watakila wajen yarinyar nan zaije” Anty ta ce “To yaje mana, nace miki yanzu aka fara wasan” Jiddah tayi shiru tana jin zuciyarta na zafi, Anty ta tausasa murya cikin rarrashi ta ce “Haba Auta, kiyi hakuri na dan lokaci ne, yanzu ki koma kiyi baccinki, kima saki jikinki gida naki ne miji naki ne” murmushi ta danyi ta ce “Toh Anty nah” daga haka sukai sallama. Duk yadda taso ta koma bacci kasawa tayi, bayan minti 30 Yusuf ya shigo rike da ledan take away, bata amsa sallamar da yayi ba saima juya kai da tayi, ya shigo dakin yana murmushi ya ce “Na siyo miki favorite dinki love” juya kai gefe tayi ta danja tsaki, ya ce “What? Na miki laifi ne?” Kin kulashi tayi ta mike ta dauka wayarta zata fita falo ya jawo hannunta ta fado jikinshi ya ce “who are u hissing” kallansa ta dinga yi kafin ta kara hade rai ta ce “Sai kaje ka rungume ita wacce kaje wajenta” da mamaki yake kallanta jin abinda tace, ya ce “Ko kin fara hauka ne Jiddah? What are u saying?” zame jikinta tayi a fusace ta ce “Abinda kaji shina fada, kuma ni ba hauka nake ba tinda banyi abinda za’a kirani da mahaukaciya ba, kaida kaje wajen wata da auranka ai kai ya kamata a kira da wannan sunan” daga hannunsa yayi zai wanka mata mari sai kuma ya sauke kasa ya zauna bakin gado, ficewa tayi a dakin hade da jan tsaki ya bita da kallo, bayan few minutes ya fara karanto Al~qur’an kasa kasa saboda ya samu saukin abinda yake ji.
Bayan mintina kalilan ya mike ya fita parlor, zaune ya sameta a kan kujera tana kallo, ya zauna gefenta ya ce “What comes over u Jiddah? u just change all of a sudden” a hankali ta juyo tana kallansa sai kuma ta ce “Kaje wajen yarinyar ai nasani” ya kamo hannunta ya ce “What is ur evidence? Ina san ganinta kam banyi karya ba, but ai yanzu lokacinki ne, i can’t leave u at this condition” harara ta balla masa ta zame hannunta cikin nasa, tana juya kanta ta fara hawaye, ya rungumeta ta baya ya ce “Sorry if i hurt u” juyo da ita yayi yana kallan fuskarta camly ya ce “This is our first day as couples Jiddah, pls don’t let shaidan deceive u” a hankali ta kwantar da kanta akan kafadarsa tana sheshekar kuka, ya dinsha shafa bayanta yana rarrashinta, ita a duniya yanzu babu wadanda takejin haushinsu irin su Anty Khadija, idan ta tuna kullukan maganin da suka bata sai taji zuciyarta na zafi, itama yanzu dama ce ta samu kuma dole tayi amfani dashi, babu abinda zaisa ta yarda su shanye Yusuf ita ta tashi a babu, kara shigewa jikinsa tayi tana limshe ido, ya dan bubbuga bayanta ya ce “Are u not hungry?” ta girgiza masa kai, dago da kanta yayi yana kallan idanta ya ce “Why? Tin jiya bakici komai ba” ta sauke kanta a kirjinshi ta ce “I will eat ltr” ya kara dago kanta ya jawota jikinshi sosai ya ce “Then we will eat together ko?” Daga masa kai tayi, ya kai bakinsa kan nata ya fara bata hot and romantic kiss…
Horn Abi yayi Mustapha ya bude gate yana daga masa hannu, bayan ya shigo yayi parking sannan ya fito, da ladabi Mustapha ya gaisheshi sannan ya tambayi Abba, Mustapha ya ce “Bari a masa magana” daga haka ya nufi apartment din Anty Amina, ba jimawa Abba ya fito sukai musabaha, yana ta murmushi ya ce “U are welcome Honorable, bismillah ka shigo” daga haka suka nufi BQ, a parlor suka zauna sannan suka kara gaisawa, Abba ya ce “Bari a kawo maka abin sha” Abi ya ce “Alhamdulilah Engineer, ba dadewa zanyi ba i have an important meeting” Abba ya ce “Ohk ba damuwa, dama ‘yan siyasa are always on meeting” Abi ya danyi murmushi ya ce “Dama wata magana ce ta kawoni, and i wish u will be happy with it” Abba ya ce “I hope so Honorable” Abi ya gyara babban rigarsa ya ce “Dama yau da safe d’an wajena Ahmad yazo min da magana ta cewa yana son ‘yarka da aure, so shiyasa naga nazo na fara maka magana kafin komai” still Abba yayi yana kallan Abi with shock jin abinda yace, ya danyi murmushi ya ce “That is not a problem Honarable…

_08103810398_

*Hello everyone 馃 i hope u are all fine? if so that’s my wish 馃グ Many people suna complain akan na rage yawan page, but u too should notice that da ina page biyu ne yanzu kuma guda daya nake saboda yanayin time,so kunga page daya ai bai kai page biyu yawa ba, that is it 馃槆 sannan masu comment are like sisters to me, i luv u so much cus d comments are melting my heart billah, Allah ya bar zumunci yasa mu karu da juna 馃げ馃徎 ku huta lafiya* .

*_…卮乇賷賰 丨賷丕鬲賷…_*
_{MY LIFE PARTNER}_

*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
_We are here to Educate, Motivate and Entertain our Readers._

_By FATIMA 鉁嶐煆籣

_35_

Abba ya danyi murmushi ya ce “That is not a problem if i didn’t made promise to someone, na riga nayi wa wani yaro alkawari and i’m sorry to say so Honorable” murmushi Abi yayi ya ce “Don’t think u did bad, cika alkawari ai abu ne me kyau, Allah yasa hakan shine mafi alkhairi” Abba ya ce “Ameen, Ameen” tashi Abi yayi ya ce “To yallaboi zan wuce, a huta gajiya” Abba ya bi bayansa with respect ya ce “Allah ya kiyaye a gaida iyali” Har mota Abba ya raka shi sannan sukai sallama, bayan ya shigo ya apartment din Anty Amina. Mami ce zaune a dakinta tana shirya kayanta cikin press, daga kai tayi dan ganin wanda zai shigo, Ikram ta zauna bakin gado ta ce “Mami kinga Ya Sadeeq ya kwacemin phone dina” Mami ta ce “Let him give u, ina Yayanku?” ta ce “Yana cin abinci a parlorn Abi” ta ce “Call him for me” tashi tayi ta fita a dakin, ba jimawa ta dawo ta ce “Yana zuwa” sannan ta juya ta fice. Few minutes Jawad ya shigo da mug a hannunsa yana jujjuya tea din da spoon, Mami ta ta6e baki taci gaba da abinda take, zama yayi a bakin gado ya ce “Gani” ta ce “Magana nakeso muyi” ya ce “Ohk i’m all ears” zama tayi tana kallansa ta ce “I want u to get marriage” da sauri ya dago kansa yana kallanta, ta ce “Yes, ka samo mata aure zakiyi” sauke kansa yayi yana kallan tea din hannunsa ya ce “Ohk” harara ta dan 6alla masa ta ce “Not just ok Ahmad, na gaji da zamanka a gidan nan, ga gidanka caan kaima kayi aure ka koma” a hankali ya ce “Insha Allah” tashi tayi taci gaba da abinda take shima ya mike ya fita a dakin ta bishi da harara. A hankali Jiddah ta mike a jikin Yusuf ta dauka scarf dinta ta saka, dago kansa yayi yana kallanta ya ce “Ina zakije?” Ta ce “Zan bude kofa, baka ji ana knocking ba?” ya ce “To ke zakije?” Zama tayi ta dan 6ata fuska ta ce “Ai nasan Anty Khadija ne” ya ce “Let me check” daga haka ya fito a dakin ta biyo bayansa, yana bude kofar parlor Anty Khadija ta shigo tana kallansu, Yusuf ya danyi murmushi ya ce “Welcome sis, have a seat” ta zauna akan 2 seater tana kallan Jiddah dake tsaye bayan Yusuf, a hankali ta zauna ta ce “Ina yini” Anty Khadija ta ce “Lafiya kalau, ya amarci?” Jiddah ta ce “Lafiya” Anty Khadija ta kalli Yusuf ta ce “Doctor ya amarci, ya kuma kwanan amarya?” A hankali ya ce “All fine” daga haka ya wuce daki. Yana shiga Anty Khadija ta kalli Jiddah ta ce “Dama sauran maganin nan na kawo miki, shine zaki hada shi dana bakin leda” tana rife bakinta ta ciro kullin magani ta mika mata, Jiddah ta dan yamutse fuska kafin ta kar6a ta ce “Ohk nagane” Anty Khadija ta ce “Yauwa, idan lokacin yayi zanyi alerting dinki” Jiddah ta daga mata kai ta ce “Ohk ba damuwa ki gaishe da Umma” Anty Khadija ta mike tana lankaya hand bag dinta ta ce “To sai anjima” daga haka ta fice a parlor Jiddah ta bita da harara hade da tsaki, jujjuya maganin ta dinga yi sannan ta ta6e baki ta mike ta cusa shi kasan cushion ta koma ta zauna, tana zaune taji Yusuf ya rungumeta ta baya, a hankali ya ce “What are u thinking?” Ta ce “Nothing” daga haka ya saketa ya dawo gefenta ya zauna, kwanciya tayi ta dora kanta akan cinyarsa tana kallan TV ta ce “Yaushe zan koma school” ya shafa kanta ya ce “Next week i think” ta ce “Allah ya kaimu” daga haka ta limshe ido.
Anty Amina ce zaune a parlor’n ta tana ta sheka dariya, Ikleemah ta fito a daki tana kallanta ta ce “Anty Lafiya?” Mika mata wayar Anty Amina tayi, Ikleemah ta dinga kallan pic din Yusuf da Jiddah na aure, duk sai taji ba dadi, ga wani haushi daya tsaya mata a wuya, ta kalli Anty Amina ta ce “Da gaske ne aure yayi?” Anty Amina ta kara shekewa da dariya ta ce “Aure mana Ikleemah, zanso naga fuskar waccen yarinyar” ta6e baki Ikleemah tayi, ita dai taji dadi ko banza Rafi’ah ta shiga kunci, ta wani bangaren kuma haushi taji, dan a yadda mafarkinta ya nuna mata ita kadaice mata a gurin Yusuf, ajiye wayar tayi ta koma daki tana jaan tsaki.
Da sallama Anty Khadija ta shigo dakin, Umma ta amsa sannan tayi hanging wayar da take ta ce “Khadija kin dawo ne?” Ta ce “Na dan jima ma ina daki ne” Umma ta ce “Kin kaiwa Jiddah maganin dai baki manta ba ko?” Zama tayi a bakin gado ta ce “Na kai mata, kinga a hankali a hankali aiki zaina tafiya” Umma ta sauke ajiyar zuciya ta ce “To saura kuma ke, dama jira nake na gama da Yusuf, ki fito da miji kema kiyi auranki” Anty Khadija ta dan ta6e baki ta ce “Umma kenan” Umma ta ce “Ba batun Umma kenan ba, shekararki fa 37 Khadija, ga Yusuf da yake 35 yayi aure ai yanzu kam kema sai ki tafi” Anty Khadija ta ce “Zan tafi ai, akwai lokaci” Umma ta ce “To Allah ya kaimu, ga Jiddah me 25 ma tayi auranta” tashi Anty Khadija tayi tana kallan Umma ta ce “Nifa har yanzu ban samu wanda raina ya kwanta da shi ba, ni inasan mijin da yake da Kudi na gani na fada, kyau, kuma wanda zai soni kamar ya mutu” Umma ta ce “To Allah ya kawo miki” ta ce “Ameen” daga haka ta fice a dakin. Rafi’ah ce zaune a gefen Abdul tana kallan yadda yake limshe ido yana juyi, ta kamo hannunsa ta ce “Abdul ko zaka ci abinci?” Ya girgiza kai, juyawa Rafi’ah tayi tana kallan Ummi ta ce “Ummi yaci abinci dazu ne?” Ummi dake kallansu ta ce “Yaci, ku fita waje ko zai dan sake” Rafi’ah ta kama hannunsa ta taimaka masa ya mike sannan suka nufi kofa Ummi ta bisu da kallo, tin dawowan ta a islamiyya bata tashi gefen Abdul ba, da yayi motsi zata tambayeshi koda abinda yake so, kana kallan Rafi’ah kasan ba karamar damuwa tayi akan rashin lafiyar luvly brother dinta ba. Ummi ta sauke ajiyar zuciya sannan ta mike ta wuce upstairs. Kujera Rafi’ah ta ajiye musu a balcony suka zauna, lokaci lokaci ta kan bashi labari ko kuma ta nuna mishi abu a waya duk dan ya dan sake, kuma alhamdullilah hakan ya masa dadi sosai, juyawa tayi jin footsteps a bayansu, ganin Ikleemah ce yasa ta juyo taci gaba da bawa Abdul labarin da take,
“To shi dama mutumin shi kadai mamanshi ta hai…” Shiru tayi ganin Ikleemah ta tsaya akansu ta kama kugu, Rafi’ah ta kauda kanta ta ce “Malama Lafiya?” Dariyar karfin hali Ikleemah ta fara yi kafin ta ce “Nazo ne na miki jaje game da abinda ya faru” Rafi’ah ta ce “Wane abu kuma?” Ikleemah ta kara fashewa da dariya ta ce “Wai kina nufin baki da labarin auran Yusuf?” Sosai zuciyarta ya buga, ta juya kanta taki kallan inda Ikleemah take, Ikleemah ta ce “To sai ayi hakuri a nemo wani, dama nasan wahalar banza kike Yusuf ba tsarar auranki bane” tashi Rafi’ah tayi cikin fishi ta ce “Mind your words Ikleemah, meye hadina dake daza ki dinga min irin wannan maganar” Ikleemah ta ce “Ai dama bance na hada abu dake ba, Allah ma ya kiyaye in hada jini da dangin cuta” tass, tass, ya sauke mata mari biyu a kumatun ta, Ikleemah ta zaro ido tana kallan Abdul dake tsaye a gabanta yana huci, yayi pointing dinta da yatsa ya ce “This should be the last zaki kira mu da dangin cuta, and idan cutan ne ai daga familyn ku ta fito, and let me keep this warning to u, Antynah isn’t ur mate, u stay far away from her, idan ba haka ba u will know the bad side of me” yana kai karshe ya dauki wayar Rafi’ah ya wuce cikin apartment dinsu, kai kace bashi ke nishin rashin lafiya yanzu ba, daga Ikleemah har Rafi’ah kallansa suke, Rafi’ah ta wuce ciki itama ta bar Ikleemah dafe da kuncinta a tsaye.
Tana shiga ta samu ba kowa a parlor ta wuce dakin Abdul ta murda handle din ta shiga, tsaye ta sameshi gaban mirror da towel a hannunsa, strictly ta ce “Why did u slapped her?” Ba tare daya kalleta ba ya ce “Because she insulted u” Rafi’ah ta ce “Don’t u ever try to slap her again, bata girmeka bane? or are u stupid” baice komai ba saima kayansa daya fara cirewa, ta ce “Kuma kasan Abba won’t take it likely ko? Yanzu da abinda ya faru da wanda bai faru ba zasu fada mishi, so kake kullum yana yiwa Ummi fada, zai ce fault dinta ne” idanta taap cike da hawaye ta karashe maganar, ita babbar damuwarta bai wuce fishin Umminta ba, shiyasa yanzu komai zai faru ta hakura zata shanye akan Abba yayi wa Umminta fada, rungumeta da taji yayi ne yasa ta dawo daga tinanin data tafi, Abdul ya kai hannunsa idanta ya ce “Pls don’t cry sister, insha Allah babu abinda zai faru” a hankali ta ce “But u slapped her Abduljalal, why?” Bayanta ya hau bubbugawa calmly ya ce “Not when they’re insulting u sis, bazan iya ganin ana insulting dinki nayi shiru ba, bama zagi ba, wallahi ko kallan banza aka miki bazan bar mutum ba, did u know how much i luv u Aunty?” Rungumeshi itama tayi tana murmushi ta ce “Idan kana sona ta kaida abinda banaso” ya ce “Ohk” daga haka ta sakeshi ta fita jin an bude kofar parlor.
Tinda Abi ya turo Sadeeq ya kira shi ya kasa nutsuwa, ya dinga kai kawo yana tinanin abinda zaije yaji, bayan minti 10 Sadeeq ya kara knocking dakin ya shigo, tsayawa yayi yana kallan yayan nasu ya ce “Abi yana jiranka fa Yaya” kai ya daga masa sannan ya bi bayansa suka fita, parlor ya fita ya zauna akan carpet yana kallan Abi ya ce “Sannu da dawowa” Abi ya ce “Yauwa son” shima shiru yayi ya rasa ta ina zai fara masa bayani, caan dai ya dago yana kallan Jawad da kansa ke kasa ya ce “Naje gidan su Fatima dazu, sai dai kuma the answer wasn’t funny saboda an riga da an yiwa wani alkawari, so u don’t worry son, kayi fatan Allah yasa haka shine alkhairinka, ya kawo maka wata da ban” tinda Abi ya fara magana Zuciyarsa take bugawa non stop, a hankali ya ce “Ameen” daga haka ya mike ya nufi dakinsa just trying to control himself, yana shiga dakin wasu hawaye masu zafi suka sauko masa, yayi saurin gogewa saboda raban da yayi kuka harya manta a rayuwarsa, ya zauna bakin gado ya kama kansa yana karanto addu’o’i, bayan few minutes aka bude kofar dakin, dagowa yayi suka hada ido da Mami, yayi saurin sauke kansa ya ce “I’m having headache” [8/3, 7:09 AM] My Imaan: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation
*_…卮乇賷賰 丨賷丕鬲賷…_*
_{MY LIFE PARTNER}_

