CIKAKKEN TARIHIN RAYUWAR JARUMA UMMI RAHAB DA KUMA ABUNDA YA HADA TA DA ADAM A ZANGO.
Zamu gabatar muku da cikakken TARIHIN RAYUWAR JARUMA UMMI RAHAB da abunda ya hadata da adam a zango har suka samu sabani.
Jama’a da dama suna ta yada jita-jita akan asalin jaruma ummi rahab,wasu suce yar dangi ce wasu kuma suce a’a,yar adam a zango ce,acikin wannan videon zakusan cikakken al’amari.
Wacece ummi rahab kuma a ina aka haifeta?.
Anhaifi ummi rahab 17 gawatan afrilu a shekarar 2003 a jihar kaduna dake arewacin najeriya.Ummi rahab tayi makarantar firamare da sakandire duk anan kaduna.
Sakamakon shakuwa da kuma kauna dake tsakanin Adam a zango dakuma ummi rahab,yasa har yanzu wasu basu yarda cewa ummi rahab ba diyar adam a zango bace tun bayan fitowarta acikin shirin Ummina lokacin tana karamar yarinya.
Fim din ummi na daya daga cikin finafinan da jarumar tafara fitowa,tun daga lokacin kuma ba’asake jin duriyarta ba sai a wadannan shekarun.
Bayan jaruma ummi rahab ta girma sai adam a zango ya kara dakkota yasakata acikin sabon shirin sa mai sjna Farin wata sha kallo,wanda yasanya tasake daukaka a kannywood.
yanzu haka dai adam a zango da ummi rahab sun shata layi bayan da jarumin ya zargi cewa yana niyyar bawa jarumar tarbiyya amma taki dauka,inda ita kuma tace idan har yaci gaba da bata mata suna to zata tona masa asiri.
jarumar da jarumin har yanzu basa shiri tun daga lokacin da wannan matsalar ta faru,saboda haka nema ba wanda yake kula da al’amarin wani a tsakaninsu
Ga dai cikakken bidiyon nan akasa sai ku kalla domin jin cikakken tarihin a kasa.
Ga cikakken bidiyon nan akasa ku kalla.
Wannan shine cikakken tarihin rayuwar ummi rahab.
Ga duk wanda yakeson irin wadannan videos zai iya zuwa youtube channel dinmu mai suna HAUSA FLEX TV Domin ya kalla. Mungode.