*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
_We are here to Educate, Motivate and Entertain our Readers._

_By FATIMA 鉁嶐煆籣

_36_
*THE PAGE IS DEDICATED TO THE WHOLE MEMEBERS OF ZAMANI WRITERS ASSOCIATION* 馃挒

Shiru Mami tayi tana kallansa kafin ta ce “Since when?” Ba tare daya kalleta ba ya ce “Two hours ago” juyawa tayi ta fita a dakin, ba jimawa ta dawo da bottle water sai cup hade da panadol, zama tayi gefensa ta 6alla masa maganin ta mika masa sannan ta zuba masa ruwa a cup ya hadiye, mika mata cup din yayi ya ce “Thank u” Mami ta kar6a sannan ta mike ta ce “U rest first, idan bai daina ba sai muje clinic” kai ya daga mata sannan ta fita a dakin ta jawo masa kofa. Bayan sati daya da bikin Yusuf, Rafi’ah na kitchen tana kwashe shinkafa cikin warmer wayarta ya fara ringing, ta fito cikin nutsuwa ta dauka wayarta sannan ta koma kitchen Ummi ta bita da kallo, picking call din tayi hade da sallama Yusuf ya ce “How are u Baby?” a hankali ta ce “I’m fine” ya ce “Good, zanzo yau da yamma” dan murmushi tayi me kyau tana gyara zaman phone din a kunnenta, dan tinda yayi aure sai yau zata ganshi, waya dai kwana 3 da aure suka farayi, cikin cool voice dinsa ya ce “Or are u not happy? I missed u more than u know Baby” cikin sanyin murya ta ce “I also misaed u Doctor” ya ce “Worry not u will see me insha Allah” murmushi tayi ta ce “Allah ya kaimu” ya ce “I will call u ltr when i’m home, ina driving” toh kawai tace sannan tayi hanging call din tana murmushi. Bayan ta gama komai ta wuce upstairs zuwa dakinta ta tattaro hijabs dinta na hadda ta wuce backyard ta saka a washing machine, tana zaune tana chat da Ameera harya gama sannan ta dauraye tayi spinning ta fara shanyawa, tana gamawa taji anyi parking mota, lekawa tayi taga Mummy na shirin fitowa, ta karasa da gudu ta rungumeta tana murmushi ta ce “You’re welcome mother” Mummy ta shafa kanta ta ce “Thank u daughter” handbag dinta Rafi’ah ta kar6a sannan suka wuce ciki.
Haka Rayuwar Rafi’ah ya kasance watarana dadi watarana kunci, babu abinda yake daga mata hankali face idan ta kira Yusuf Jiddah ta dauka, dan dole haka ta dinga avoiding call dinsa ko zata samu sauki, dan kwana biyu ciwanta ya kan tashi but not that serious, hakan yasa tayi concentrating akan karatunta ta watsar da shi itama, duk da shi yana kokarin zuwa ya ganta amma saam bata wani sake masa yanzu, musamman yanzu da take shirin yin Waec dinta, Khairiyya ta kan zo gidan sosai wajen Rafi’ah, ko Yusuf ya kawota ko kuma driver ya suketa, sosai Rafi’ah take ji da yarinyar har cikin ranta. Bangaren Jawad kuma tin da aka saka bikin Rafi’ah ya daina zuwa gidan, kullum wajen aiki yake yini sai dare yake dawowa gida, idan ka ganshi zaka rantse bashi da damuwa, har wani kiba ya danyi ya kara haske, ya watsar da duk wani abu da zaisa ya shiga damuwa, Mami ma idan ya gaisheta da safe ya fice sai tayi bacci yake dawowa. Ba karamin tashin hankali Anty khadija da Ummanta suka shiga ba ganin maganinsu baya tasiri a jikin Yusuf, duk da dama malamin yace a hankali aiki zaiyi amma gashi dai babu changes tsawon wata 8, ita kuwa Jiddah tinda tayi 6ari ta shiga damuwa saboda har yanzu shiru ne babu alamun wani ciki a tattare da ita, suma suna nasu maganin ita da Auntyn sai dai suma babu abinda ya canza, dama da zarar Anty Khadija ta kawo magani Jiddah zata tattara tasa a handbag dinta idan ta fita school ta zubar a titi, haka ta dinga musu tin farkon bikinta har zuwa yau, wani lokaci idan ta tuna auran Yusuf sai ta fashe da kuka, haka zaiyi ta tambayarta amma ta masa banza. Anty Amina ma kullum taje gidansu sai an hado ta da magani, wani lokaci tayi amfani dashi wani lokaci ta ki, dan ita yanzu babbar damuwatarta bai wuce ta hana auren Rafi’ah ba, wannan karan da kanta ta kar6o magani tayi amfani dashi da sunan Rafi’ah ta bunne, bata ta6a shiga tashin hankali kamar ranar da aka kawo lefe ba, ko Jiddah batai haukan da tayi ba, yini tayi tana zarya a parlornta, karshe data kasa hakuri taje ta tono layoyin taga sunan nan inda suke, sake rufe wajen tayi sannan ta koma apartment dinta cike da damuwa, gashi Abba tinda biki ya rage saura sauti 2 ya dawo gida, baya bari ta fita ko ina saboda kullum Ikleemah sai tazo, watarana ta kwana watarana kuma ta tafi. Ranar Saturday Rafi’ah ta gama Neco, tsabar dadi ranar yini tayi tana bacci, washegari kuma Mummy ta taho da mai gyaran jiki aka fara mata, a BQ aka sauki matar saboda safe da yamma ake mata dilka, tin tana marmarinsa harta gaji, ga warinsa daya isheta, ji take kamar tayi amai wani lokaci, ana saura sati daya biki tana kwance a daki taji ana knocking ta danyi shiru sannan ta ce “Waye?” Abdul ya turo kofar ya ce “It’s me, ana jiranki a BQ” tashi tayi tana turo baki ta zura himar dinta sannan ta fito a dakin zuwa downstairs, Ummi kadai ta samu a parlor, ta sunkuyar da kanta ta ce “Bacci nayi shiyasa ban fito ba” Ummi taci gaba da abinda take bata kulata ba, fita tayi ta wuce BQ, ta shiga parlor da sallama, Mummy ce da mai gyaran jikin a zaune suna magana, karasowa tayi ta zauna tana dan yatsine fuska ta ce “Wai yaushe za’a gama ne Mummy?” Anty Halima ta ce “Ranar da aka fara biki mana” kamar zatai kuka ta ce “Dan Allah daga yau a kyaleni banaso nikam, Allah ji nake kamar zanyi amai” harara Mummy ta dalla mata ta ce “Wallahi baki isa daga yau a daina gyaran jiki ba, ina laifin ranar Wednesday, Thursday ki huta friday a fara biki” tagumi Rafi’ah tayi tana kallanta kafin ta ce “Ni gaskiya i’m tired Mummy” Murmushi me gyaran jiki tayi cikin rarrashi ta ce “Kwana hudu fa kawai ya rage Amarya, ki kai hakuri kusan sati 3 ma balle kwana 4” dan turo baki Rafi’ah tayi ta cire hijabin jikinta sannan ta dauka zanin da take daurawa ta wuce daki.
Da daddare Rafi’ah na zaune a parlor tana shan tea Abba ya shigo parlor, ta mike a hankali ta kar6a ledan hannunsa ta ce “Sannu da dawowa Abba” ya ce “Yauwa Mamana, how are u?” Silently ta ce “Fine Abba” daga haka ta wuce kitchen, ajiye ledan hannunta tayi ta ce “Ummi, Abba ya dawo” daga haka tayi saurin ficewa dan ma kar a sata aiki, Ummi ta bita da harara sannan ta wanke hannunta ta fito parlor. Rafi’ah na shiga dakinta taga missed call din Yusuf har 7, kafin ta sake kira wani kiran ya shigo, a hankali tayi picking ta kai kunne, ya ce “Where have u been Baby?” ta ce “Bana kusa ne” ya ce “I’m outside” toh kawai tace sannan tayi hanging call din, babban himar dinta ta saka har kasa, sai kamshi take ga fatar jikinta dake sheki, ko powder babu a fuskarta amma tayi bala’in yin kyau, ta jima a tsaye tana rike da staircase, gashi tana san fita amma kuma su Abba na parlor, ganin call din Yusuf na kara shigowa tayi karfin hali sannan ta sauko ta nufi kofa, Ummi dake yayyanka Apple ta dago tana kallanta ta ce “Ina zakije?” Tsayawa tayi cikin cool voice ta ce “Waje” daga haka ta bude kofar ta fita, as usual yana tsaye jikin motarsa yayi folding hannu, Yusuf ya dan zaro ido ganin yadda ta canza sosai, gaba daya street light din ya haskata, ta sauke kanta tana wasa da fingers dinta ta ce “You’re welcome” ya ce “Thank u wife, kinga yadda ki kai kyau kuwa? anya nima bazanje amin ba” boye fuskarta tayi tana murmushi ta ce “Kai ai namiji ne” ya ce “To ai banaso ki fini kyau” dariya ta danyi ta ce “How are u?” Ya shafa gashin kansa yana kallanta ya ce “I’m fine love, ya jikin ki, ina bakya damuwa sosai” kai ta daga masa sannan ta ce “Ehh” ya ce “That’s good” bude mota yayi ya ciro IV card da yawa cikin bakin leda da kuma key ya mika mata ya ce “Take this, key din na gidan ne” ta kar6a tana murmushi ta ce “Thank u, ai basu tambayi key ba” ya ce “Mummy ta tambaya dazu, ki kai mata” kai kawai ta daga masa, ya ce “To ya kamata ki shiga gida, dare yayi” ya karashe mganar yana kashe mata ido daya, murmushi tayi kawai ta ce “To, saida safe” ya ce “Alright Baby” daga haka ta shige ciki shi kuma ya koma mota yayi reverse sannan ya bar layin. Anty Khadija ce zaune gaban Umma duk sunyi jugum har abin tausayi, Anty Khadija ta mike tana kallan Umma ta ce “Nifa gani nake kamar Jiddah yaudararmu take bata amfani da duk wani magani da muke bata, inba haka ba yau wata kusan 9 labari bai canza ba” Umma ta ta6e baki ta ce “Haka dai kika gani Khadija, idan hakane ta ina zata so a mata kishiya? dole dai tana amfani da magungunan nasara ce babu, gobe kuwa zan koma inji ya ake ciki” Anty Khadija ta sauke ajiyar zuciya sannan ta ce “To Allah ya kaimu” daga haka ta fice a dakin. Karfe 12 na dare Rafi’ah ta tashi ta danna wayarta dake gefenta, missed call din Yusuf ta gani guda 3, ta danyi murmushi ganin text dinsa a saman wayar ya rubuta “I love you” hasken wayar ta kunna sannan ta shiga toilet ta dauro alwala ta fito ta shimfida sallaya ta tada sallah, har kusan karfe 3 kafin ta kwanta anan kasa nan da nan bacci ya dauketa, washegari ya rage saura kwana 4 biki, ‘yan uwan su Ummi sun fara sauka a gidan maza da mata, ba karamin tashin hankali Anty Amina ta shiga ba, dan a cewar malaminta ko taron bikin baza’ai ba, gaba daya ta shiga damuwa har wani rama takeyi gashi ta kasa nutsuwa, kusan kullum sai kaji Abba na mata fada. Da sallama ya shigo dakin hannunsa rike da makullum mota, ya zauna bakin gado yana kallan mahaifiyarsa ya ce “Mami gobe fa zan tafi Cyprus” tashi tayi ta zauna tana kallansa ta ce “Ai na zata ka fasa tafiyan da naji ba kai magana ba” ya dan shafa gashin kansa ya ce “Ehh, da ba yanzu bane, to amma sun kirani ne” Mami ta ce “To Allah ya kaimu, da yushe zaku tashi?” Ya ce “Karfe 10 na dare, idan na kwana a Abuja sai mu wuce” ta ce “To Allah ya kaika lafiya, kana dawowa kayi auranka kaima ka zama mutum, ga masu cuta ma suna aure ballantana lafiyayyu” shiru yayi kansa akan wayarsa yana dannawa, Mami ta ce “Wannan karan bakasan kilishi ne? naji bakai maganar ba” dagowa yayi yana kallanta ya ce “Inaso” daga haka ya mike ya fita sannan ya ja mata kofar. Direct part din Mummy ya shiga da sallama, ya zauna akan kujera yana kallan TV, fitowa tayi tana kallansa ta ce “Jawad kaine?” Ya ce “Ehh” dan raban daya shigo mata harta manta, sai dai idan sun hadu a parlorn Abi su gaisa, Mummy ta dauko masa malt da cup sai ruwa ta ajiye masa a gabansa ta ce “Dan kai yanzu ka zama bako Ahmad, bama ganinka baka ganinmu” murmushi ya danyi yana shafa gashin kansa ya ce “Aiki ne Mummy” ta ce “Haka dai kace, kaikam idan ka zama shugaban kasa sai dai muyi hakuri da kai, kullum aiki aiki baya karewa, ai naga a court dinma ana hutu ko?” Murmushi ya sakeyi ya ce “Zan tafi Cyprus ne gobe” Mummy ta sake baki tana kallanshi ta ce “Cyprus Ahmad?” Ya ce “Insha Allah” ta ce “Amma kasan zan aurar da Rafi’ah ko?” A hankali ya ce “Ehh, amma kiyi hakuri daga court din ne suka nemi a turani, wata biyu zanyi a caan” Mummy ta sauke ajiyar zuciya ta ce “Ai shikkenan, Allah ya taimaka ya kuma bada sa’a, bari na aike ka ka kai musu sako” daga haka ta shiga daki tana fadin “To dambu kake so ko meat pie zan maka sai kana soyawa?” Fitowa tayi da envelop a hannunta ta mika masa ta ce “Dan Allah ka kai musu yanzu Jawad, tin dazu nake kiran Abduljalal yazo ya kar6a baizo ba gashi yamma ta kusa” very gentle ya mike ya dauki malt din yana kallanta ya ce “To saina dawo” ta ce “Ka gaishe su, baka fadi me zan makan ba” ba tare daya kalleta ba ya ce “Dambu nakeso” ta ce “Ba damuwa” daga haka ya fita a parlorn Mummy, Sadeeq kadai ya samu yana cin abinci, ya wuce shi ya fita a parlor ya nufi parking lot, yana kunna motar ya danna horn, gate man ya bude sannan ya fitar da motar bayan ya amsa gaisuwar mai gadin, yana fita yayi parking ya bude envelope din, kananun IV card ne aciki na kamu na Mummy tayi organizing, ya ciro guda daya yana kallo, bayan ya gama karantawa ya maida ciki ya rufe sannan ya tada motar ya bar kofar gidan.
[8/4, 2:59 PM] My Imaan: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation
*_…卮乇賷賰 丨賷丕鬲賷…_*
_{MY LIFE PARTNER}_

*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
_We are here to Educate, Motivate and Entertain our Readers._

_By FATIMA 鉁嶐煆籣

_37_

A bakin gate yayi parking as usual, dashboard ya bude ya dauko chequebook da biro yayi rubutu sannan ya yage paper din yasa a pocket dinsa, wani dan karamin box ya dauko sannan ya dauki envelope din ya fito a motar ya rufe, gently ya karasa bakin gate din ya tura sannan ya shiga, few people ne a tsakar gidan kowa da abinda yake wasu na zaune akan mat, wasu kuma nata backyard ana girki, wasu manyan mata ne akan tabarma suna zaune sai hira suke, kana kallansu kaga dangin su Ummi ne sai kanwar mahaifiyarsu da ita kadai ta rage musu wacce suke kira da Gwaggo, ko ba’a fada ba kamanni sun nuna, tsugunawa Jawad yayi ya ce “Ina yinin ku” a tare duk suka amsa da fara’a ya mike ya shiga cikin gidan, Ummi ce zaune a parlor da wasu mata biyu, ya zauna akan carpet yana murmushi, Ummi ta ce “Is it you Jawad? Dama kana nan?” murmushi yake yana gyara hulan kansa ya ce “Ina nan Ummi, aiki ne ya min yawa yanzu” ta ce “To Allah ya taimaka” ya ce “Ameen, ya hidima?” Ta ce “Alhamdulilah, let me get something for you” daga haka ta mike, gaishe da sauran matan yayi suka amsa masa, ba jimawa Ummi ta fito a kitchen da warmers a hannunta ta wuce parlorn Abba, bayan ta fito ta ce “Ka shigo ciki Ahmad” tashi yayi a hankali ya wuce parlorn Abba ya zauna akan carpet ya fara danna wayarsa. Shigowa Ummi tayi ta zauna ta ce “Kaci abincin ko, bari Rafi’ah ta kawo maka kunu, ko baka sha?” kansa ya dan sauke kasa ya ce “Ina sha, amma dai na koshi da abincin” Ummi ta ce “To bari a kawo maka kunun” daga haka ta fita a parlor. Upstairs ta wuce ta shiga dakin Rafi’ah, a kwance ta sameta tana waya, tayi saurin hanging wayar tana kallan mahaifiyartata, Ummi ta ce “Kije ki dauki kunu ki kaiwa Jawad, yana parlorn Abbanki” a hankali ta mike ta dauki himar dinta ta saka sannan tabi bayan Ummi ta fito, tana saukowa ta wuce kitchen ta dauko flask din sannan ta shiga parlorn Abba, very gentle ta karasa gabansa ta ajiye flask din, suna hada ido tayi saurin dauke kanta ta nemi waje ta zauna gefenshi, a hankali ta ce “Ina yini” ya ce “How are u?” ta ce “I’m fine” ya ce “Ya shirye shirye?” Kanta na kasa ta ce “Alhamdulilah” daga haka ta mike ta fita a parlor ya bita da kallo. Mug ya dauka ya bude flask din sannan ya debi kunun ya saka cube din sugar guda 2 sannan ya dauka spoon ya juya ya fara sha a hankali. Few minutes ya gama sannan ya ajiye cup din, Ummi ne ta shigo parlor daukan abu, ya danyi kasa da kansa ya ce “Ummi zan tafi Cyprus gobe insha Allah” dagowa tayi tana kallansa ta ce “Tooh zaka kara nisa kenan, daga wajen aiki ne suka tura ka?” Ya ce “Ehh” ta ce “To Allah ya tsare hanya, ya dawo da kai lafiya, are u staying long?” Ya ce “Noo, just 2 months” ta ce “Aida yawa Jawad, Allah dai ya taimaka ya tsare” ya ce “Ameen”, daukan abinda zata dauka tayi sannan ta fita a parlor, so yake yace mata yana san yaga Rafi’ah amma ya kasa, gashi he is eager to go home.
After 15 minutes Rafi’ah ta shigo parlor, sai data dan tsaya ganinsa dan a tinaninsa ya wuce, ta sunkuyar da kanta ta wuce dakin dake parlor, ba jimawa ta fito da wani dan bucket a hannunta, Jawad ya ce “Idan kin gama kizo” juyawa tayi ta kalleshi sannan ta fita ta kaiwa Gwaggo bucket din ta dawo, a hankali ta karasa inda yake ta zauna, ya mika mata envelope din ya ce “Mummy ta bayar a baki” ta kar6a sannan ta ce “Thanks” daga haka ya ciro box din da cheque ya mika mata ya ce “And this is for you” ta dago ta kalleshi sannan ta kar6a, kallan cheque din ta dinga yi, ta kara kallansa ganin 100k ajikin cheque din, sauke kanta tayi kasa ta bude box din a hankali, ta dan zaro ido ta ce “Azurfa?” Ya daga mata kai ya ce “I hope it will size you?” Murmushi tayi ta fara zira ring din a hannunta na dama, ta juyo hannun tana kallansa ta ce “Yayi kyau sosai, thank u so much” kallan dogayen fingers dinta kawai yake, ta cire ring din ta maida shi box dinsa sannan ta ce “I’m so much greatful, nagode sosai Allah ya saka da alkhairi” a hankali ya dago yana kallanta ya ce “I know u have more than that, so no need to say thanks, and i’m wishing u a happy marriage life, try your best and be the best wife ever” a hankali ta ce “Insha Allah” still looking at her ya ce “Gobe zan tafi Cyprus bazan samu daurin auran ki ba” duk jikinta sanyi yayi ta ce “Allah ya kiyaye, ya kaika lafiya” ya ce “Ameen” daga haka ya mike ya dauki key din motarsa, tashi tayi tabi bayansa har suka fito a gidan, ta rakashi har mota tana mishi Allah ya kiyaye, silently ta tsaya a bakin mota ta ce “I’m lost of words Ya Jawad, nagode sosai da sosai, Allah ya saka, i’m happy with the gift” murmushi ya danyi ya ce “Ba komai, thanks too” rife motar tayi sannan ta shiga gida shi kuma ya tada motar ya bar layin. Tana shiga compound Gwaggo ta ce “Shine angon ne Fatima?” Turo baki tayi tana kallan kakartata ta ce “Ba shine bane fa Gwaggo” Gwaggo ta ce “To shi wannan din waye? angon baizo ya gaishe niba fa, baisan kanwar kakarki tazo bane” dariya ta danyi ta ce “Keda zamu tafi tare, ai an maki dakinki” daga haka ta wuce ciki ta barta a tsaye.
Washegari da sassafe Jawad ya gama shirinsa na tafiya Abuja, daga caan karfe 10 na dare zasu tashi zuwa Cyprus Mami na tsaye ta gama hada masa komai ta ce “Yanzu sai kaje Abujan zaka karasa kenan?” Ya ce “Ehh” ta ce “To saura karkaje ka gaishe da mutanen gida, nasanka yanzu zaka ce aiki ya maka yawa” murmushi ya danyi ya ce “Ai a caan zan sauka tinda yau zan wuce” ta ce “To Allah ya kiyaye, ya kuma tsare hanya” ya ce “Ameen”, Sadeeq ne ya fitar mishi da komai zuwa mota, bayan sun fito parlor Mummy ta fito da dambun namanta cikin dan karamin bucket ta ce “Allah ya tsare Ahmad, ga dambun naman” kar6a yayi ya ce “Nagode Mummy” ta ce “To Allah ya tsare” daga haka ta koma part dinta Mami ta bita da harara, shi dai sauke kansa yayi kasa ya fice a parlor, Mami tabi bayansa ta ce “Dambun naman ne bazan iya maka ba sai ka fadawa duniya an maka” dan murmushi yayi ya ce “It’s nothing ai Mami, duk daya ne” harara ta 6alla masa ta ce “Allah ya tsare” daga haka ta koma cikin gida ba tare data ga tafiyarsa ba. Da Yamma liss aka fara shirin waleeman da Mummy ta hada, ita ce komai akan gaba, karfe 4 mai make~up tazo ta fara yiwa amarya, Ameera na gefe ta gama make~up dinta tana daura dankwali, bude kofar akayi Mummy ta shigo ta ce “Wai har yanzu baku gama ba?” mai kwalliyan ta danyi murmushi ta ce “An gama Hajiya” Mummy ta kalli Rafi’ah dake kyalli ta ce “Masha Allah” daga haka ta fita a dakin, by 4:30 sun gama komai da komai, a compound din cikin gidan aka jera kujeru akai decorating wajen, Babbar malama aka dauko ta wa’azantar da mutune akan rayuwar zaman aure, da yawa mutane sun karu ba kadan ba, bayan ta gama aka fara cin abinci sannan aka raba snacks, daga karshe akai hotuna kowa ya watse. Da dare musalin karfe 10 Rafi’ah na zaune a dakinta ita da Ameera da wasu friends dinsu na islamiyya su biyu, Mummy ta shigo ta ajiye musu warmer din abinci ta ce “Rafi’ah Gwaggo tace bata ganki ba tin bayan waleema” limshe idanuwanta tayi ta ce “Ina daki, bayan dazu data ganni da make~up tace min abu kamar aljana” dariya Ameera ta dinga yi tana kallan Rafi’ah, Mummy ta ce “Ai kadan da aikin Gwaggo, Yusuf din ya aiko kayan da zaki sa goben?” Rafi’ah ta ce “Yace zai kawo da safe” Mummy ta ce “Ok to shkn, zaizo ne ayi kamun dashi” Rafi’ah ta dan turo baki ta ce “Yace dai zaizo muyi pictures” Mummy ta ce “To ba damuwa na zata ai bazai zo ba ne danaji baki maganar ba” daga haka ta fita, Rafi’ah ta kalli Ameera ta ce “Ai sai yazo wajen kamun nan, ai da bikin matarsa shima yaje” Ameera ta dan yi murmushi ta ce “Kishi” duka Rafi’ah ta kai mata ta kauce tana dariya. Washegari ya kama friday, gidan biki ya cika da jama’a kowa nata hidima, Rafi’ah dai tattara nata nata tayi ta koma gidansu Ameera saboda mutane. Bangaren su Umma kuwa, mutane kadan ne a gidan, dan batayi wani gayya ba, gaba daya abin duniya ya isheta, sau biyu Jiddah na zuwa mata tana kuka, haka dai Umma ke lalla6ata ta koma gida. Gidan Ammin Khairiyya kuwa acaan duk ‘yan uwa suka sauka, gidan ya cika da mutane kai kace a gidan Yusuf ya girma. Anty Amina ce zaune a dakinta tare da Anty Rahama, ta dan yatsune fuska tana kallan Anty Rahama ta ce “To ya zanyi Maman Ikleemah, kina gani dai abun nan yana nan ba’a tone ba” Anty Rahama ta ta6e baki ta ce “To sai asan abinyi a gaba ai, ba wai zuba ido zamuyi ba, su kuma ‘yan uwanmu da basu iya zuwa birni ba duk sun cika gida, gidan Umman ma acike yake, kema naki acike, nifa idan na gaji kaaf mutanen parlorn nan saina koresu wallahi” Anty Amina ta gyara zamanta ta ce “Ga kazanta kamar ta fito fili, shima Yayah Muhammad din a hotel yace zai kwana yau” Anty Rahama ta gwalalo ido ta ce “Anya mun ta6a bikin da akai taro irin wannan kaf zuri’ar mu kuwa? Har Abban sunma ya rasa wajen kwana a gidansa sai hotel?” Anty Amina ta ce “To shine abinda yake damuna, gashi shi Mutumin Umma cewa yayi ko taro baza’ai ba gashi har gobe daurin aure” Anty Rahama ta ce “Mudai zuba ido, ba kince yana nan ba a binne?” Kai ta daga mat, Anty Rahama ta mike ta fita tana kallan mutanen parlorn da duk yawanci ‘yan uwansu ne ta ce “Kuma wallahi duk matar data ci abinci ta share, haka kawai kun cikawa kanwata parlor da ‘ya’ya ‘yan kauye” wata ‘yar uwarsu ce ta mike tana kallansu ta ce “Ke Rahama ki kiye bakinki, gidankine da zaki finga yiwa mutane iyayi kina fada musu magana” Anty Rahama ta ce “Amma ai gidan kanwatane kuma gidan Yayana” matar ta mike tana tafa hannu ta ce “Indan ta wannan ne muma ai dan uwanmu ne, saboda haka duk inda muka ga daman zama a gidan nan zama zamuyi” wata mata ce ta tashi tana kallanta ta ce “Dan Allah Safiya kiyi hakuri kibar kulata, ita har tanada bakin magana, shekararta nawa a gida babu aure, ga zandareriyar budurwar ‘yarta banda rashin kunya bata iya komai ba” Cakumeta Anty Rahama tayi ta ce”Har ni zaki cewa bazawara, yanzu sai naci kaza-kazanki a gidan nan wallahi” mutanen dake zaune a parlor suna ta bada hakuri, da kyar dai Anty Rahama ta saketa ta shige daki tana zage-zage.

_08103810398_
[8/5, 7:38 AM] Zarah: *_…卮乇賷賰 丨賷丕鬲賷…_*
_{MY LIFE PARTNER}_

*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
_We are here to Educate, Motivate and Entertain our Readers._

_By FATIMA 鉁嶐煆籣

_38_

Zaune take akan sallaya tana addu’a misalin karfe 10 na safe, juyawa tayi jin ringing din wayarta, ta dago wayar tana murmushi ganin Yusuf ne, a hankali tayi picking call din ta kai kunne hade da sallama, on the orther hand Yusuf ya ce “How are u Baby?” A hankali ta ce “I’m fine” ya ce “I saw ur make~up yesterday, kinyi kyau sosai, i hope yau kifi jiya kyau” a hankali ta danyi murmushi ta ce “Insha Allah” ya ce “Zanzo na kawo miki kayanki anjima” ta gyara zamanta ta ce “I’m not at home” da mamaki ya ce “Kina ina?” ta ce “Gidansu friend dina Ameera, bayan layin mu ne” ajiyar zuciya ya sauke har sai data jiyoshi, ya danyi shiru sai kuma ya ce “Caan gidansu zanzo kenan?” Ta ce “Ehh, ina ga” ya ce “Alright, u send me the address, take care” ta ce “Ohk bye” hanging call din tayi taci gaba da addu’a, bayan ta gama ta mike akan carpet ta dan limshe ido dan bacci takeji bana wasa ba, daren jiya batai baccin kirki ba tai ta sallah tana addu’a hopping for the best marriage in her life. Jiddah ce zaune a parlornta tana share hawaye, tinda taji Yusuf yana waya kuka ya dinga cinta, bata samu sauki ba saida tayi kukan, tana nan zaune ya fito daga daki, ta gefen ido ta dan kalleshi, sai da kirjinta ya buga ganin kyan da yayi, sai sheki yake kamar shima am masa dilka lol, ya sha farar shadda da babbar riga sai ya fito as the groom he is, banda kamshi babu abinda yake, bude warmers din kan dinning yayi yaga babu komai, ya juyo ya kalleta tayi saurin dauke kanta, yana murmushi ya karasa gefenta ya bata side hug ya ce “Why the mood first wife?” fashewa tayi da kuka ta ce “Aure zakiyi ka kyaleni ko Yaya?, dan Allah ka fasa auran nan Allah zan iya mutuwa” limshe idanuwansa yayi jin yadda tayi collapsing a jikinshi, ya dinga shafa bayanta cikin rarrashi ya ce “I told u everything yesterday night Jiddah, alkawari nayi zan zauna daku biyun har karshen rayuwana, all i want is peace, ba aure zanyi dan hankalina ya tashi ba, and ba wai zanyi aure bane saboda bana sanki ba, ina sanki babu abinda kika gaza yimin a zamana dake, duk da ma satin nan kaff da yunwa kike barina amma dai na yafe miki” kara fashewa da kuka tayi ta ce “Bayan yarinyar rainin yawo ne da ita, gata karama amma sai rashin kunya, wallahi idan ta shigo gidana she will regret” ta karashe maganar tana share hawaye, rungumeta yayi tsam tsam cikin lallami ya ce “Amma ai tin farko na riga na gaya miki tare zaku zauna, sannan jiya da aka zo jere u did wrong, kin 6atamin rai kawai banyi magana bane saboda banasan hayaniya, ya za’ai ki rife kofar parlor bayan kinsan ta nan zasu shigo?” Rife idanuwanta tayi ta ce “To meyasa baka mata nata kofan ba?” Strictly ya ce “That’s my wish, ba gidana bane? don’t make me angry now, kuma yau kam kije gida, da daddare idan an kawo amarya u can come back, idan kinga dama ki kwana in kina so” kara fashewa tayi da kuka ta ce “Ni bazanyi attending auranka ba wallahi, bazanje gidan ba, sai dai na tafi gidan Anty na” zameta yayi a jikinsa ya ce “I don’t permit u, idan baza kije gidanmu ba u can stay at home” daga haka ya dauki key din mota da kayan Rafi’ah a leda ya fita a parlorn, yana fita ta rushe da kuka ta durkusa akan carpet tana ta shiga 3. Umma ce zaune a gaban Malaminta sai zufa take, ya juyo kwaryar dake cike da ruwa yana nuna mata ya ce “Da karfe nawa ne auran?” Cikin rawar jiki ta ce “Yau Juma’a da karfe 2 idan an idar da sallah” girgiza kansa yayi yana kurawa ruwan ido ya ce “Ba lallai a daura auran ba” Umma ta share zufa tana kallansa ta ce “Alhamdulilah” da sauri ya dago ya kalleta ta ce “Allah gafarta Malam” ya juya jajayen idanuwansa ya ce “Mutanenmu na bukatar wata gudumawar Hajiya, saboda aiki sabo zasu yi” cikin sauri Umma ta ciro dubu 50 ta ajiye masa a gabansa ta ce “Indai aiki zaiyi ko nawa ne zan bayar Allah gafarta Malam” yayi wata kalar dariya ya ce “An gama Hajiya, sai dai ki zuba ido” mikewa Umma tayi tana murmushi ta ce “A huta gajiya” daga haka ta debi takalmanta a hannu ta fita a dakin.
Anty Amina ce zaune a dakinta ta buga uban tagumi, duk jikinta yayi sanyi ganin awanni ya rage a daura aure , gashi so take ta tono abin tagani yana nan din amma gidan cike yake da jama’a ta ko’ina, duk ta rasa inda zata sa ranta gashi Anty Rahama ta koma gidan kawarta wai sai an fasa auran zata dawo tayi dariya, bude kofar dakin d akai yasa ta dago kanta, Ikleemah ta karaso dakin da kumburarrun idanuwanta da sukai jaa, zama tayi a gefen gado tana kallan Anty Amina ta ce “Saura awa 3 fa Anty, kunce min dani za’a daura amma har yanzu banji ana ango yace bayayi ba” fashewa tayi da kuka tana kallan Anty Amina. Ajiyar zuciya ta sauke ta kamo hannayenta ta ce “Kiyi hakuri mu zuba ido mu gani, ai yadda kika sha dilka da gyaran jiki dole ke zaki shiga gidan Yusuf, kima daina daga hankalinki muna nan zakiji komai anjima” cikin kuka ta ce “Fatana kenan Anty, dan idan na rasa Yusuf mutuwa zanyi Anty Amina, sai dai Ammina ta dauki gawana ko ku… ” rife bakinta Anty Amina tayi ta ce “Kina hauka ne Ikleemah, menene na zancen daukan gawa kuma” share hawayenta tayi ta jingina kanta akan gado tana kuka kasa~kasa.
Simple make~up Rafi’ah tayi ta saka atampa Ameera tayi mata daurin, sosai tayi kyau, sai kamshi take duk inda ta gifta, Ameera dake kallanta ta ce “Anya Doctor zai bari ki dawo gida Fatima? Masha Allah kin yi kyau” ‘yar harara ta 6alla mata ta ce “Ina dai Babanku baya kasa?” Ameera dake dariya ta ce “Jiya fa nace miki yayi tafiya, amma anjima zai dawo, dan yace min zai iya samun daurin auranki” ta dauka veil dinta ta yafa ta ce “Ameera kaina ciwo yake” dafa goshinta tayi ta ce “To bakya bacci Fatima, taya baza kiyi ciwan kai ba” a hankali ta dan limshe ido ta ce “To ya zanyi Ameera, dole ne nayi addu’a sosai na roki Allah yasa a gama bikin nan lafiya, gaba daya na gaji so nake a gama kowa ya huta” Ameera ta danyi murmushi ta ce “Dama haka hidima yake ai, insha Allah lafiya kowa zai koma gida” a hankali ta ce “Ameen” tana rife bakinta phone dinta ya hau ringing, ta bude idanuwanta dake limshe tayi picking call din, Yusuf ya ce “I’m outside” ta ce “To” daga haka tayi hanging wayar tana kallan Ameera dake gaban mirror ta ce “Bari naje Khadija, su Maryam Sa’eed basu zo ba har yanzu” Ameera ta juyo tana kallanta ta ce “Soon zasu zo, dazu da kina bacci munyi waya, wai tailor ne bai karasa musu dinkin ankon ba” Rafi’ah ta ce “Alright, sai na dawo” Ameera ta ce “Ki gaishe sa” da toh ta amsa sannan ta fita a dakin, kannan Ameera ne kawai a parlor suna kallan power rangers samurai, ta danyi murmushi ganin yadda suke gaisheta ta ce “How are u people?” Suka ce “Fine” daga haka ta fita, tsaye suke shida Aliyu a jikin motarsa, ya dinga kallanta harta karaso inda suke, ta dan kalli Aliyu ta ce “Ina yini?” Ya ce “Lafiya kalau Amaryar mu, ya hidima?” Ta ce “Alhamdulilah” Yusuf ya gyara zaman hularsa yana murmushi ya ce “Ina yini Baby” rife idanuwanta tayi da veil dinta, ya ce “Kinyi kyau Allah, i feel like stealing you and run” harara Aliyu ya 6alla masa ya ce “Doctor ka daukeni karshen layin nan idan ka gama, zan shiga wajen Mukhtar” Yusuf ya ce “Ba damuwa” daga haka Aliyu ya kalli Rafi’ah ya ce “Amaryarmu sai anjima ko” ta ce “To nagode”. Bude back seat Yusuf yayi ya ce “Pls enter Baby” ta sauke kanta kasa sannan ta shiga motar, zagayawa yayi shima ya shiga back seat yana kallanta ya rife kofar, ya jawo ledan kayanta ya ce “Ya miki kyau?” Ya zaro rigar yana warewa a hankali, ta dinga kallan hadaddiyar gown din ta ce “Yayi kyau sosai, thank u” ya ce “Mention not, meyake damunki?” tayi saurin sauke kanta kasa ta ce “Me kaga?” Maida rigar yayi cikin ledarta ya ce “Your eyes, bakya bacci ko?” Ta girgiza masa kai a hankali, kamo hannunta yayi murya caan kasa ya ce “Pls tell me dear” silently ta ce “I’m just having headache” Yusuf ya dinga kallanta with lots of disturb ya ce “Have u take any medicine?” Ta girgiza masa kai kanta na kasa, limshe ido yayi yana matsa hannunsa cikin nata jiin zafin jikinta, iya hannunta daya rike kawai yaji jikinta da zafi, dago kanta yayi yaga idanta tap da hawaye, ya kai hannunsa face dinta zai tare tayi saurin janye fuskarta ta ce “I’m not crying” ya ce “You are” ta ce “Kawai ina tinanin Ummina ne idan na tafi” jinginar da kansa yayi ajikin kujera yana kallanta, ji yayi kamar ya jawota jikinshi ya rarrasheta, ya sake hannunta ya ce “Are u taking ur drugs?” Ta ce “Ehh, dazu ma nasha” ya ce “Abinci fa?” Ta ce “Naci” ya ce “Allah ya kara miki lafiya, but don’t stress yourself pls, u know ur condition more than anyone else, nasan dole zakiyi kewar Ummi but do a little Baby, kar ki bari ki samu attack today pls” tana ta jujjuya yatsunta ta ce “To” ya danyi murmushi yana kallan Henna hannunta ya ce “It’s looks beautiful” ita dai bata bari sun sake hada ido ba, ya ce “Waya maki?” Ta ce “Wata ce” ya ce “Ohk, anjima da dare zan gani sosai da sosai” turo baki tayi ta kara sauke kanta, ya ce “Take ur clothe, Allah ya sauwake, but make sure kinsha panadol sai ki kwanta kinga yanzu is 12 idan an daura auran i will call u” boye fuskarta tayi a jikin kujera tana murmushi ya ce “Yess i will be the first to tell u insha Allah” bude kofar tayi ta fito, ta dan saci kallansa ta ce “Thank u” ya fito shima yana kallanta ya ce “Allah ya sauwake” daga haka ta daga masa hannu ta koma cikin gida.
Mami ce ta shigo gidan da Ikraam a bayanta, suka dinga wuce mutane a tsakar gida suka shigo ciki, Gwaggo ta kalli daya daga cikin ‘ya’yanta ta ce “Waccen ba kishiyar Halima bace?” Anty Salma dake kallan Mami ta ce “Itane mana Gwaggo” Gwaggo ta ce “Shine ta wuce ba gaisuwa, aiko bata sanni ba tana ganina taga jinin su Halima” ita dai Anty Salma shiru tayi taci gaba da danna wayarta, Ummi na shirin fitowa a parlor suka ci karo da Mami, ta danyi murmushi ta ce “Sannu da zuwa Hajiya” ba yabo ba fallasa Mami ta ce “Sannu” Ummi ta juya ta ce “Ku shigo ciki” daga haka ta wuce dasu dakinta dake sama inda Anty Halima da kayenta suke, sosai Mummy tayi mamakin ganinta, dan tanaji da safe Abi na mata fada jiya bata zo gidan biki ba, Mummy ta ce “Sannunku da zuwa” Mami ta gaisa da kawayenta, ta ce “Ina Amaryar?” Ummi dake jera musu abinci agabansu ta ce “Tana nan neighbors dinmu” Mami ta ce “To ya hidima?” Ta ce “Mun gode Allah” kallan Ukraam Mummy tayi ta ce “Ke bakya gaisuwa ne?” Mami ta dan hade rai sai kuma ta ce “Haka take ai” Ikraam ta gaishe da mutanen dakin sannan ta koma bayan uwarta ta lafe, bayan minti 10 Mami ta mike tana kallan Ummi da shigowanta dakin kenan ta ce “To ni zan wuce ga wannan ba yawa” ta nunawa Ummi food flask da bedsheet din da suka kawo, Ummi ta ce “Allah ya saka da alkhairi, mun gode, Jawad ma bana kusa ban mishi gidiya ba ya wuce, Allah yasa ya tafi a sa’a kuma” ciki ciki Mami ta ce “Ameen” daga haka ta dan kalli Mummy ta ce “Sai kin dawo” bata jira cewarta ba ta kama hannun Ikraam suka fita a dakin, gaba daya mood dinta ya canza, leda Ummi ta samu ta juye musu snacks din da basu ciba, Abdul da shigowansa kenan ta ce “Kaima Mamansu Jawad kafin su tafi, kace mun gode” cikinsa ya fara shafawa yana kallanta ya ce “Yunwa nakeji Ummi” ta dalla masa harara ta ce “Ba aiken ka nayi ba, nima babu abinda naci tin ruwan lipton dana sha da safe” juyawa yayi ya fita a dakin, da sauri ya fita gate ya samu tana shirin ta tada mota, mika mata ledar yayi ya ce “Ina yini” taja motarta ta bar kofar gidan, kallan hannunsa ya dingayi yaga ba abinda ya sameshi dan dama da sauri ya janye, ya koma cikin gida ya zauna kusa da Gwaggo dake balcony akan tabarma ya fara cin snacks din. Karfe 1 aka dinga tafiya babban masallacin juma’a dake unguwar dan anan za’a daura auran. Rafi’ah na daki taci kwalliya sosai suna ta hotuna kiran Ummi ya shigo mata, tayi picking call din ta fito a dakin saboda hayaniyar friends dinsu, a hankali ta ce “Ina yini Ummi” ta ce “Lafiya, kinci abinci ne?” Ta ce “Ehh, naci” Ummi ta ce “Kina addu’a dai ko Rafi’ah?” A hankali ta ce “Inayi” Ummi ta ce “Never get tired of praying daughter, ko me kike ki dinga addu’a, make sure kina kiran Allah a duk kan lamarinki” silently ta ce “Insha Allah Ummi” Ummi ta ce “Good, Ga Mummynki” kar6ar wayar Anty Halima tayi ta ce “Kina jina Rafi’ah?” Ta ce “Eh” Mummy ta ce “Ku shirya ayi kamun nan da wuri a kaiki kafin dare yayi sosai, kowa saiya dawo gida cikin nutsuwa, karfe 4 kuna wajen nan dan Allah” ta ce “To zamu shirya” Mummy ta ce “Allah ya tsare yasa a gama komai lafiya” a hankali ta ce “Ameen” sannan tayi hanging call din ta koma daki, gefe ta zauna tayi shiru tana kallan time, karfe 2 harda minti 15, ta kifa kanta akan gwaiwoyinta tana karanto ayatul qursiyyu, Maryam ta juyo tana kallanta ta ce “What’s wrong Fatima?” Sai a lokacin duk hankalinsu ya kai wajen, suka koma gefenta suna tambayarta menene, Ameera ta ce “Ko ciwan kanne?” girgiza musu kai tayi ta ce “Ba komai” daga haka ta fashe da kuka, Ameera da gaba daya ta rikice ta ce “Wai menene Fatima?” Cikin kuka Rafi’ah ta ce “Abbana, i will miss him” Ameera taja dan karamin tsaki tana murmushi, ita a tinaninta ma wani abin ne ya faru, daga haka ta rungumeta tana kallan agogon dakin ta ce “Kinga time kenan? Ai hamdala ya kamata ki farayi not crying Teemah” Rafi’ah ta share idanta ta ce “Na fada ai” su Maryam dake kallansu suka kwashe da dariya, harara ta musu ta turo baki tana juya kai gefe, wayarta ne ya fara vibrating tayi saurin kallan screen din, daga call din tayi kirjinta na bugawa da sauri~da sauri, Yusuf ya danyi murmushi ya ce “You are now my wife” limshe idanuwanta tayi tana murmushi. Karfe 2 da rabi ‘yan daurin aure suka fara dawowa, Anty Amina ta fito tsakar gida ko zata ji wani labari amma taga kowa hidimar gabansa yake, Ikleemah na biye da ita har suka karaso wajen apartment din Ummi, juyawa tayi sai ga Abba ya shigo gidan, tayi karfin hali ta kakalo murmushi ta ce “Abban Rafi’ah har kun dawo?” Ya ce “Ehh an daura aure, ki samo min abincin mutum 10 akai guest house dina” da ido kawai ta bishi yana magana, juyawan da zatai taji faduwar Ikleemah a kasa, Abba da har ya fara tafiya ya juyo da sauri yayi kansu, Anty Amina ta saki kara tana jijjigata ta ce “Na shiga uku Ikleemah dan Allah ki tashi” dai dai nan Anty Rahama ta shigo, tayi kansu da gudu tana ta shiga uku, daga Ikleemah Abba yayi ya nufi bakin gate da ita Anty Amina tabi bayansu tana kuka.

*I dedicated this page to the members of my groups, i love u all and thanks for d comments i appreciate sisters 馃グ*
_08103810398_
[8/7, 2:53 PM] Zarah: *_…卮乇賷賰 丨賷丕鬲賷…_*
_{MY LIFE PARTNER}_

*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
_We are here to Educate, Motivate and Entertain our Readers._

_By FATIMA 鉁嶐煆籣

_39_

Anty Rahama na tsaye rike da hannun Ikleemah a ward din da akai admitting dinsu, lokaci~lokaci ta kan jijjiga hannunta tana kiran sunanta ko zata tashi, Anty Amina dake tsaye bakin kofa tana kallansu ta ce “Anty Rahama ki bar jijjigata tunda sunce very soon zata tashi” dago kanta tayi tana kallan Anty Amina kafin ta fara magana kamar haka “Na rantse da Allah, na rantse da wanda ya halicci uwata da ubana Rafi’ah bazata zauna a gidan Yusuf ba, sai tayi nadamar auransa a rayuwarta, sai ta dandana bakin ciki kamar yadda tasa Ikleemah” a hankali Anty Amina ta karaso inda suke ta dafata ta ce “Kamar anyi an gama, amma yanzu hankalinmu ya dawo wajen Ikleemah kafin komai” tana rife bakinta wani Doctor ya bude kofar dakin Abba na biye dashi a baya, Abba ya karasa kan gadon yana kallan Ikleemah dake kwance kamar gawa ya ce “Allah ya baki lafiya” Anty Rahama ta ce “Ameen” Doctor na gyara mata drip din hannunta ya ce “Soon zata tashi, so karku daga hankalinku ba wani damuwa” Abba ya ce “Fatanmu kenan, amma menene yake damunta Dr” kallan Abba yayi kafin ya ce “We can talk in my office yallaboi” Abba yabi bayansa suka fita zuwa office dinsa, bayan sun zauna Doctor ya kalleshi ya ce “How are u related with her? Naga kamar kaine mahaifinta” Abba ya ce “Yess i’m a dad to her but not biological father” Doctor ya ce “Do u have any heridity of Heart Attack either family dinku kona mahaifiyarta” Abba ya ce “Yess we have” Doctor ya ce “Allah ya karawa masu shi lafiya, i’m sorry to say itama ta kamu dashi” Abba ya danyi jiim kafin ya ce “What the next thing now” Doctor ya ce “Eh insha Allah zata tashi anjima, zamu daurata akan magani, amma ina ga ba lallaima ta kwana ba” Abba ya mika masa hannu ya ce “Mungode sosai” Doctor ya ce “Allah ya bata lafiya yallaboi” daga haka Abba ya fita a dakin ya wuce masallacin dake asibitin, bayan an idar da sallan la’asar ya dawo ward din da suke, a zaune duk ya samesu sunyi jugum Abba ya kalli Anty Rahama ya ce “Ko zaki kira mahifinta ki sanar masa” ta hade fuska ta ce “Sai dai idan an sallamemu kuma, mutumun da ko nemanmu baya yi” Abba ya ce “Koma menene u let him know, uba ai uba ne, kuma rabuwa ba hauka bane, dole ne yasan abinda yake damin ‘yarsa” Anty Rahama da idanta ya kawo ruwa ta ce “Menene yake damunta Ya Muhammad? Dan Allah ka fadamin ina ba mutuwa zatai ba” Abba dake kallanta ya ce “Ba kuka zakiyi ba, kiyita mata addu’a kawai” Anty Rahama ta goge idanta ta ce “Menene yake damun Ikleemah Yaya” Abba ya ce “Itama ta kamu da ciwan zuciya, yace zai sata akan magani idan ta tashi, so dont worry about Allah ya basu lafiya baki daya, zanje na sallami bakina da suka zo daurin aure” daga haka ya fita a dakin Anty Rahama ta bishi da kallo, yana fita ta rushe da kuka tana jijjiga Ikleemah ta ce “Na shiga uku na, Ikleemah ciwan zuciya? Nida nakewa wasu dariya yau gashi a jikin ‘yata na shiga uku Umma ya zanyi inasan ‘yata wallahi” Anty Amina dake kuka itama ta ce “Mun shiga uku, dan Allah suce ba gaskiya bane”. Haka suka dinga rusa kuka har saida Doctor ya shigo ya musu magana sannan suka sassauta kukansu. Parking Abba yayi a kofar gida ya fito sannan ya shiga ciki, wayar Ummi ya kira yace ta sameshi a parlorn shi, ba jimawa ta shigo cikin shigarta ta alfarma, kana kallanta kaga uwar amarya sai kamshi take da gold dinta a wuya da kunne, zama tayi a gefen Abba ta ce “Ya jikin Ikleeman?” Ya ce “Da sauki, wai ciwan zuciya ne itama” Ummi ta dan zaro ido ta ce “Subhanallah, Allah ya bata lafiya, anyi discharging dinta ne?” Abba ya ce “Noo, sunce dai may b anjima, an kai abincin da nace akai guest house?” Ta ce “Ehh, an kai dazu” Abba ya mike ya ce “Bari naje na sallami baki, sannan ku hakura da wannan event din da zakuyi” Ummi ta ce “Nifa bani zanyi ba, Anty Halima ce ta hada musu” Abba ya ce “To kice mata a barshi kawai, akwai marar lafiya a gida” ta ce “To Allah ya sauwake” daga haka ya fita a parlorn.
Da kyar Ummi ta shawo kan Anty Halima aka fasa kamun nan, dan cewa tayi ita ba ruwanta da ciwansu sai anyi kamu, wai idan sune da yanzu suna abinda yafi haka. Duk da haka sai da Mummy ta kira mai hoto sukai ta hotuna a compound din gidan bayan anyi decorating dinsa, sosai Rafi’ah tayi kyau kamar ka saceta ka gudu, ganin Yusuf da friends dinsa sunzo yasa Ummi ta koma cikin gida, Mummy kuwa hotunansu suka sha da Yusuf har kusan Magrib sannan suka tafi, daga haka kowa ya watse, Aliyu ne ya dauki su Rafi’ah ya maidasu gidansu Ameera.
Umma ce zaune a gefen Ikleemah tana bata tea a baki, Anty Rahama da idanuwanta suka kumbura tsabar kuka tana gefe a zaune kamar marainiya, bayan Ikleemah ta koshi Umma ta kalli Anty Amina ta ce “Yanzu dai rashin lafiyar Ikleemah shine gaba da komai, idan ta samu sauki na tabbata komai zai tafi dai dai rannan zasu gane banbancin aya da tsakuwa” su dai suna zaune ba wanda yace kala a acikinsu, kowa da abinda yake sakawa cikin ransa musamman Anty Rahama gani take kamar su Ummi dariya zasu mata.
Da damuwa Anty Khadija ta shigo dakin da Ummanta take, bayan ta zauna ta ce “Umma mahaifiyarta tana da kishiya, sai dai kuma tafi zama a Abuja akan a nan, inaga kafin su koma zuwa gobe ni zanje” Umma ta ce “Hakan za’ai, shima Malam da mukai waya cewa yayi baisan me faru ba aikin yaki yi, yana da tabbacin aurin ba zai dade ba” Anty Khadija tayi wani murmushi ta ce “Ai dama bai cancanta ya dade ba, ai Yusuf Umma bazai ta6a samun kwanciyar hankali ba” Umma ta mike ta fita a dakin sakamakon kiran Malam daya shigo wayarta.
Karfe 9 bayan sallan isha su Mummy suka shirya Rafi’ah tsaf, tinda aka fara shiryata take hawaye, bayan an gama Mummy ta kama hannunta zuwa dakin da Ummi take, Mummy ta damka hannunta cikin na Ummi ta ce “And pls don’t cry daughter” daga haka ta fita a dakin, silently Ummi ta kira sunanta, ta dago idanta da suka cika da hawaye ta ce “Ki yafemin Ummi na” rungumeta Ummi tayi trying hard not to cry ta ce “Allah ya miki albarka daughter, Allah yasa auranki ya zama abin kwatance, i will miss u daughter” Rafi’ah ta fashe da kuka ta kankame Umminta, bude kofar dakin akayi Abba ya shigo, ya zauna gefensu ya fara magana cikin rarrashi, sosai ya lalla6a Rafi’ah hade da mata addu’an samun sa’ar aure, bayan nan shida Ummi suka mata nasiha sosai da sosai, a karshe suka mata addu’ah, duk sai jikinta yayi mungun sanyi, ta rungume Abba tana kuka, da kyar ya raba ta da jikinsa ya fita a dakin, Ummi ta kama hannunta suka fito, Mummy ce ta lullu6a mata alkyabbar jikinta suka sauko downstairs har lokacin kuka take da haka suka wuce da ita.
Minti 14 ya kaisu gidan Yusuf, aka shiga da Rafi’ah har dakinta, zuwa karfe 10 kowa ya watse sai Mummy, Gwaggo da Anty Salma, sosai da sosai suka kara mata nasiha, da zasu tafi gwaggo harda kukanta, Rafi’ah na kuka haka suka tafi suka barta, koda suka fito Jiddah na zaune aparlor taci uban kwalliya tana kallo, ko kallansu batai ba bare susa a rai zata gaishe su, Gwaggo sai mita take har suka fita, Mummy ce ta jasu zuwa gidanta dan a caan zasu kwana. Karfe 11 Yusuf ya shigo gidan, ajiye dayan take away yayi ya shiga da daya, a kwance ya samu Jiddah tayi rub da ciki, ya hau kan gadon ya dagota ya ce “How are u?” Ta fashe da kuka ta kankameshi, a hankali ya ce “Ga abinci na kawo maki, amma ai kinmin alkawari u won’t cry ko?” hawayenta ta share ta koma gefe ta zauna, Yusuf ya kara matsawa inda take ya ce “Take ur food, and stop crying” kai kawai ta gyada masa, ya ajiye mata take away din akan bed side drawer ya ce “Good night” da ido ta bishi harya fita ya rufo mata kofar, ta fashe da kuka tayi wurgi da take away din. A kan dinning ya dauki ledan daya ajiye ya shiga part din Rafi’ah, tana zaune a parlor tana kallon wani series, tayi saurin dago kanta tana kallanshi, bude hannayensa yayi ta taso da sauri tayi hugging dinsa, ya rungumeta shima yana shafa bayanta ya ce “This was my dream always” Rafi’ah ta sake shi tana kallansa tayi murmushi, ya bata side hug yana kissing forehead dinta ya ce “I luv u” ta ce “I luv u more” hannunta ya kama suka shiga cikin daki, ta zauna akan stool ta dan turo baki ta ce “I’m missing my parent Doctor” durkuswa yayi ya kamo hannayenta biyu ya ce “Not when u have me dear, tashi muyi sallah” make kafada tayi ta ce “Ai nayi sallah a gida” ya ce “I know, wancen da wannan ba daya bane” ta ce “To amma ai nace maka nayi” ya ce “Kinyi kuka ba, ur eyes are red” sauke kanta tayi ta daina kallansa ta ce “I’m hungry kuma” babban rigarsa ya ajiye a gefenta ya ce “Idan kikai sallah sai kici abincinki” ta dan kalleshi sai kuma ya ce “Sai bacci” ta dan turo baki ta ce “Kafana ciwo yake i can’t walk” tashi yayi ya dagata kamar Baby suka shiga toilet, da alwala suka fito yaja su sukai sallah sannan ta jawo take away din ta fara cin kazar dan yunwa takeji bama wasa ba, shi dai kallanta kawai yake yana murmushi harta gama, ta mike ta dauko cup ta sha fresh milk sannan ta shiga toilet tayi brush ta fito tana kallansa ta ce “Doctor” ya ce “Matar Doctor” tayi saurin rife fuskarta ta ce “Banaso” ya ce “Nine bakyaso” ta dan kalleshi sai ta ce “Tsokalan ne i don’t want” ya kamo hannunta ta zauna gefenshi ya ce “Gist me, meyasa aka fasa event din?” Rafi’ah ta kwanta a jikinshi ta ce “Ikleemah ne ba lafiya” ya ce “Waye ita?” Ta ce “Wacce ta kai maka abinci first time kazo gidanmu” yaja hancinta ya ce “Kice wacce kike kishi da ita” ta dan yatsine fuska ta ce “Ni ina ruwana da ita” bakinshi ya daura akan nata tayi saurin komawa baya ta ce “Are u not sleepy?” Ya ce “Of course, kwana zamuyi muna hira yau” ta dan zaro ido ta ce “Oh oh, ni bacci nakeji” ya ce “Ni banajin bacci to, ya zamuyi” ta dan bude hannayenta alamun bata sani ba ta ce “Nasan kuma kanaji” ya ce “Banaji, i can spend the whole night without sleeping” dariya ta danyi ta koma baya ganin yana kokarin kamota, ya jawota jikinshi ya ce “Sai munyi hira fa” tana dariya ta ce “Then let me sleep sai na baka labarin” ya kara rungumeta ya ce “Bacci zakiyi” ta ce “I won’t” kwantar da ita yayi yana jaan hancinta ya ce “Good” tayi shiru tana saan kwace jikinta ya ce “Wait,,, let me show u something” tsayawa tayi tana kallan phone dinsa da yake dannawa, kashe hasken wayar yayi sannan ya kashe wutan dakin, ta dan zare ido ta ce “Doctor” sai kuma ta yatsine fuska kamar xatai kuka ta ce “Pls stop”.

*Thank u all for d du’ah nagode sosai* .
[8/8, 9:48 AM] Zarah: *_…卮乇賷賰 丨賷丕鬲賷…_*
_{MY LIFE PARTNER}_

*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
_We are here to Educate, Motivate and Entertain our Readers._

_By FATIMA 鉁嶐煆籣

_40_

Bayan kwana 3 da bikin Yusuf Anty Khadija tazo gidansu Rafi’ah, dai dai gate din tayi parking sannan ta fito ta shiga ciki, Mustapha ne kadai a compound din yana wanki caan gindin pampo, ganin bakuwace yasa ya wanke hannunsa ya karaso inda take tsaye, cike da ladabi ya ce “Ina yini Hajiya” a hankali take chewing gum din bakinta, kamar ba zata amsa ba ta ce “Lafiya, ina ne apartment din Amaryar gidan nan?” Mustapha ya nuna mata part din Anty Amina ya ce “Wancen ne Hajiya” ba tare data yi magana ba ta fara takawa zuwa apartment din, bayan ta hau balcony ta danna bell taja gefe ta tsaya. Few seconds aka bude kofar parlor, Anty Khadija ta dinga kallan Ikleemah data dawo kamar skeleton, dan ba karamin rama tayi ba, dan yatsine fuska tayi ta ce “Matar gidan na nan?” Ikleemah ta daga mata kai sannan ta bata hanya ta huce, bayan sun shiga ta turo kofar ta ce “Tana ciki bari na mata magana” daga haka ta haura upstairs Anty Khadija kuma ta nemi waje ta zauna. Da sallama ta bude dakin ta shiga, Anty Rahama dake kwance tayi saurin tashi zaune ta ce “Ikleemah bance karki hawo bane, kina ganin yadda ake fama amma ke bakyajin magana” karasawa tayi gefen mahaifiyarta ta zauna tana sauke ajiyar zuciya, dafe kirjinta tayi a hankali ta ce “Ammi kirjina, wayyo Allah na” cike da damuwa Anty Rahama ta rungumeta ta ce “Allah zai baki lafiya Ikleemah, amma menene na haurowa bayan kinsan nima yanzu zan sauka” silently ta ce “Anty Amina ne tayi bakuwa” Anty Rahama ta ta6e baki ta ce “Koma wacece karki kara yin gangancin haurowa ba tare dani ba, bazaki kwala min kira ba” tana rife bakinta Anty Amina ta shigo dakin da phone dinta a hannu, karasawa wajensu tayi ta ce “Subhanallah, lafiya dai ko?” Anty Rahama ta ce “Ina lafiya Amina, daga kinyi bakuwa wai ta hauro sama kiranki, tana gani jiya sai da muka koma asibiti aka bamu wasu magungunan” Hannun Ikleemah Anty Amina ta kama ta ce “Haba Leemah, so kike ki kara jawo mana wani abun ne, ai yau kam jiki yayi kyau, maza muje kasa a dafa miki abinda kikeso” dagata tayi suka nufi kofar fita Anty Rahama tabi bayansu, a hankali suka dinga saukowa a stairs din saboda Ikleema, bayan sun shigo parlor Anty Amina ta dinga kallan Anty Khadija dake zaune tana danna wayarta. Kwantar da Ikleema tayi akan kujera ta zauna ta ce “Sannu da zuwa” Anty Khadija kallesu ta ce “Yauwa sannu” zama Anty Rahama tayi ta ce “Wa kike nema?” Anty Khadija ta danyi murmushi ta ce “Fatan an gama biki lafiya” harara Anty Rahama ta balla mata ta ce “Malama kinyi kuskure, ai ba anan akayi auran ba da zaki zo mana ban gajiya” murmushi Anty Khadija tayi ta ce “Nasani, nazo ne muyi magana da matar gidan nan” Anty Amina dake kallanta ta ce “Wace irin magana?” Anty Khadija ta gyara zama ta ce “To da farko sunana Khadija Bello, nice yayar Yusuf wanda ya auri ‘yar gidan nan” dan murmushi Anty Amina tayi, bata san Anty Khadija ba amma tanajin labarinta dan ita tayi sanadiyyar raba Yusuf da Nusaiba, a hankali ta ce “Sannu da zuwa Hajiya Khadija, bari a kawo maki abin sha” daga haka ta mike, cikin saurin Anty Khadija ta ce “No, No, karki damu, ba zama nazo yi ba, nazo ne daman muyi magana, nasan kina daya daga cikin makiya auran nan” Anty Amina ta koma ta zauna tana kallan yayarta ta ce “Aiba ni kadai ba, kinga dani da yayata da ‘yarta da Ummanmu da wasu daga cikin danginmu duk ba so muke ba, dalili kuwa shine basu dace ba, ga kuma cuta dake cin yarinyar” Anty Khadija tayi crossing legs dinta tana jijjiga key din mota ta ce “To kun samarwa kanku mafita?” Anty Rahama dake kallanta ta ce “Tukunna dai” juyowa Anty Khadija tayi ta kalleta sannan ta ce “Tukunna fa kika ce?” Anty Rahama ta ce “Ehh, bakiga muna da marar lafiya ba, wannan yarinyar da kike gani sanadin auran nan ta shiga wannan hali” Anty Khadija ta kalli Ikleema sannan ta ce “Allah ya kyauta, to muma dai ta bangarenmu basan auren muke ba, taya za’ai shekara daya da auran ‘yar uwata ya mata kishiya, kishiyarma yarinya karama da bata san ciwan kanta ba, to ni ba dogon magana nazo yi ba, harka ce ta samu yadda zakuji dadi muma muji dadi, idan kun yanke shawarar ga card dina da komai ajiki” tana rife bakinta ta dauko card din ta ajiye akan kujera sannan ta mike ta ce “Sai anjimanku” Anty Amina ta ce “Allah ya kiyaye”. Tana fita Anty Rahama ta kalleta ta ce “Anya kuwa yayarsa ce? Naga basa kama” Anty Amina ta ce “Ba iyaye daya suke ba, inaga a gidansu ya girma, amma kinsan mubi matarnan komai zai tafi dai dai” Anty Rahama ta ce “Nima naga alamun nasara, amma kinsan baza su so Ikleema ta shiga gidan ba” Anty Amina ta ta6e baki ta ce “To shine autan maza? Mu dai idan Rafi’ah zata fito na har abada ai ko ba komai mu mukai nasara, wallahi Ikleema ki kwantar da hankalinki namiji sai kin zama amma ki manta da Yusuf” shiru Ikleema tayi tana kallan Anty Amina, caan ta danyi murmushi ta ce “Na hakura Anty indai itama xata fito, wallahi a yanzu bani da burin daya wuce naga ta gama wulkanta” Anty Rahama ta ce “Gaskiya mu yarda kawai, kuma idan auran ya 6alle sai dai kinga tai ta zama a gida, daga nan suyi rayuwarsu muyi tamu” Anty Amina ta dauka card din tana kallan address din gidan ta ce “Zanje gobe na sameta nima” Anty Rahama ta ce “Bari naje na kira Umma na fada mata komai, daga haka ta mike ta wuce sama tana murmushi.
Gently ya dinga daga kafarsa yadda baxata ji footsteps dinsa ba, juyowa yayi yana kallan Rafi’ah dake kwance akan kujera, mistakenly kafarshi ta bugi center table tayi saurin mikewa tana kallan parlor, komawa yayi bayan kujera da sauri ya buya, ta dinga bin parlorn da kallo jin motsi, mikewa tayi ta leka bayan kujerar suka hada ido, ta turo baki ta koma kan kujera ta kifa kanta ta fara kuka, with lots of disturb ya tashi yana murmushi ya zauna gefenta ya ce “Yanzu fa zan dawo, i just want to buy something akan junction” kwace hannunta daya rike tayi ta ce “Nasan ai wajen matarka zakaje” jawota yayi jikinshi ya rungumeta ya ce “Noo, zan samo mana lunch ne” ta kara turo baki ta ce “Ni bazanci irin na jiya” ya shafa bayanta ya ce “What do u want then?” A hankali ta ce “Egg and bread with tea” ya ce “Meyasa kike shan tea da rana” ta ce “Ni ko yaushe ma idan inasan sha” ya ce “To bari na hada miki” daga haka ya kwantar da ita akan kujera ya fita a parlor, kamshi yaji a kitchen hakan yasa ya nufi nan, Jiddah ce tsaye a gaban gas tana soya kwai, ya rungumeta unexpected tayi saurin juyowa, suna hada ido ya manna mata kiss a kumatau ya ce “How are u, dazu da safe naje na samu kina bacci” ta ce “Fine” daga haka taci gaba da abinda take, yana rike da ita harta gama ta kashe gas din, a hankali ta ce “Zan wuce parlor na ka sakeni” ya danyi murmushi yana kallan egg din hannunta ya ce “Nima zanci” ta hade fuska ta ce “To muje parlor” ya ce “Noo, sai dai ki zuba min nawa” kallansa ta dingayi kafin ta sauke kanta, ya ce “Bazaki bani bane?” Ta ce “Nifa banci komai ba tin safe gashi yanzu karfe 2 ne, kuma idan na zuba maka baxai isheni ba, dama kai zaka ci saina baka, amma wallahi bazan hada abinci wata banza taci ba” Yusuf ya matseta a jikinshi ya ce “Yanzu dai bazaki bani ba kenan” ta ce “Na fada maka ai” ya ce “Zanje eatery na siyo mana abinci yanzu sai mu kara” make kafada tayi ta ce “Nifa bazata ci abincina ba” kin saketa yayi saima kansa daya kwantar a wuyanta, Tana kokawar kwacewa Rafi’ah ta shigo kitchen din, hakan yasa tayi collapsing a jikinshi tana dallawa Rafi’ah harara, ko kallansu batai ba ta wuce ta dauko flask da mug ta fito a kitchen din, kasa hada tea din tayi ta tsaya rike da mug din a hannunta, jin motsi yasa tayi saurin bude flask din zata debi ruwa Yusuf ya ce “What are u doing?” Kin kulashi tayi ta zuba ruwanta sannan ta rufe ta dauka liptopn akan dinning ta saka a ciki, daukan mug din tayi zata wuce part dinta ya riko hannunta ya ce “Sugar fa” juyawan da zatai ta zubo ruwan zafi a kafarta, ta saki kara ta jefar da cup din ya tarwatse a wajen, da sauri Yusuf ya dagata ya ajiyeta kan kujera yana kallan kafar, Jiddah ta dinga hararansu tana murguda baki, cikin rarrashi Yusuf ya ce “Sorry dear, bari na gyara wajen muje mu siyo abinci” hawayen idanta ta share ta ce “Bayan kasa na xubar da tea dina” dariya ya danyi jin ta kirashi da tea, ya san ko me za’ai ba iya sha zata tai ba, ya dagata suka nufi part dinta ya ce “Keda baki da lafiya menene naki na hada tea kuma” a hankali ta ce “Ba kabarni da yunwa ba kaje wajen matarka, meyasa bazan hada ba” ta turo baki ta kwanta akan kujera, murmushi yayi ya fita a parlor ya share inda mug din ya fashe sannan yayi mopping wajen, karasawa yayi gefen Jiddah ya ce “Zamuje eatery me zan kawo maki” girgiza masa kai tayi ta ce “Ni banasan komai” ya bata light kiss ya ce “I know u like shawarma, ita zan siyo maki” bata ce masa komai ya koma part din Rafi’ah, a tsaye ya sameta harta sa hijabi, ya ce “Bafa dake zanje ba” cushion din gefenta ta wurga masa ta ce “Kuma saina bika, ai jiya ma daka fita baka dawo da wuri ba” ya danyi murnushi ya ce “Zance naje ai jiya” ta kara turo baki ta nufi kofa ya bita da kallo yana murmushi, baisan meyasa idan yana tare da ita baya gajiya da kallan abubuwanta ba, key din mota ya dauka ya fita, a parlor ya sameta tsaye tana jiranshi, tayi saurin kama hannunsa ta ce “Harda yawo ma zamuje ko Doctor” ya ce “Eh” rungumeshi tayi tana murmushi ta ce “When are we coming back?” Ya ce “Till night” ta danyi tsalle ta ce “Yess” daga haka suka fita zuwa parking lot Jiddah ta bisu da harara. Sai lokacin Anty Khadija ta koma gida, bayan tayi parking ta shiga parlor da sallama, Umma dake kallanta ta ce “Sai yanzu” ta ce “Ehh na biya clinic ne” Umma ta ce “To ya kukai?” Anty Khadija ta ajiye veil dinta akan kujera ta ce “Kamar dai yadda Malam ya fada hakan take, suma inaga da abinda suka kulla a kasa, shine ya hadu da wanda muke ya kasa bada result me kyau, gaskiya Umma sun mungun tsanar yarinyar” Umma ta danyi murmushi ta ce “Barka, kinga yanzu haduwarmu dasu, zasu bar komai a hannunmu, sai muyi yadda mukaga dama” Anty Khadija ta ce “Hakane, kuma Umma baza suyi tinanin sake wani abun ba, balle su toshe mana hanyar namu aikin” Umma ta danyi dariya ta ce “Dama Malam yace min bamu kadai bane” daga haka Anty Khadija ta mike ta haura upstairs.
Yau ya kama sati 2 da bikin Rafi’ah, tin sassafe ta tashi ta shirya saboda Yusuf ya mata alkawari zai kaita gida yau, sosai tayi kyau ta yafa veil dinta akai, gefenshi ta koma ta zauna ta ce “Doctor” ya dauke kansa akan laptop ya juyo yana kallanta, ta ce “Pls na kwana mana kaji” dan zaro ido yayi ya ce “I can’t sleep here without u, sai dai idan zaki bari jibi kwanan Jiddah sai kije ki kwana” kwantar da kanta tayi akan kafardarsa ta ce “Banaso” ya ce “To ba kwana, da daddare zan dauko ki” a hankali ta ce “Na yarda to, kuma sannan ni…” Shiru tayi ta fasa cewa komai, ya bata side hug ya ce “Now tell me, me zaki ce?” A hankali ta ce “Matarka ta daina shiga harkana tinda bataso mu zauna lafiya, kagani dazu na jona ruwa a kettle shine ta juyemin, hakama jiya ta daukemin Apple dina akan dinning kuma nayi magana tace wai in kwata idan zan iya” shiru yayi yana kallan lips dinta dake motsi, ta kai hannunta kan botton din rigarsa ta ce “Kuma Ummina tace karna sake nayi fada da ita, so kace itama ta daina min haka” bakinshi ya ajiye akan nata ya ce “Ai jiya na mata fada sosai, bazata kara ba” ta ce “To ai yau…” Shiru tayi jin bakinshi cikin nata, tayi saurin janye fuskarta ta matsa a gefensa ta ce “Ba yanzu zamu tafi ba” jinginar da kansa yayi akan gado ya limshe ido, kamar zatai kuka ta ce “Karfe 9 fa yanzu Doctor” bude idanuwansa yayi ya kamo hannunta ta dawo kusa dashi ya ce “Zanyi missing dinki Baby, i so much luv u, banasan naji bakya jikina” daga haka ya rungumeta tsam tsam a jikinshi, cikin rarrashi ta ce “I will miss u too, but ni kam ka tashi mu tafi” ya danyi murmushi ya ce “Tona tashi” ta kama hannunsa ta ce “Let’s go” kashe laptop din yayi ya dauki phone dinsa da key din mota sannan suka fita. Jiddah na zaune a parlornsa tana shan tea, ya ce “Zan kaita gida na dawo” ta juya musu keya bata ce komai ba, har zasu fita ta ce “To meye damuwana da sai ka gayamin, aikin banza kawai” Rafi’ah ta juyo da sauri jin abinda ta fada, sai kuma tayi shiru, Yusuf ya bude kofar suka fita, yana jiwo tsakin da tai amma baice mata komai ba, har sukaje parking lot baiyi magana ba, bayan sun shiga ya tada motar Rafi’ah ta kamo hannunsa ta ce “Dan Allah ka daina fishi Doctor, i apologize on behalf of her” juyowa yayi yana murmushi yaja hancinta ya ce “I’m not angry dear” ta ce “But you’re not smiling” ya ce “Ai nayi” ta ce “Ai saida nayi magana” shiru yayi ya danna horn gateman ya bude sannan suka fita, bayan sun hau titi ta dan kalleshi ta ce “I’m soryy to say ur wife doesn’t have manners of talking”.

_08103810398_ [8/10, 8:46 AM] Zarah: *_…卮乇賷賰 丨賷丕鬲賷…_*
_{MY LIFE PARTNER}_

*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
_We are here to Educate, Motivate and Entertain our Readers._

_By FATIMA 鉁嶐煆籣

_41_

Shiru Yusuf yayi ya ci gaba da driving dinsa, bayan few minutes ta dan kalleshi sannan ta ce “I’m sorry if i hurt u” still baice komai ba, sai bayan minti uku ya ce “Not at all, i don’t feel like talking anymore” jinginar da kanta tayi jikin kujera ta limshe ido, har sukaje gida babu wanda ya kara magana a cikinsu, a kofar gida yayi parking yana kallanta ya ce “Come down” ta ce “Why not kayi parking a ciki to?” Ya girgiza mata kai kawai, ta ce “But Abba zaiyi magana yana nan fa” ba tare daya kalleta ba ya danna horn, bayan Mustapha ya bude gate din ya shigar da motar sannan yayi parking. Fitowa tayi tana kallansa ta ce “Bari na fadawa Ummi tare muke” ya girgiza mata kai, kamo hannunsa tayi cike da damuwa ta ce “My Doctor is anything wrong with u? Kona maka laifi ban sani ba” limshe idanuwansa yayi ya ce “Uhm~uhm, baki min komai ba, kawai naji banasan magana ne, may be…” Shiru yayi ya bude idanuwansa yana kallanta, ta kai hannunta face dinsa ta ce “May be what?” ya girgiza kai ya ce “I’m having Headache kuma haushi nakeji” murmushi tayi ta rungumeshi ta ce “Allah ya baka lafiya” a hankali ya ce “Ameen” tana dago kanta ta hango Anty Amina da Anty Khadija suna tahowa, sai shewa suke suna tafawa, yadda take kallansa shima Yusuf haka yake kallansu, har suka karaso inda suke Rafi’ah na rike da hannun Yusuf dake zaune, ta dan sunkuyar da kanta ta ce “Ina kwanan ku” Anty Khadija ta washe baki tana kallanta ta ce “Amarya har kin fara fita ne?” Kafin tayi magana Anty Amina ta ce “Haba sati biyu fa, ai yaci ace tazo taga mutanen gida” Anty Khadija ta karasa wajen motar tana kallan Yusuf ta ce “Bashi da lafiya ne?” Rafi’ah da kanta ke kasa ta dan sake hannunsa ta ce “Ehh, kanshi ne yake ciwo” sai lokacin ya dago kansa yana kallansu ya ce “Good morning” a tare suka amsa gaisuwar, Anty Khadija ta ce “To Allah ya sauwake” daga haka suka nufi inda motarta take, murya caan ciki ta kalli Anty Amina ta ce “Kingani ko, alamu sun nuna abin ya fara aiki, aina fada miki daga yau komai zai dai dai ta” Anty Amina ta kamo hannunta ta ce “Gaskiya babu abinda zan iya saka miki dashi Khadija, Amma dama nayi alkawarin idan komai ya dai daita akwai filina da zan mallaka miki, nasan dai watakila kinfi karfinsa amma ai kyauta da dadi” Anty Khadija tayi murmushi tana kallanta ta ce “Gaskiya naji dadi sosai, yanzu dai ki koma komai ake ciki zan kira ki” Anty Amina ta daga mata hannu sannan ta koma apartment dinta ba tare data kalli inda su Rafi’a suke ba, dago kansa yayi ya ce “Move, zan rife kofar i’m going home” ta marairaice ta ce “Baza ka gaishe su ba?” Ya girgiza kai ya ce “Some other time, i can’t stay here” matsawa tayi ya rufe kofarsa sannan ya tada motar yayi horn, juyawa tayi duk jikinta a sanyaye ta nufi apartment dinsu, tana hawa balcony ta juyo taga harya fita a gidan, bell ta danna sannan taja gefe ta tsaya, bayan minti 2 aka bude kofar, kallan budurwar data bude kofar tayi sannan ta shiga parlorn, Rafi’ah na murmushi ta rungume Umminta dake zaune akan kujera, Ummi ta shafa bayanta ta ce “How are u daughter?” a hankali ta dago tana kallan Ummi ta ce “I’m fine Ummi, ina Abba?” ta ce “He’s upstairs” daga haka ta mike ta ce “Abdul fa?” Ummi ta ce “Yana dakinshi” upstairs ta wuce tana murmushi ta ce “Let me see Abba first” tana shiga dakinsa ta sameshi yana zaune akan stool, Abba yayi murmushi ganinta ya ce “Is this my Mum?” Itama murmushi tayi ta zauna a kan carpet ta ce “Ina kwana Abba” ya ce “Lafiya kalau Mamana how are u and everyone?” Ta ce “All fine Abba, tare muka zo amma kanshi na ciwo shine ya wuce gida” Abba ya ce “Subhanallah, i will call him ltr, Allah ya sauwake” ta ce “Ameen” mikewa tayi ta ce “A huta gajiya Abba” ya ce “Alright Mother” tana fitowa a dakin ta shiga dakinta, yana nan yadda ta barshi sai kamshi yake, ta kwanta akan gadon tana murmushi ta ce “I missed u bed” daga haka ta mike ta fita a dakin ta sauko kasa. Abdul na gefen Ummi yana taya ta arranging papers, ya dan zaro ido ya ce “Anty” ta rungumeshi ta ce “Ya kake, tashi min a gefen Ummina” dariya Abdul ya dinga yi yana kallanta ya ce “Ai ke mun kyautar dake, yanzu ni kadai ne ko Ummi?” ta shafa kansa ta ce “Exactly Babana, tashi dai ka bata wajen tinda ita bakuwa ce” turo baki Rafi’ah tayi jin ance mata bakuwa, Side hug Ummi ta mata ta ce “So ya kuke, i hope everything is going fine?” A hankali ta Jinginar da kanta ajikin mahaifiyarta ta ce “Lafiya kalau, amma ba shida lafiya ne” Ummi ta ce “Subhanallah, meya sameshi?” Cike da damuwa ta ce “Ciwan kaine, dama fa akan da yamma idan yazo daukana zamuje gidan Mummy” Ummi ta ce “Ki bari next time sai kije kawai” a hankali ta ce “Toh, mai aiki kika dauka Ummi?” Ta ce “Ehh, ko karna dauka” Rafi’ah tayi murmushi ta ce “A’a ai aiki zai maki yawa” Ummi tayi murmushi tana shafa kanta ta ce “I hope bakya saan jikin ki nan” ta ce “Noo, da sassafe nake komai Ummi” Ummi taja hancinta ta ce “Good kici gaba da haka kinji first born, watarana zaki ga amfaninsa” a hankali ta ce “Insha Allah” daga haka ta mike ta wuce kitchen.
Da yamma Rafi’ah na zaune a dakinta duk ta shiga damuwa, ta kira Yusuf yafi a kirga amma ko daya baiyi picking ba, bude kofar dakin akai, tayi saurin juya kanta saboda idanta duk yayi jaa sakamakon kuka data yi, karasowa kusanta Ummi tayi ta ce “Idan bazaki tafi ba in kira Abbanki in fada masa, sau uku ina aiko Saudatu ta kira ki amma kinyi zamanki” mikewa tayi a hankali ba tare da kalli Ummi ba ta dauki Hijab har kasa cikin sauran kayanta sannan ta nufi hanyar fita, Ummi dake kallanta ta ce “Wait Fatima, wani abu na daminki ne?” A hankali ta girgiza kai, Ummi ta ce “Toh Allah ya kiyaye kije Mustapha ya kaiki, Abba kuma kya kirashi dan dawowarsa sai dare” slowly ta share hawayen daya sakko mata, ga zafin barin gida, ga damuwarta na halin da Yusuf yake ciki, gani take kamar yana nan kwance ba lafiya, cikin muryar kuka ta ce “Allah ya dawo dashi lafiya, na tafi” cike da tausayin Rafi’ah Ummi ta ce “Allah ya kiyaye” daga haka ta wuce dakinta. A hankli ta sauko a stairs din ta fita zuwa parking lot ta shiga mota, Mustapha yaja motar suka tafi, har sukaje gida ba tai magana ba, sai da yayi parking ta ce “Thank u” daga haka ta fito ta shige gate. Da sauri ta karasa entrance din gidan ta murda handle din kofar, still ta tsaya tana kallan Yusuf dake kwance yayi pillow da cinyar Jiddah, tayi saurin kauda kanta duk suka bita da kallo harta wuce part dinta, tana shiga ta turo kofar ta durkusa a wajen ta fara rera kuka, kusan awa daya tana zaune a bakin kofa kafin ta mike ta shige dakinta ta rufo kofa, tana nan zaune har akai magrib ta tashi tayi alwala tayi sallah har akai isha tana zaune akan sallayar, ta mike tayi isha sannan ta dauki towel ta shiga toilet tayi wanka, tana fitowa ta samu Yusuf a bakin gado yana zaune da laptop a gabansa, sauke kanta tayi ta nufi inda kayanta suke ta dauki night dress sannan ta koma toilet ta shirya, scarf ta saka bayan ta fito sannan ta karasa gefenshi ta zauna, a hankali ta ce “How are u now?” Ba tare daya kalleta ba ya ce “Better” tayi shiru tana kallansa, dago kansa yayi suka hada ido tayi saurin sauke kanta ta ce “Dan Allah kayi hakuri idan na maka laifi Doctor” girgiza kai ya danyi kafin ya ce “How many times zance miki bakimin laifi ba, ko kin daina fahimtar magana ne” hawaye ne tap a idanta jin yadda yayi maganar, cikin muryar kuka ta ce “U never shout at me, meyasa zakamin tsawa yau” hannunta ya kamo ta matso kusa dashi ya rungumeta very light, dan bai bari sun hada jiki sosai ba, ya ce “I’m sorry, i don’t know what comes over me, haushin kowa nakeji yau, especially…” Shiru yayi yana rike da ita, ta dan sake shi tana kallansa ta ce “Ni ko?” Daga haka ta fashe da kuka, matsowa yayi ya kara rungumeta sosai ya ce “Bance ba, but haushi nakeji kawai” cikin kuka ta ce “Kayi addu’a mana” ya ce “Nayi” daga haka ya saketa ya kwanta akan gadon, share hawayen idanta takeyi tana kallansa ta ce “Or is it because nace matarka bata iya magana ba da safe?” Shi dai kallanta kawai yake, caan ya mike ya dauki pillow ya koma parlor ta bishi da kallo, duk yadda taso ta hakura karta bishi kasawa tayi, bayan 30 minutes ta leka parlorn ta sameshi saman kujera har yayi bacci, a nan wajen ta sulale ta fara kuka sosai.
Washegari da sassafe ta tashi ta hada masa breakfast sannan tayi wanka, tana shigowa dakin ta sameshi ya shirya, ta danyi kasa da kanta ta ce “Good morning” kai kawai ya daga mata, daga haka ya dauki briefcase dinsa da statescope zai fita ta ce “Breakfast din yana kan dinning” ya girgiza kai sannan ya fita a dakin, bin bayansa tayi har suka fito main parlor, ya gama saka takalmi sannan ya dauki komai nasa zai fita ta ce “Doctor breakfast din fa” ba tare daya kalleta ba ya fice ya rufo kofar, Jiddah dake zaune akan dinning ta sheke da dariya, duk yadda Rafi’ah taso kar tayi kuka amma hakan bai yuwu ba, ta fashe da kuka ta koma part dinta, jikinta har rawa yake ta zube aKan gado tana kuka me cin rai. Haka Rafi’ah taci gaba da hakuri, tin daga ranar duk maganar da zatai masa sai dai ya daga kai koya girgiza mata kai sai kace kurma, amma idan da Jiddah ne sukanyi hira wani lokaci, wani lokaci kuma zai kulata amma ba sosai ba, Rafi’ah kuwa babu abinda yake hadasu, yanzu a parlor ma yake kwana indai a dakinta yake, wani lokaci tayi kuka harta godewa Allah, wani lokaci kuma tayi hakuri amma ko kadanne saita zubar da hawaye, a haka har ta cika wata daya a gidansa duk ta kara ramewa tayi farii sosai saboda damuwa, kuma koda wasa bata gayawa kowa a gida ba. Ranar Saturday da yamma tana zaune a main parlor aka fara knocking, ta mike a hankali ta karasa kofar sannan ta bude, rungumeta Khairiyya tayi ta ce “Oyoyo Anty” itama rungumeta tayi tana kallan Ammi ta ce “Sannu da zuwa Ammi” Ammi ta shigo parlorn tana murmushi ta ce “Sannu Fatima” Rafi’ah na rike da hannun Khairiyya ta ce “Have a seat Ammi” Ammi ta zauna akan kujera, zama Rafi’ah tayi a kan carpet ta ce “Ina yini?” Ammi ta ce “Lafiya kalau Fatima, fatan duk kuna lafiya?” Ta ce “Alhamdulilah Ammi” mikewa tayi ta shiga kitchen Khairiyya ta biyota, abinci ta kai wa Ammi da fruits sai dambu da Mummy ta aiko mata jiya, bayan ta gama jere mata ta dauko fanta guda biyu da cups ta ajiye mata, Ammi ta danyi murmushi ta ce “Sannu da kokari” ita dai murmushi kawai take kanta na kasa, Khairiyya ta zuba abincinta ta fara ci, Rafi’ah na kallanta ta ce “Yaushe zaki zo mana hutu?” Khairiyya ta ce “Soon Anty, muna gama exams zanzo, jss3 zan shiga fa” Rafi’ah ta danyi murmushi tana kallanta ta ce “Masha Allah, i wish u all d best”
“Shiru Rafi’ah baku zo mana ba muma bamu zo ba” dagowa tayi jin muryar Ammi, with smile on her lips ta ce “Ammi ai yanzu baya dawowa da wuri sai yamma sosai shiyasa, kuma har weekend fita yake” kafin Ammi tayi magana aka bude kofar, ya shigo yana kallansu sannan ya nemi waje ya zauna, silently ya ce “Sannu da zuwa Ammi, ina yini?” Ta ce “Lafiya kalau, yanzu nake tambayarka ai, baka kaita ba kai baka zo ba muma kuma shiru” dan shafa kansa yayi yana murmushi ya ce “Wallahi Ammi aiki ne yamin yawa yanzu, amma insha Allah zamu zo” ta ce “To Allah ya kaimu” Khairiyya na kallansa ta ce “Yaya ina yini” ya ce “Lafiya Ammina, karfa ki cinye mana abincin mu” ta danyi murmushi ta ce “Ai Anty Fatima zata dafa maka wani” kallan Rafi’ah dake zaune ya danyi sannan ya dauke kai ya ce “Sai dai ke ki dafa min ai” ta danyi murmushi taci gaba da cin abinta, Yusuf ya ce “Ammi ke ba xaki ci abincin ba?” Ta ce “Alhamdulilah Yusuf na koshi” ya ce “Sameer ya tafi ko?” Ta ce “Ya tafi Dubai sai bayan wata biyu kuma” Yusuf ya ce “Ayyah, ya sameni a office jiya ai, so munyi sallama” ta ce “Haka yake cemin, shine nace ai yau bari nazo tinda kunki zuwa” cire hular kansa yayi ya ce “Zamuzo Ammi, Jiddah taje gida za tayi kwana biyu” Ammi ta ce “To Allah ya dawo da ita lafiya, na zata ai tana ciki ta ki fitowa ne” ya dan zaro ido yana murmushi ya ce “Never, ai ba zata jiki tayi shiru ba” Ammi ta ce “Hakan kake gani” daga haka ta kalli Khairiyya ta ce “To idan kin gama ciye~ciyen ki tashi mu tafi, dan idan magrib yayi driving wahala yake min” Yusuf ya ce “Har yanzu Ammi” ta ce “Har gobe kuwa Yusuf bana samun nutsuwa” daga haka ta mike, tashi Rafi’ah tayi ta ce “Mungode Ammi” Ammi ta ce “Ba komai, sai kunzo din” Khairiyya ta kama hannun Rafi’ah ta ce “Anty sai na zo hutun” Rafi’ah ta ce “Sai kinzo” Hijab dinta ta dauka akan kujera ta saka sannan tabi bayansu, har mota suka rakasu, Yusuf nata murmushi har suka tafi, juyowa yayi zai koma cikin gida suka hada ido, sai da kirjinta ya buga tayi saurin dauke kanta, ita tama manta raban da yayi mata murmushi ko magana, kusan sati uku da kwanaki kenan, sai daya shige ya rufo kofa sannan ta shiga itama. Da dare Yusuf na kwance a parlor ta fito sanye da Hijab ta zauna gefensa, a hankali ta ce “Doctor” ya bude idanuwansa yana kallanta, ta ce “Gobe zanje follow up clinic, maganina ya kusan karewa” sauke idansa yayi a kanta ya ce “Wa zai kaiki?” Sai yau ya mata magana bayan sati uku da suka wuce, ta kauda kanta gefe hawaye taap idanta ta ce “Cab” maida kansa yayi gefe ya limshe ido, ta tashi ta koma daki tana goge hawayen idanta, dama tasan yanzu duk duniya ba wanda ya tsaneta kamar Yusuf, babu abinda yake 6ata mata rai irin rashin magana da yake mata, fashewa tayi da kuka ta jawo wayarta akan drawer zata kira Mummy, kawai kuma ta fasa ta gefar da wayar a kasa, kuka sosai take tana kiran sunan Abbanta, da tasan haka rayuwar aure yake da tin tini bata yarda da Yusuf tayi aure ba, gaba daya yanzu ta tsani kanta da komai nata, cikin kuka ta ce “Nina jawowa kaina, Ummi dan Allah ki yafemin, bansan haka zai faru dani ba, i’m tired with this misrable life na gama gajiya” shiru ta danyi jin an bude kofar dakin, ta dago kanta a hankali ganin wanda zai shigo.

*Gashi harda na jiya 馃 Sorry for keeping u waiting.*

_08103810398_
[8/11, 1:23 PM] Zarah: *_…卮乇賷賰 丨賷丕鬲賷…_*
_{MY LIFE PARTNER}_

*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
_We are here to Educate, Motivate and Entertain our Readers._

_By FATIMA 鉁嶐煆籣

_42_

A hankali Jiddah ta tura kofar dakin ta rufe, ta kama kugu tana murmushi ta ce “Dama duk macen da tasan inda yake mata ciwo bai dace ta shigo gidan wata ba, gashi kin shigo banda azaba babu abinda kike sha” kwashewa da dariya tayi tana tafa hannu, Rafi’ah ta kauda kanta tana share hawayen idanta, Jiddah sake cewa “Gara ki tattara naki ya naki kibar mana gidanmu kafin abu yayi tsanani, dan yanzun nan ya gama gayamin ya tsaneki fiye da kowa a duniya” tana fadin haka ta juya ta fice a dakin. Tsabar bakin ciki kasa kuka tayi ta kifa kanta akan gado numfashinta yana neman sarkewa, a hankali ta jawo wardrobe din dake gefenta ta dauko drugs dinta, bayan ta balla ta mike ta dauki guntun pure water ta hadiye maganin, komawa kan gadon tayi ta kwanta tana addu’a ko zata samu saukin abinda take ji. Washegari da tinda ta tashi ta gama abinda za tai ta shirya tana jiran Yusuf saboda clinic da zata je, shiru yana dakin Jiddah ko lekowa baiyi ba, Rafi’ah na zaune a parlor Jiddah ta fito da plate din abincin a hannunta, sai rakwarkwasa take tana murmushi, bayan ta ajiye plate din ta koma part dinta tana dariya, shiru har bayan azahar Yusuf bai fito ba, Rafi’ah dake kwance ta jawo phone dinta tayi dialing number Ameera, yana shiga ta dauka ta ce “Amarya, how are u?” Cikin sanyin murya Rafi’ah ta ce “Fine, where are u now?” Ameera ta ce “I’m at home, do u need something?” Limshe ido Rafi’ah tayi ta ce “I want to see u Khadijah” Ameera ta ce “To bari nazo yanzu” hanging wayar Rafi’ah tayi ta share hawayen idanta ta koma ta kwanta. Bayan minti 15 taji ana knocking, ta mike ta fita a dakin, tana bude kofar Ameera ta rungumeta ta ce “I missed u friend, how are u?” Murmushi kawai Rafi’ah tayi ta kama hannunta ta ce “You’re welcome” daga haka suka shiga part dinta, har dakin Rafi’ah ta shiga da ita suka zauna, Ameera dake kallanta ta ce “Kinyi rama and kin kara fari, is anything wrong?” Tare hawayen idanta takesan yin amma hakan bai yuwu ba, ta rungume Ameera ta fashe da kuka ta ce “I’m tired Ameera, na gaji da zaman auren nan kuma” zaro ido Ameera tayi tana kallanta ta ce “What are u saying Rafi’ah? Indai matsalar Jiddah ce ba sai kin shiga harkarta ba” Rafi’ah ta hau girgiza kai cikin kuka ta ce “No it’s Doctor, Ameera bansan da wani ido zan kalli Ummina na fada mata na gaji da auren Yusuf ba” kara fashewa tayi da kuka ta sulale kasa ta zauna akan carpet, Ameera ta sauko itama tana kallanta ta ce “Pls explain further, ban gane abinda kike fada ba”. Share hawayen idanta tayi ta ce “Ameera Doctor ya tsaneni, tin satina biyu a gidan nan nake ganin ba dai dai ba, baya min magana, baya cin abincina, baya min komai da kika sani, ko dakina baya shigowa yanzu” daga haka ta fashe da kuka ta turo baki ta ce “Wannan ma shiya dama ai, ni babban damuwana daina min magana da yayi, i’m in pain Ameera, my heart is always beaten, it hurts me morethan u know Ameera” ganin yadda take kuka yasa idan Ameera ma ya ciko da hawaye, gaba daya ta shiga damuwa itama, ko a mafarki bata tinanin Yusuf zaiyi abinda Rafi’ah ta fada ba, amma gashi a zahiri tin aure na wata daya matsaloli iri iri, lallai yau ta yarda maza abin tsoro ne.
Share hawayen daya gangaro mata tayi ta dago Rafi’ah dake kuka kamar ranta zai fita ta ce “Have u tell anyone?” Rafi’ah ta girgiza kai ta ce “Noo, dan Allah karki fadawa kowa banasan hankalinsu ya tashi, and beside that inasan mijina, no matter how zan zauna dashi har karshen rayuwata” Ameera ta shiga share mata hawayenta ta ce “No Fatima, u have to tell someone ko zaki samu mafita, u can’t be hurting yourself this much, bayan haka ma bakya tinanin ciwanki ya tashi” Rafi’ah ta rungumeta ta ce “Dan Allah promise me u won’t tell anyone, Khadija kar ki bari wani yaji zancen nan, pls keep my secret only u Ameera” fashewa ta karayi da kuka jikinta na rawa, Ameera dake kuka itama ta ce “Ohk i promise u that i will keep this secret alone, amma meya kamata muyi yanzu?” Rafi’ah ta saketa ta fara goge hawayen idanta ta ce “U help me praying Ameera, nasan dai tinda nake ban ta6a cutar wani ba, so Allah ba zai bari a cuceni ba nima” Ameera ta ce “Insha Allah zan taya ki da addu’a, kuma zaki cinye wannan jarabawar da yardar Allah” Rafi’ah ta share mata idanta ta ce “Nagode Ameera, dama inasan in baki hand card dina na asibiti, sai ki kar6omin drugs dina, zan kira Doctor Hisham na gaya masa” Ameera ta ce “Ohk ba komai zan kar6o maki yanzu” tashi Rafi’ah tayi ta dauko hand card dinta cikin jaka ta mikawa Ameera ta ce “Zakiga office dinsa da sunansa a jiki, zan kirashi sai na masa bayani” ta ce “To shikkenan, kinci abinci ne?” Girgiza kai Rafi’ah tayi ta ce “Zan dafa anjima naci” Ameera ta yafa veil dinta ta ce “Ohk saina dawo” daga haka ta fita a dakin, kwanciya Rafi’ah tayi ta kira Dr. Hisham, bayan sun gama wayar taja blanket ta rufu har kanta, dan wani sanyi take ji yana ratsata har cikin jikinta. Tana nan kwance har Ameera ta dawo, Rafi’ah na jin an bude kofar ta mike zaune, Ameera ta karasa kusanta ta ce “Are u ok?” Ta daga mata kai kawai, Ameera ta ajiye mata ledan drugs din ta ce “Yace kinsan yadda kike sha ko?” Ta daga mata kai ta ce “Yes i know” daga haka Ameera ta mika mata wani leda mai takeaway a ciki ta ce “Ga abinci na siyo miki, u don’t have to cook” murmushi Rafi’ah tayi ta ce “Thank u so much” Ameera ta mike ta ce “I’m going Fatima, Abbana ya kirani da ina hanya, idan kina bukatar wani abu u call me, ko Sajeed zan bawa ya kawo maki” Rafi’ah ta kamo hannunta ta ce “Thank u so much Khadijah, i don’t know how much to thank u friend, nagode sosai” Ameera ta ce “Mention not, sai anjima” daga haka ta fita a dakin, tana fita Rafi’ah ta share hawayen idanta sannan ta koma ta kwanta. Ba ita ta shi ba sai kusan la’asar, ta shiga toilet tayi wanka tayi alwala sannan ta fito, gaban mirror ta zauna ta shafe jikinta ta tashi tasa kaya, tayi kyau sosai sai dai kana kallanta kaga rama sosai da damuwa a tattare da ita, takeaway din da Ameera ta siyo mata ta bude, tana kallan abincin ta fara yatsina fuska, spoon ta dauka ta debi fried rice din ta kai bakinta, da sauri ta zubar jin yadda zuciyarta ke tashi, ta rufe takeaway din ta ajiye a gefe sannan ta mike ta shiga toilet ta wanke bakinta ta dawo ta kwanta.
Da dare kasa kwanciya tayi saboda yunwa dake daminta, ta fito a blanket ta dauka himar dinta ta saka ta fita a dakin, ba kowa a main parlor sai dai tana juyo muryarsu a parlorn Jiddah, ta dan turo baki ta shiga kitchen, tsayawa tayi tana bin kitchen din da kallo ko zata ga abinda ranta yake so, flour ta duba taga babu, ta tsuguna tayi tagumi, babu abinda take kwadayi taci sai dan wake, mikewa tayi ta bude fridge ta dauki fanta da glass cup ta koma part dinta, ta kai minti 6 tana kallan Fantan kafin ta zuba a cup ta dauka ta kai bakinta, tin kafin ta hadiye ta fara kakarin amai, tayi saurin zubar dana bakinta sai sauke numfashi take tana kallan sauran fantan dake cikin cup din, mikewa tayi ta shiga toilet ta wanke bakinta sannan ta fito ta dauki bottle din fantan ta jefar ta window, sauran na cup dinma ta zubar dashi sannan ta ajiye cup din akan drawer ta neki waje ta zauna.
Haka Rafi’ah take ta faman shan wahala ita kadai har tsawon sati uku, wani lokaci ta samu abinda takeso wani lokaci idan babu ta hakura tayi kuka ta share ko kuma ta kira Ameera, kullum sukai waya da Ummi ko Mummy bata ta6a fada musu abinda ke faruwa, laulayi take sosai amma ko kadan bata kawowa kanta ciki ne da ita ba, ga mungun zazza6i da take kwana dashi duk dare, duk ta kara ramewa tayi mungun haske, ita kanta batajin nauyin jikinta saboda ramar da tayi. Ranar Monday da Yamma tana zaune a bakin gado ta buga uban tagumi, damuwarta bai wuce kiran da Mummy ta mata ba na cewa zata zo, duk sanda ta tuna sai kirjinta ya buga, tana nan zaune wayarta ya fara ringing, ganin Mummy ce yasa ta danyi jiim kafin ta dauka, Mummy ta ce “Kina jina Fatima?” Ta ce “Ehh Mummy” ta ce “Kiyi hakuri na fasa zuwan, kinga Ikram ne ba lafiya yanzu haka muna hanyar asibiti” wani 6oyayyen ajiyar zuciya ta sauke kafin ta ce “Ohk ba komai Allah ya bata lafiya” Mummy ta ce “Ba damuwa ki gaishe da Yusuf din” daga haka tayi hanging call din, tana nan zaune aka danna bell, ta mike a hankali ta zura hijabi har kasa sannan ta fita ta bude kofar, Khairiyya ta rungumeta ta ce “Anty” Rafi’ah na murmushi ta ce “You and who?” Ta ce “Driver ya kawoni” Rafi’ah ta tura kofar ta kama hannunta suka shiga ciki, a parlor suka zauna Khairiyya ta ce “Ina yini Anty” Rafi’ah ta ce “Fine, how is Ammi?” Ta ce “She’s fine, tace na gaisheki wai yaushe zaki sake zuwa” Murmushi kawai tayi bata ce komai ba, ita gidansu ma sau biyu kawai taje, Khairiyya ta ce “Anty jiya na gama exams dina, jss3 zan shiga next term” Rafi’ah ta gyara mata himar dinta ta ce “Good, Allah ya sanya alkhairi, kiyi karatu sosai” Khairiyya ta ce “Sure, i want to be a medical doctor just like Yah Yusuf” Rafi’ah ta ce “Allah yasa to” mikewa tayi ta ce “Let me get something for u” Khairiyya ta ce “Anty indomie zanci” Rafi’ah ta juyo tana kallanta ta ce “Can u cook?” Ta ce “Yess ina dafa indomie, white rice, spaghetti, macaroni and also…” Da hannu Rafi’ah ta nuna mata kofa ta ce “To kije ki dafa, banasan surutu” Khairiyya ta danyi murmushi ta mike ta ce “Anty are u sick?” Ta girgixa mata kai kawai, tana fita Rafi’ah ta rufe kofar dan babu abinda ta tsana kamar aroma din indomie, kwanciya tayi akan gado taja blanket ta rufe duka jikinta. Bayan minti 10 taji Khairiyya na kiranta, ta janye blanket din jikinta ta ce “What khairiyya?” Phone dinta ta mika mata ta ce “Ana kiran wayarki kuma number ne” kauda kanta gefe tayi saboda kamshin indomie daya bugi hancinta, Khairiyya ta ce “Should i pick the call?” ganin yadda Rafi’ah take yasa ta matsa baya tana kallanta ta ce “Is like u are not well Anty” da sauri Rafi’ah ta mike ta sauko a gadon, kafin ta karasa toilet ta fara kwararo amai a kan tiles din dakin, ta durkusa a wajen taci gaba da kwararo shi kamar zata fitar da kayan cikinta. Khairiyya da jikinta ya gama sanyi ta ajiye plate din indomie ta nufi inda take ta tsuguna gabanta ta ce “Sorry” kwanciya Rafi’ah tayi a kasa tana sauke ajiyar xuciya, Khairiyya ta mike ta fita a dakin da sauri, tana fita parlor Yusuf na shiga part din Jiddah, tabi bayansa da gudu ta ce “Yaya” juyowa yayi yana kallanta ya ce “When did u came?” Ta ce “Tin daxu, Anty bata da lafiya fa” Yusuf ya juya ya shige parlorn Jiddah tabi bayansa, akwatuna ne guda 4 manya manya a tsakiyar parlorn, Jiddah ta fito a daki tana kallan Yusuf ta ce “I think we have to go, kayi abinda Umma tace maka?” ya zura hannunsa a aljihu ya dauko karamar paper ya ce “Here it is” Jiddah tayi murmushi ta ce “To akwatinan a kai parlor, bayan nan ka bata takardar ka sameni a mota” ita dai Khairiyya na tsaye tana kallansu, Jiddah ta wurga mata harara ta ce “Ubanwa kika tsaya kalla anan?” khairiyya tayi saurin jaa baya ta ce “Ni bake nake kalla ba” sai kuma ta kalli Yusuf dake jan akwatina zai kai waje ta ce “Yayah i’m talking to u, Anty Fatima bata da lafiya” ko ya daga kai ya kalleta, tabi bayansa har ya fito balcony, ya bawa mai gadi yace a sa a mota sannan ya koma ya dauko sauran ma ya kawo masa, Khairiyya ta kama hannunsa ta ce “Yayah” cikin tsawa ya ce “What.. What do u want?” Ta fashenda kuka ta ce “Anty bata da lafiya, she’s vomiting yaya, kazo ka ganta pls” fisge hannunsa yayi ya shiga parlorn sannan ya wuce daki, tana nan kwance ga amai a gabanta kaca~kaca gaba daya tayi weak ko hannunta bata iya motsawa, Khairiyya ta kalleshi ta ce “Kagani tun daxu tana kwance a kasa” tsugunawa Yusuf yayi yana kallanta ya ce “I’m leaving Fatima, i can’t stay with u anymore, kinci amanata ba kadan ba, na soki tsakani da Allah but u betrayed me, mena maki da zaki saka min da haka, ba dan Jiddah ba da tin tini kin kasheni, so i want to tell u that i hate u, Jiddah kadai nakeso, na tsaneki Fatima, i will go far away from u, i will distance my self from seeing this ur ugly face” ita dai kallansa kawai take ta kasa magana, Khairiyya ta durkusa tana kuka jin abinda yake cewa, a hankali ya zura hannunsa ya ciro takarda ya bude hannunta na dama ya saka mata a ciki ya ce “Finally u take this, the only solution kenan da zan samu peace of mind” daga haka ya mike ya fita a dakin, sai lokacin hawaye suka dinga sakkowa a idanta, ta mike a hankali tana kallan paper hannunta, jikinta na rawa ta bude paper, bayan ta gama karanta content din two lines ta saki kara ta fadi a wajen sumammiya, Khairiyya ta mike ta karasa wajenta tana jijjigata amma ko motsi batayi, tana kuka ta dauki wayar Rafi’ah ta fara dailing number Mummy. Kallan Jiddah Yusuf yayi ya ce “Where are we heading to?” Cike da isa ta ce “Kaduna mana, su Umma suna caan suna jiranmu, gobe da safe kuma mu keta hazo” Yusuf ya danyi murmushi yaci gaba da driving ya ce “I so much luv u, Umma, and Khadija, u mean alot to me, bansan ya zan saka muku ba” Jiddah tayi murmushin gefen baki ta ce “We love u too Yusuf Muhammad”

_08103810398_
[8/12, 10:27 AM] My Imaan: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation
*_…卮乇賷賰 丨賷丕鬲賷…_*
_{MY LIFE PARTNER}_

*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
_We are here to Educate, Motivate and Entertain our Readers._

_By FATIMA 鉁嶐煆籣

_43_

Ummi ce zaune a room din da akai admitting dinta, drip ne a hannunta na dama dayan hannun kuma tissue ne a ciki, lokaci~lokaci tana goge hawayen dake sakkowa kumatunta. Kusan awanta 5 da tashi kenan amma har yanzu Rafi’ah bata farfado ba, jin an bude kofar yasa ta daga kanta tana kallan direction din kofar, Abba ya shigo dakin ya zauna gefenta, kana kallan idanuwansa kasan shima yayi kuka, ga rashin jin dadi a fuskarsa karara, karfin hali kawai yake a matsayinsa na babba wanda ya yarda da kaddara either good or bad. Kamo hannun Ummi yayi ya ce “Ya jikin?” Ta share hawayen idanta ta ce “Da sauki” Abba yayi shiru yana kallanta kafin ya ce “It is a test from God Zainab, babu kuma wanda ya isa ya wuce kaddararsa a rayuwa, idan Allah ya rubuta zai faru definitely it might happen, amma dan Allah ki daina kuka haka nan, nasan abin da ciwo, it really hurt us, musamman keda kika haifeta” Ummi tayi shiru kawai tana ci gaba da goge idanta, Abba ya juyo yana kallanta sosai ya ce “Itama ta tashi yanzu, amma dan Allah idan kikaje kar kiyi kuka, pray for her, u are a mother, don’t make her to give up in life, encourage her, support her, karki bari ta tsaneni aure at this her age, it’s a destiny” a hankali ta ce “Insha Allah, kun kira shi dinne?” Abba ya ce “I called him, ya kuma ce ya saketa so muyi hakuri kawai, nata kaddarar kenan” Ummi ta kara share hawayen idanta ta ce “She’s pregnant fa Abbu Rafi’ah, wallahi bazan yafewa Yusuf ba, dama tun farko abinda nayi gudu kenan” Abba ya girgiza kai ya ce “That should not be a problem, fatana Allah ya raba lafiya, ko guda 100 zata haifa i can take care of them, kawai kici gaba da addu’ah, soon komai zai zama tarihi, shi kuma watarana zaiyi nadama” Ummi ta ce “Hakane, Allah ya bamu ikon cinye wannan jarabawar” ya ce “Ameen” daga haka ya zare mata drip din hannunta ya ce “Ki daure ki mata sannu don’t forget all i said” Ummi ta gyara hijabinta kawai ta nufi kofar fita walking slowly, dan ji take kamar zata kara faduwa, kamata Abba yayi har suka je dakin da Rafi’ah ke kwance, Abba ya bude kofar suka shiga, Mummy ce tsaye a kanta tana rarrashinta, sai maganganu take anyhow komai yazo bakinta fada take, dayan side din kuma Ammi ne tsaye da Khairiyya sai share idanta take da hijabi, Anty Amina dasu Anty Rahama ma suna tsaye, sai goge hawayen munafirci suke, Mummy ta dago jajayen idanuwanta da suka kumbura tana kallan Ummi ta ce “Sannu” Ummi ta daga mata kai tana kallan Rafi’ah dake kwance, a hankali ta karasa kusanta ta ruko hannunta, jikinta zafi gaau, tana kallan Ummi ta zabura ta mike ta rungumeta, fashewa tayi da kuka tana fadin “Ki yafemin Umminah, ya sakeni for no reason, ban masa komai ba sai ma shine yake cutana for almost 2 months, ban ta6a fadawa kowa ba, pls Ummi kuce karyamin haka, never thought i will be divorced at this my age” saketa Ummi tayi ta fita a dakin saboda kuka da take itama, Mummy ta kama hannun Rafi’ah ta zaunarta akan gado ta ce “So u haven’t heard all i said Fatima” cikin kuka ta ce “Naji Mummy, but u people should let me cry, idan banyi ba bazanji dadi ba, Allah ya Allah idan mafarki nake kasa na tashi yanzu” rungumeta Mummy tayi ta dinga jijjigata tana fada mata kalaman da zasu mata dadi, bayan kusan minti 30 tayi shiru tana bin kowa na dakin da kallo, Mummy ta kwantar da ita ta ce “Kiyita addu’ar dana fada maki dazu, dan Allah u stop crying, kinsa Umminki na caan tana kuka, so kike BP dinta yayi raising ne?” Ta girgiza kai a hankali hawaye na sakko mata ta ce “Indai a kaina take kuka nima na daina, kice mata bazan kara ba Mummy” Mummy ta ce “To karki kara, ki kwanta kiyita addu’a” mikewa tayi ta kwanta tana kallan Abdul dake share hawaye yana zaune akan kujerar dake opposite din gadon da take. Mummy na fita taji hawaye masu zafi na sakko mata, ta share idanta sannan ta karasa dakin da Ummi take, tana zaune Abba na gefenta ya hada mata tea, Mummy ta shigo dakin tana kallansu ta ce “Zakici abincin ne?” Ummi ta girgiza kai ta ce “Na koshi” Mummy ta ce “Allah ya sauwake”. Bata wani jima a nan b ta koma dakin da Rafi’ah take, tana nan kwance bakinta na motsi tana ta addu’a, kujera taja ta zauna itama, duk dakin yayi shiru sai numfashinsu kakeji a hankali, jin an turo kofar yasa Mummy ta daga kanta tana kallan Mami data shigo, Mummy ta ce “Ya mai jikin?” Mami na kallan Rafi’ah ta ce “Ai taji sauki, cikinma ya daina ciwan, sun sallamemu yanzu, ya jikin Rafi’ah?” Mummy ta ce “Da sauki itama” Mami ta kara kallanta ta ce “Bari mu wuce gida ga dare yayi, gobe na dawo” Mummy ta ce “To Allah ya kara sauki, a mata sannu” Mami ta fice a dakin bayan tayiwa su Ammi sallama. Karfe 11 na dare Abba ya shigo dakin da Daddynsu Khairiyya sai Abi dan tin dazu da sukazo aka hana kowa shiga wajenta sai data tashi, sun tausaya mata matuka ba kadan ba, Daddyn Khairiyya ya dinga mata addu’a da nasiha iri iri, haka Abi ma yayi ta mata kafin sukai musu sallama, Ammi ta kalli Mummy dake zaune ta ce “Hajiya zamu tafi, Allah ya kara mata lafiya” Mummy ta ce “Mungode Allah ya tsare” Khairiyya dai sai kallan Rafi’ah dake kwance take har suka fita a dakin, ba jimawa Abba ya dawo dakin, ya kalli su Anty Amina dake zaune ya ce “Bari na maidaku gida” kamar jira take ta mike tana kallan Mummy ta ce “Allah ya sauwake” Mummy ta ce “Yauwa Amina mun gode” Abba ya kalli Abdul dake zaune ya ce “Kaifa?” Ya girgiza kai ya ce “Zan zauna anan Abba” Abba ya ce “To shikkenan, bari in kaisu, Umminsu ma gida zata kwana sun sallameta” Mummy ta ce “Ehh yafi kam taje ta huta, Allah ya tsare hanya” Abba ya ansa da Amin kafin ya fita a dakin. Ta6e baki Anty Rahama tayi ta ce “Kawai kinsamu zaman asibiti kamar dole, wallahi da niyyata sanda Umma da Ikleemah zasu tafi muma mu wuce” Anty Amina ta ce “Haba Anty, idan ban zauna ba ai zasuce murna nake, bakiga yadda na dinga kakalo kukan karya ba?” Har Anty Rahama zatai magana sai tayi shiru saboda Abba data hango yana tahowa da Ummi, Anty Amina na kallansu ta dauke kai, bayan sun karaso ya bude lock din motar Ummi ta shiga gaba su kuma suka shiga baya yaja motar suka bar clinic din.
Daren ranar kwana Ummi tayi tana salla tana kai kukanta ga Allah, tayi kuka ba kadan ba a daren nan, kafin safiya ita kanta tasan ta rame tsabar damuwa, tana idar da sallan asuba ta shiga kitchen tayi dan~wake da kunu sannan tasa a basket, sama ta koma dakinta tayi wanka ta shirya, tana gamawa Abba ya dawo daga masallaci, bayan sun gaisa ya kalli agogon dakin ya ce “Karfe 7 saura yanzu, kinyi breakfast ne?” Ta girgiza masa kai ta ce “Idan naje caan zanci” Abba ya ce “No, kafin na shirya kiyi breakfast”daga haka ya juya ya koma dakinsa, half cup na kunu kawai ta iya sha, shima turawa tayi ta shanye bawai son ranta ba, bayan ta gama ta ajiye cup din ta shiga dakin Saudatu mai aikinta, tana zaune akan sallaya tayi shiru itama, duk da ba wani zama tayi da Rafi’ah ba, jiya data ganta sai da tayi kuka, haka kawai takeji tana san yarinyar, jin an rufe kofar tayi saurin jaa baya tana kallan Ummi ta ce “Ina kwana Ummi” Ummi ta ce “Lafiya kalau, jiya mun dawo kinyi bacci” ta ce “Ehh nayi bacci, ya Anty Rafi’ah da jiki?” Ummi ta ce “Da sauki, yanzu zamu koma, da rana ki dafa komai ma kici, ba sai an kai asibiti ba” Saudatu ta ce “Toh, Allah ya kara mata lafiya” daga haka Ummi ta mike ta ce “Ameen” tana fita a dakin Abba na sakkowa, ta dauka basket din suka fita zuwa parking lot, Mustapha ya musu ya mai jiki sannan ya bude gate suka fita, sosai Abba ya dinga kwantarwa Ummi hankali a mota, ba irin misalan da bai mata ba dan hankalinta ya kara kwanciya, kuma Alhamdulilah ta rage fargaban da takeji sosai. Bayan sunyi parking ta dauko basket din suka shiga ciki, Abba ne ya bude kofar dakin ya shiga Ummi ta bishi a baya, kan gadon duk suka nufa, tana nan zaune da hijab a jikinta, da alamu salla ta gama idarwa, Ummi dake kallanta ta ce “How are u daughter” ta dan goge hawayen idanta ta ce “Alhamdulilah Ummi” daga haka ta kalli Abba da shima kallanta yake ta ce “Ina kwana Abba” ya ce “Lafiya kalau Mamana, ya jikin ki?” Ta ce “Da sauki Abba” nan suka gaisa da Mummy ma, Abdul ya gaishe dasu shima, Rafi’ah dai na zaune akan sallaya ta lula duniyar tinani, idan ta tuna abinda Mummy ta fada mata sai ziciyarta ta buga, wai itane dauke da cikin Yusuf, jin Ummi na ta6a ta yasa tayi saurin zabura, lokaci daya hawaye ya shiga zirya a idanta, Ummi ta sauke ajiyar ziciya ta ce “Ko so kike na koma gida?” Ta girgiza kai a hankali tana share hawayen idanta, she can’t believe that she’s pregnant, ta kara rufe idanta da hijab dinta ta fara kuka tina ko shekara 18 bata cika ba, saura two months ta cika shekara 18, bayan Abba ya fita tare da Abdul Mummy ta ce “Aiba a kanki aka fara saki da ciki ba, kinganta harta yi shiru tindana gaya mata tana da ciki ta daga hankalinta” Ummi ta shafa kanta cikin rarrashi ta ce “Stop crying daughter, duk abinda kika gani jarabawace daga Allah, watarana sai labari, ki daina damun kanki ko dan cikin dake jikinki ma” rungume Ummi tayi ta ce “Ina kokarin yin hakan Amma Ummi bana iyawa” Ummi ta ce “Zaki iya Rafi’ah, just forget about Yusuf, ki manta da kin ta6a rayuwa dashi” kwanciya tayi liif a jikin Ummi tana sauke ajiyar zuciya. Karfe 8 Ammi ta karaso asibitin da warmers din abinci, sosai taji dadi ganin Rafi’ah nacin dan wakenta sosai, kunu ne dai bata wani sha ba, da azahar Mami ma sukazo ita da Sadeeq, minti 10 sukai suka koma gida, wajajejn karfe 2 su Umma dasu Anty Rahama suka iso, carton din maltina Umma tasa aka siyo aka ajiye musu. Kwanan Rafi’ah 3 a asibitin aka sallameta bayan an bata magunguna sabi, by now ta dan sake saboda kullum Ameera na zuwa asibiti ita da mamanta, anan take kara kwantar mata da hankali, Mami ma kullum sai tazo ta kawo abinci, haka Ammima itakam safe rana dare sai ta kawo abinci duk da hanata da Ummi take amma bata fasawa, kafin a sallameta ‘yan uwa da abokan arziki su kaita zuwa dubata, Yusuf ya sha tsinuwa a gun Gwaggo ba kadan ba, motsi kadan saita tsine masa. Washegarin randa aka sallameta tana zaune a daki ita da Ameera, gaba daya ta damu dan Ameera sallama ke mata zata tafi zaria makaranta ta samu admission, Rafi’ah ta fashe da kuka ta ce “Zanyi missing dinki Ameera, Allah bazanji dadi ba” Ameera ta share mata idanta ta ce “Duk bayan sati biyu zan ringa zuwa, nidai kawai ki daina damuwa ki kula da kanki sosai” Rafi’ah ta kamo hannayenta ta ce “Insha Allah friend, Allah ya bada sa’a yasa ki fara a sa’a” Ameera ta ce “Ameen Fatima” duk jikinta sanyi yayi ganin yadda Rafi’ah ke share hawaye, jin hawaye na zuwa mata tayi saurin daga mata hannu ta fita a dakin, a corridor ta goge idanta sannan ta sakko downstairs, tayi wa Mummy da Ummi sallama, Ummi ta mata fatan alkhairi sannan ta bata leda me dauke da tirare da sleeping dress, da kyar ta kar6a sannan ta kara musu sallama ta tafi, Ummi ta kalli Mummy dake zaune ta ce “Anty bazaki koma gida ba, ai jikinta yayi sauki?” Mummy ta ce “Anjima zan tafi Zainab, Jawad ma yau zai dawo” Ummi ta ce “Allah ya dawo dashi lafiya”, tashi Ummi tayi ta ce “Bana leka Rafi’ah ko zata ci abinci” Mummy ta ce “Ohk to” daga haka Ummi ta dauki warmer da plate ta haura sama.

_ALHAMDULILAH, anan na kawo karshen littafin *SHARIK HAYATI* part one, ina rokon Allah ya yafemin kuskuren danayi ya kuma bani ikon rubuta abinda shine dai dai_ 馃檹馃徎

_Special thanks to the members of my Groups, wallah u people are the best, ina sanku sosai da sosai 馃挒馃挒_ _And again my Kk 馃グ i luv u so much sweetheart, u are always supporting me right from the beginning, billahil azeem ina sanki Dije ta, my Jiddah soyayyarki is endless_ 馃槏, _AISHA SHEHU can’t forget with u sister, Fatima is thanking u again and again Allah ya raya Na’eem ya bashi ilimi me inganci_ 馃槆, _Then my FANS 馃槆 Billah ina sanku a duk inda kuke sisters, only God knows how much i luv u people, ina muku fatan alkhairi duniya fil akhirah 馃槝_ .

Back to top button

You Want Latest Updates?

X